24/09/2023
Kwana ɗari (100) masu albarka...
Bayan cikakkiyar godiya mara misaltuwa ga Ubangiji, Mahalicci, wanda ya ajiye aya ga masu hankula a cikin abinda ya zartar.
Godiya ta musamman ga Jagoranmu kuma shugaba abin koyi cikin riƙe aminci, alƙawari da rama alheri ga wanda yayi masa; lallai ya cika mai dattaku, ya mantar damu raɗaɗin rashin mahaifin da ya ƙare rayuwarsa cikin ɗaukaka na ƙasa da yayata ayyukan alkhairi ga masoyansa da akasinsu; har yakan cemin:
"Ustazu na (haka yake kirana) na taimaki mutane, ko na mutu baza ku tozarta ba"
Ina farinciki da nuna gamsuwa ga aminansa, na gida da na waje; gwamnanmu, sanatoci da ƴan majalisu mabanbanta (a jiha da tarayya), shugabannin jam'iyya na ƙasa har zuwa kan mazaba, ƴan kasuwa da ma'aikata, masarauta da masu mulki; da... da... abin da yawa; bisa irin riƙon da suke yi mana da nuna hanyar da sun san idan mun bita zata haifar da mafita.
Godiya ga dandazon masoyanmu (a Wudil da Garko), har da wasu Jihohin; waɗanda kullum suke nuna soyayya, goyon baya, gamsuwa da yaƙini da suke dashi akanmu; a kullum muna samun saƙonni na fatan alkhairi da nuna irin farincikinsu bisa abubuwan da gudanarwa na alkhairi da ƙoƙarin sauke nauyi.
Al'ummar Garko da Wudil,
Abinda muka gabatar a cikin kwanakin nan, somin taɓi ne na irin abinda zuciyarmu ta taskance na cigaba da muke fatan samarwa yankinmu a cikin ɓangarori mabanbanta musamman na ilimi, lafiya, samar da wadata ta ruwan sha da kuma aikin yi/sana'a.
Lokaci kaɗan zamu gabatar da wasu daga cikin ayyukan da suke gabanmu; mafi kusa shine shiri na Empowerment mai ƙayatarwa wanda zamu ƙaddamar da kwamitin da zasuyi aiki wurin tantancewa da kuma tsarin da za a bi wurin gabatarwa; zai shafi bayar da jari ga masu ƙananan sana'o'i da kuma koyar da sana'ar ga waɗanda basu da ita (tare da samar musu da kayan sana'ar), insha Allah.
Sauran bayani zai zo daga baya...
A kullum, bamu da ƙarfi, dabara ko wayo sai daga Allah, bamu iya ba sai da iyawarSa, Ka iya mana, Ka fitar damu haƙƙin mutanen da suk