27/11/2016
IYAYEN ANNABI MUHAMMADU
(SAW) 'YAN ALJANNA NE
Wasu mutane sun dauki kayan
talla domin sayarwa a madadin
IBLIS (L.A.) . Kayan da Shaydan
din kuwa ya dora masu a kansu
domin su sayar masa shi ne CIN
MUTUNCIN MANZON ALLAH (SAW)
, wato halittar nan mai albarka ,
wadda Shaydan ya fi kin ta a cikin
halittun Allah (SWT) .
Kowane mai talla da abinda yake
fada a lokacin talla domin ya jawo
hankalin mutane zuwa ga kayan
da yake
so a saya . Su masu wannan talla ,
a madadin Shaydan ,abinda suke
cewa shi ne " IYAYEN ANNABI
'YAN WUTA NE . " Allah (SWT) Ya
tsare mu . Innaa lil-Laahi , wa
innaa ilayHi raaji'uun !
SAKAMAKON DA WANNAN TALLA
ZAI HAIFAR
Duk wanda ya yarda da cewa
iyayen Manzon Allah (SAW) 'yan
wuta ne , wato kafirai ne , to zai
samu kansa cikin :
i . karyata Allah (SWT) ;
ii. karyata Manzon Allah (SAW) ;
iii. cutar da Allah (SWT) , da kuma
ManzonSa (SAW) .
SAKAMAKON DA MASU TALLA DA
SAYEN WANNAN KAYA ZASU
SAMU
Mafi kankantar sakamakon da
masu cewa iyayen Manzon Allah
(SAW) , Abdul-Laahi da Aaminatu
(A.S.),
'yan wuta ne , da wadanda s**a
yarda da haka , zasu samu shi ne
zama a katafaren gidan Shaydan ,
wato WUTA . Allah (SWT) Ya tsare
mu .
Zasu samu wannan sakamako ne
sanadiyyar karyata Allah (SWT) ,
karyata Manzon Allah (SAW) , da
kuma cutar da Allah (SWT) , da
ManzonSa (SAW) . In sha'Allah ,
zamu ji yadda fadin haka yake
karyata Allah (SWT) da ManzonSa
(SAW) , da kuma cutar da su .
DALILAN DAKE NUNA CEWA
IYAYEN MANZON ALLAH (SAW) BA
'YAN WUTA BA NE
Akwai dalilai masu nuna cewa
iyayen Manzon Allah (SAW) ba
'yan wuta ba ne . Dalilan kuwa su
ne :
i. dalilai daga Al-Qur'ani ,
ii. dalilai daga Hadisi , da kuma
iii. dalilai na hankali .
Abin mamaki ne a ce musulmi-
mai-hankali ya yarda , kuma har
ya rika fadin cewa iyayen
Shugaban manzanni (A.S.) , kuma
halittar da Allah(SWT) Ya fi so a
cikin dukkan halittarSa , "'yan wuta
ne ." A'uudhu bil-Laah ! A dalilin
wannan gawurtaccen rashin
hankali da masu fadi , da kuma
yarda da wannan mummunar
magana , ke nunawa zan fara
amfani da dalilai na hankali domin
kifar da wannan kaya na talla da
Shaydan (L.A.) ya dora wa masu
tallan kayansa domin su sayar
masa .
DALILAI NA HANKALI MASU NUNA
CEWA IYAYEN MANZON ALLAH
(SAW) BA 'YAN WUTA BA NE
Akwai dalilai , masu yawa ,na
hankali masu nuna cewa iyayen
Manzon Allah (SAW) , Abdul-Laahi
(AS) , da Aaminatu (AS) , ba 'yan
wuta ba ne . Daga ciki akwai :
i. sunayensu (AS) : sunan
mahaifin Manzon Allah (SAW)
Abdul-Laahi , wato BAWAN ALLAH Sunan mahaifiyarsa Aaminatu ,
wato WADDA TA YI IMANI .Idan
mutum yana da lafiyayyen hankali
, zai gane cewa
lallai Allah (SWT) Ya kimsawa
iyayensu ne su sa masu wannan
suna saboda ya san zasu kasance
mutane ne muminai wadanda zasu
haifi shugaban manzanni (SAW) .
A wancan lokaci , babu mutane
masu suna Abdul-Laahi , da
Aaminatu , a cikin mushirikai .
ii. iyayen dukkan Annabawa (AS)
muminai ne : dukkan Annabawa ,
har da Annabi Ibraahiim (AS) ,
iyayensu ba kafirai ba ne . Saboda
haka , mai lafiyayyen hankali zai
fahimci cewa iyayen Manzon da ya
fi dukkan Manzanni komai , a
wurin Allah (SWT) , baza su zama
a ce su kadai ne kafirai ba , 'yan
wuta . A'uudhu bil- Laah !
Misali : Babu yadda za a yi a ce
kwamishinoni nada motar ofis ,
amma gwamna baida ita .
iii. duk iyayen Annabawa(AS) 'yan
Aljanna ne : mai hankali zai
fahimci cewa babu yadda za a yi a
ce kowane manzo zai zauna tare
da iyayensa a Aljanna , amma
Shugabansu nasa iyayen na wuta .
iv. duk wanda ya shiga Aljanna ,
ya shiga ne saboda sakamakon
bin sakon da Manzon Allah(SAW)
ya kawo :
mai hankali zai fahimci cewa babu
yadda za a yi a ce duk alherin nan
da Manzon Allah (SAW) ya zo da
shi , amma kuma a ce iyayensa
(AS) ba zasu amfana ba , saidai su
zauna a wuta tare da Shaydan ,
Abuu Jahlin , Abuu Lahbin ,
Fir'aun , da sauran kafirai .
Misali : Attajiri , kuma mutumin
kirki , mai ba talakawa abinci , an
ya zai hana iyayensa abinci , har
su mutu saboda yunwa ?
v. Makkah da Madinah sun fi
kowane gari ne saboda an haifi
Manzon Allah (SAW) ne a Makkah ,
kuma ya tafi gidan rahama a
Madinah : mai hankali zai fahimci
cewa yadda garin da aka haifi
Manzon Allah (AS) ya fi kowane
gari , haka tsatso , da kuma cikin
da Manzon(SAW) ya zauna ya fi
kowane tsatso da ciki.Saboda
haka , mai tsatson , da kuma
mahaifar da
Manzon Allah (SAW) ya zauna ,
wato Abdul-Laahi (AS) , da
Aaminatu (AS) , sun fi iyayen kowa
, dalilin haka su ba 'yan wuta ba
ne .
vi. mushirikai kazanta ne : Saboda
haka , babu yadda za a yi a ce
Allah (SWT) Ya sanya Manzon
Allah (SAW) ,
halittar da Ya fi so , a cikin
kazanta , wato tsatso da mahaifa
ta mutane kafirai .Wannan yana
nuna wa mai
hankali cewa mai tsatso da
mahaifar da Annabi (SAW)
ya zauna , wato iyayensa (AS) , ba
kafirai ba ne , domin su ba najasa
ba ne .
Zan tsaya a nan yau . In sha'Allah
, gobe ko jibi , zan kawo wasu
daga cikin dalilai na Hadisi masu
nuna cewa iyayen Manzon Allah
(AS) ba 'yan wuta ba ne kamar
yadda Shaydan ya bayar da talla
ga wasu , kuma
suke yi.
Allah (SWT) Ya kara wa Manzon
Allah (SAW) , alayensa(AS) , da
sahabbansa(RA) , tsira da aminci .
Bis-salaam ,
Haliru Abdullahi Maraya .