18/05/2026
TIRKASHI: Barrister Hamza Nuhu Dantani ya fadi Abubuwa Guda 19 daza su Hana ya Zabi Tubunu Kuma yayi kira da kada Jama'a su sake Zaɓar sa karanta su Kamar haka.👇
Idan zaka ki mutum ka kishi bisa Dalili Inji Barrister Hamza Nuhu Dantani.
Tubunu abin da ya saka nake son naga an Sallemeshi shine k**ar Haka!
1- Baya bin Tafarkin Demokradiya
2- A 2024, ya saka An k**a Yara kanana tun daga States nasu zuwa Abuja don sunyi zanga zanga , sai da suke azabtu sannan aka sake su, wasu kuma an kashe su a lokacin zanga zanga.
3- Ya Kawo Dokokin Haraji. Ana zabtarewa mutane kudadensu a Asusun Bankunansu. Na tabbata idan kana anfani da banki, kullum sai kaga debit alert.
4- Ya kara kudin Haraji ma Kanfanannuwa Inda Abubuwan more rayuwa kudadensu sukayi mugun Tashi. Wanda daga karshe wahala akan talaka ne zai kare.
5- An Kara kudin Kiran waya dana Data saboda Karin kudaden da Gomnati mai ci tayi musu a bangaren karin kudin haraji da suke biya.
6- Ya zabtare Tallafin Mai Petr , wanda ya saka kudin mai ya karu tun hawansa mulki.
7- Ya Bata Mulkin Demokradiya inda yake so mayar da Kasar Tsarin Jam'iya Daya. Inda ya sakawa gomnonin jahohi tsoro, wajen rashin basu damar walwala idan kai gomna ne a jam'iyar adawa. Ko kuma yayi maka barazabar tubeka a gomna.
8- Ya Cire Zabbaben Gomnan Ribas , batare bin tafarkin doka ba, kuma ya Daura Gomnan wacin gadi, kafin daga baya ya Dawo dashi.
9- Yayi Anfani da ikonsa wajen kara wa'adin Manya manya Jami'an tsaro wanda Lokacin yayi na ritaya. ( Police, Custom and Immigration )
10- Ya Mayer da Yan Majilisu Aljihunsa , sai abunda yake so za'a Aiwatar a majalisan Tarayya.
11- Kayan Abinci ya Hau, kayan Gini Sun Hau, wanda ya saka Gidaje da filaye sukayi tsada inda gidan Haya yafi karfin Talaka.
12- Ya kasa kawo karshen Tsaro k**ar yadda yayi Alkawari lokacin da yake campaign
13-Karatu ya zama bana talaka ba. Saboda kudin makaranta yayi tsada sosai
14- Yayi Anfani da Da Ikonsa wajen Kamawa da Rufe Yan Adawa.
15-ya ciyo bashin da Nigeria bata taba ciyowa ba.
16- Mutum ne wanda baya son Ayi Adawa dashi a siyasance.
17- kudin Wutan lantariki yayi tsada, Kuma har yanzu ba'a magance matsalar wutan lantari ki ba.
18- Babu wani abu na cigaba da Gomnatinsa ta kawo a Arewa.
19- Idan har ya zarce, Kamar Zaiyyi sanadiyar Birne Demokradiyya a Nigeria. Saboda Duk wanda yayi Adawa dashi a lokacin, zaka kare a Gidan prison.
Saboda Haka, Ku zabi duk wanda kukeso a APC, Anma Tubunu waje road.
~Meza Kuce.?