09/25/2025
KAZAMIN NAMIJI 10 Episod
Kundin Masoya
Littafi na (Ɗaya)
Rubutawar Adamsy Adam ©️
★★★
To. Haka na cigaba da zuwa school , Abokina Idris da muka hadu tun Ranar da na Fara zuwa shine Abokina Kuma ajinmu Daya wajan Zaman mu Daya.
Kullum tare ake Ganin mu, haka kuma idan Aka tashi zuwa Daukar mu kusan tare ake Tafiya damu,
idris wani Abokinsa Mai Suna Tahir ke zuwa da Adaidaita sahu Yana Tafiya dashi idan an Tashi a School, Ni kuma Yaya Areef ke zuwa Dauka ta A makarantar har kowa ya fahimci irin son da Yaya Areef Yake min. Domin idan Yazo Dauka ta baya taɓa zuwa latti. Wani Lokacin ma Sai dai na fito na Tarar
da Yana jirana a Harabar school,
Rayuwa ta Kam ta Chanja. Ala Dole na koyi Tsafta saboda yadda nake Ganin Yara da manya suna zuwa school tas K**ar ka Lashe su. Amma fa na Sha Duka a wajan assembly kafin na Yiwa kaina fada na rage Kazanta.
Musamman Idris ya zaunar Dani ya nunamin illar barin Yunifom da datti.
Domin idan aka K**a Ni Yunifom Dina Yayi datti a assembly Duka zanci. Ko Kuma su korani Gida.
Dole kanwar naki na koyi Tsafta.🤣
A Haka har muka Zana exam inda nazo na 7 Aka sauya Mana aji zuwa aji uku.
Saidai wannan karon ba Wajan zaman mu Daya da Idris ba Amma ajinmu Guda,. Babu Laifi na kasance mutum Mai hazaka da kokarin haddace Daraussa,
★★★
Yaya major kuwa na jima da bude wani shafi a cikin Littafin Rayuwa ta na Ajiye shi na rufe Gam tare da jefar Dashi ,
Babu shakka Yaya major yana Cigaba da bani Mamaki a duk kwanan Duniya,.
Mummunan Dabi'ar sa ta Kwashe kwashen karuwan maza na Cigaba da Faruwa Akan idona, kuma Ban taɓa Yin Gangancin fada ma Yaya Areef irin Rayuwar da nake Gani akan idanuna Yaya major Yana yi ba. Dukda cewa na Sani Sarai Yaya Areef ya San irin Rayuwar da Abokinsa yake. Ni dai Mubeen Haka na cigaba a da saka Ido.
Yaya major baya Shiga harkata b***e wata magana ta fatar Baki ta hada ni da shi, a fahimatar da nayi Masa shine Dan na Daina Kazanta ne Ina kokarin Zama ɗan Gayu Kuma Ɗan makaranta. Musamman da Yaji Labarin cewa ni Mutum ne Mai hazaka, Yaya Areef ya Sha fada min cewa. Yaya major Yana Matukar Sona da Tausayi na. Amma Abun da Baya so shine kazantar da
nake. Wai Yaya major yace idan har na Daina kazanta to Babu ruwansa Dani bazai Dinga Takura min ba. nakan ce ba Gaskiya bane. Babu Wata kazanta da nake da zai Zama Dalilin da yasa zai Nuna min kiyayya Haka, Dan haka Ko da Gaske ne ko ba da Gaske bane nima na
tsane shi fiye da Yadda ya tsane ni, ni a cikin Zuciya ta sunansa bazai chanja ba , na dauke shi a Matsayin Mutum mugu Marar Tausayi. Marar yafiya Wanda duk Abun da aka masa Sai ya Rama. Marar Karɓar duk kaddarar da ta same shi, bugu da Kari na Dauke shi a Matsayin tambaɗaɗɗe Marar class..
★★★
Yau itace Ranar da Bazan taɓa mantawa ba a Tarihin Rayuwa ta, Itace Rana ta Farko da Al'amarin Rayuwa ta ya Fara Faruwa,. Bayan An tashi daga School tare muka jero da Idris. Labarin Rayuwar sa Yake bani. Inda yace shi Mutumin fataskum ne kuma maraya. Iyayensa sun Jima da Rasuwa. Kanin mahaifinsa ne kadai ya rage Wanda
Kuma Yake neman Raywarsa. Yace min
iyayensa kafin su Rasu sun Tara Masa Dukiya Mai Yawan Gaske. Da kanin mahaifinsa ya fahimci Haka sai ya
Fara farautar Rayuwar sa. Nan ya gudo da duk wasu takardun da suke da
Amfani Ya taho Garin Abuja. Yace min ya Hadu da Haladu Wanda suke tare
a Gidan Haya yanzu Haka. Suna Matukar son juna. Abotar su Mai Matukar Amfani ce,. Dalilin Haka Ya Shiga makaranta Kai tsaye domin Nan Gaba ya samu makami mai karfi
wajan kwato Sauran hakkinsa Dake hannun kanin mahaifinsa.
Hakika na Tausaya ma Labarin Idris.
Inda na Masa kallon Namiji mai kananan shakaru Kuma jajritacce,
Na Tausaya Masa. Babu uwa Babu uba Sai mutum Guda ya rage a danginsa, Mai makon ya tallabe shi ya bashi farin ciki Amma shi ke neman Ransa, Muna Tafiya Yana bani Labari Sai na hango
motar Yaya Areef.
Da murmushi nace. "Ga Yaya Areef can ya Zo daukar mu,
Yana murmushi yace. Mubeen Zan so naji Labarin ka, Na Dade da fahimtar Yayanka Yana Matukar sonka.
Nayi murmushi nace. "Idris kenan. Ai Yaya Areef shine Rayuwa ta, shine Mutumin da ya maye Gurbin Uwa da
ubana. Shine Mutumin da ya Zama babban Yaya. Kani. Kaka. Dan uwa. Da Kuma uwa da uba a gare ni, Baffa baba ya Zama jigon Rayuwa ta
Idris yace. "Waye Kuma Baffa baba.?
Murmushi nayi nace Zan baka Labari Nan ba da jimawa ba,
Da murmushi Akan fuskokinmu muka Karasa Gaban motar Yaya Areef. Ya fito da murmushi Akan fuskarsa.
Idris Yayi saurin risinawa da cewa. "Ina wuni Yaya,
Yana murmushi ya Amsa da Lafiya kalau. Sannan Ya zare gilashin Idanunsa ya kalle ni yace. Student ya Akaji da Karatu.?
Da Sauri na fada jikinsa nace. "Yaya Akwai Wahala.
Dariya su Duka s**ayi min har da Idris. Yace, "To ai Kaima wataran zaka koyar da Wasu.
Yaya Areef ya maida hankalinsa Kan Idris Yace, "To kaji Abokin ka ya fada maka Gaskiya,
Da Sauri Yaya Areef ya Bude min murfin motar na Shiga. Na kalli Idris Dake tsaye nace. "Ka shigo mu kaika Gida Mana.
Yaya Areef ma yace. "Shigo mu sauke ka Mana.
Idris yace. "A'a nagode, yanzu Nima Abokina zai Zo ya Dauke ni,
Yaya Areef yace "Ai baka San zai Zo da Wuri ba. Gara dai mu sauke ka ko,
Idris yace "No kuje Kawai. Idan na biku ya dawo Bai same ni ba ai bazai ji Dadi ba.
Cike da son zolayarsa nayi Murmushi nace. "To Abokin Tahir mu Kwana Lafiya. Sai mun hadu gobe,
Ya daga min hannu Yana Dariya tare da cewa "sai goben.
Daga Haka Muka fice daga School
din,
A Lokacin da muka Shiga Harabar gidanmu a Lokacin jikina ya bani Akwai wani Abu Dake Faruwa a cikin Gidan,. Saboda yadda naji Gidan Yayi Shiru Babu hayaniya ko motsin Mutane. Bance da Yaya Areef komai Akan Haka ba har muka Shiga cikin Babban Falo na Farko. Yaya major na Gani tsaye da jaka Guda Biyu ya Rike Yana fadin ai ba Sai ka dauki komai ba Waɗannan sun Isa har mu Dawo. Ina kallo Yaya Areef ya saka kyalle ya share Hawayen dake kokarin zubo Masa. Nan fa jikina ya bani Akwai Matsala. Zuciya ta ta Shiga wasiwasi.
Yaya Areef ya Kamo Hannuna muka fice daga falon. Duk motocin Gidan Babu sai Guda Daya wacce muka Shiga yanzu muka Tafi.
Yaya major ke tuka mu. muna hawa Kan t**i na samu Karfin Zuciyar Tambayar Yaya Areef
"Ina zamu je,?.
Bai kula ni ba Sai Hawayen Dake bin
Kumatunsa Yana kokarin maidasu suna Nuna Masa Bai Isa ba, Na kalli Yaya major dake tuki Sai Naga ya dauki
kyalle shima Yana share kwalla,
Me zanyi idan ba kuka ba. Nan da Nan nima na saki Nawa kukan wiwi. Idan nasu kukan a Zuciya suke yi Ni Bari na fito Da Nawa fili. Dukda cewa ban San me suke ma kukan ba, Nima Sai na bi yarima Asha kiɗa na Shiga Taya su Rerawa...
🖐🏻
Thanks 🙏🏻
KU DAKACE MU 🙅🏻❤️