10/06/2025
Dan Kwarai!
A ranar 8 ga watan Yuni, shekara ta 2025, Honourable Abubakar Isah Babale, ɗan takarar kujerar Councillor na Iku South One Ward a ƙarƙashin jam’iyyar SDP, tare da tawagarsa, sun kai ziyarar ban girma da gaisuwar Sallah zuwa fadar Mai Anguwa Sarkin Noma, Alhaji Abubakar Garba Umar.
Mai girma Alhaji Abubakar Garba Umar ya nuna matuƙar farin cikinsa da wannan ziyarar. A cikin jawabinsa, ya sanya wa Hon. Abubakar Isah Babale albarka tare da nuna cikakken goyon bayansa ga tafiyar siyasar sa. Ya kuma bayyana cewa Hon. Abubakar mutum ne mai mutunci, wanda ke da sanin kima da darajar manya. Haka kuma, mutum ne mai amana, gaskiya, da tausayin al’umma.
A ƙarshe, Sarkin Noma ya yi masa addu’a da fatan nasara a tafiyar sa ta siyasa.
Masha Allah.