Prof. Isa Ali Pantami National Supporters Forum

Prof. Isa Ali Pantami National Supporters Forum Wanan Shafi Na Masoya Isa Ali Pantami Ne.

GOMBE TA MALAM CE: BI'IZINILLAHI TA'ALLAH
22/10/2026

GOMBE TA MALAM CE: BI'IZINILLAHI TA'ALLAH

ƘUNGIYAR PROF. ISA ALI PANTAMI MEDIA & DIGITAL MOVEMENT TA GUDANAR DA ZAMA DA OFFICE ƊIN FIRST LADY...A yau, 2 ga Oktoba...
02/10/2026

ƘUNGIYAR PROF. ISA ALI PANTAMI MEDIA & DIGITAL MOVEMENT TA GUDANAR DA ZAMA DA OFFICE ƊIN FIRST LADY...

A yau, 2 ga Oktoba, 2026, Ƙungiyar Prof. Isa Ali Pantami Media & Digital Movement ta gudanar da zama na musamman da Office ɗin First Lady, Hajiya Khadija Isa Ali Pantami, ƙarƙashin jagorancin Hajiya Mommy Nana Dayyab, tare da mataimakiyarta Hajiya Safara’u Zeenariyar Pantami, da kuma Mai Girma DG Zubairu Abubakar.

Zaman ya kasance wata muhimmiyar dama ta ƙarfafa zumunci, fahimtar juna da karfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyar da Office ɗin First Lady, inda office din ya mayar da hankali kan girmama gudunmawar da ƙungiyar ke bayarwa, tare da yaba wa ƙoƙarin membobinta da jajircewarsu wajen isar da manufofi da ayyukan tafiyar Pantamiyya.

Haka kuma, an gudanar da musayar bayanai da shawarwari domin ƙara inganta alaƙa da fahimtar juna tsakanin ƙungiyar da Office ɗin First Lady, tare da samar da ingantaccen tsarin haɗin gwiwa da zai amfani tafiyar baki ɗaya.

A nata ɓangaren, ƙungiyar ta tabbatar da aniyarta ta ci gaba da aiki tare da Office ɗin First Lady cikin mutunci, haɗin kai da sadaukarwa, tare da ƙara ninka ƙoƙari wajen tallata ayyuka, manufofi da kyawawan manufofin tafiyar Prof. Isa Ali Pantami, da kuma first lady da mukarabbanta bisa tsarin da aka amince da shi.

Daga cikin waɗanda s**a halarci wannan zama akwai Hajiya Asmau Gambo, wadda take daga cikin jiga-jigan ƙungiyar, tare da Amina Haruna, Aishatu Isah, Sharif Auwal Alhusainy, Abubakar Yakubu Yashi, Ado Ahmad, da sauran membobin ƙungiyar.

Wannan zama ya ƙara tabbatarwa da kungiyar mutunci, girmamawa da karrama al'umma da Office din Fist lady yake da, wanan office ya mutunta mu ya karramamu, kuma yayi Mana adduoin alkairi tsarkaka, wanan kungiya ta dauki alkawarin cimma manufofin da aka sanya a gaba. Ƙungiya ɗaya, manufa ɗaya, aiki ɗaya domin sadaukarwa da kishin al’umma.

Professor Isa Ali Pantami
Abba Sani Pantami
Ahmad Abdussamad
Prof. Isa Ali Pantami National Supporters Forum
Rubutawa: Abdussamad Tijani Sani....✍️

A GOBE TALATA ZA'A GUDANAR DA FRESH PRIMARY NA PDP...Kungiyar Prof. Isa Ali Prof. Isa Ali Pantami Media & Digital Moveme...
28/09/2026

A GOBE TALATA ZA'A GUDANAR DA FRESH PRIMARY NA PDP...

Kungiyar Prof. Isa Ali Prof. Isa Ali Pantami Media & Digital Movement, na tunatar da mambobin jam’iyyar PDP da sauran masu ruwa da tsaki na Jihar Gombe cewa, Gobe Talata, 29 ga Satumba, 2026, ita ce ranar da aka tsara gudanar da sabon zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP na takarar Gwamnan Jihar Gombe.

Wannan rana muhimmiyar rana ce ga jam’iyyar, domin ita ce damar da tsarin dimokuraɗiyya zai ba wa wakilan da s**a cancanta damar bayyana ra’ayinsu ta hanyar kada kuri’a. Saboda haka, muna kira ga dukkan mambobin PDP da za su halarci wajen wannan muhimmin zabe da wuri, su kasance cikin nutsuwa, ladabi, mutunta juna da bin dokokin jam’iyya da na zabe.

A fita da wuri, a bi umarnin jami’an da aka dora wa alhakin gudanar da aikin, a guji duk wani abu da zai iya haifar da hayaniya ko rikici, sannan a tabbatar an gudanar da komai cikin kwanciyar hankali da mutunci.

Duk wanda zai kadawa malam kuri'a ya kada masa da "Bismillah" bayan ya kada kuri’arsa, ya mika lamarin ga Allah cikin tawakkali da addu’a yana mai fadin: “HASBUNALLAHU WA NI’IMAL WAKEEL.”

Allah Ya sanya alheri, Ya ba Jihar Gombe zaman lafiya, Ya kare dukkan mahalarta wanan zabe, kuma Ya sa a gudanar da wannan zabe cikin adalci, gaskiya da lumana.

Hakika Gombe na bukatar malam, PDP na bukatar hadin kai, Dimokuraɗiyya na bukatar mutunta tsarin zabe, al'ummar Gombe na bukatar adalci. Wanan sako ne daga Uwar Kungiyar Prof. Isa Ali Pantami Media & Digital Movement, Hajiya Aisha Nana Dayyab, Da Mataimakiyar Uwar Kungiyar Hajiya Safara’u Professor Isa Ali Pantami, Da kuma Jigon kungiyar Hajiya Asmau Gambo, tare da sahalewar dukkan membobin kungiyar, da kuma sa hannun jagororin kungiyar. Rubutawa: Abdussamad Tijani Sani ✍️

Address

Gombe

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Prof. Isa Ali Pantami National Supporters Forum posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share