Sokoto State Social Media Organization

Sokoto State Social Media Organization Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sokoto State Social Media Organization, Political organisation, Sokoto.
(1)

Alhamdulillahi. To the glory of Almighty Allah (SWA), today in Yabo Local Government Area, I had the honour of joining t...
11/05/2026

Alhamdulillahi. To the glory of Almighty Allah (SWA), today in Yabo Local Government Area, I had the honour of joining the good people of Yabo and Shagari Local Government Areas as they endorsed my re-election bid and presented a cash cheque donated by constituents towards the purchase of my nomination form to continue serving the Yabo/Shagari Federal Constituency in the 2027 general elections under the banner of the ADC.

The overwhelming show of confidence, solidarity, support, and endorsement demonstrated by the people is deeply humbling and highly appreciated. This gesture is not only a reflection of the trust reposed in our leadership, but also a strong encouragement to remain committed to the ideals of quality representation, inclusiveness, and service to humanity.

I sincerely thank the people of Yabo and Shagari for their endorsement, prayers, undiluted support, and continued belief in our shared vision for the progress and development of the constituency.

By the grace of Almighty Allah (SWA), I remain dedicated to serving with sincerity, justice, and accountability. Thank you very much.

- Dan Majen Yabo

=========================================================

Alhamdulillahi. Da yardar Allah Maɗaukakin Sarki (SWA), Yau a ƙaramar hukumar Yabo, na samu damar kasancewa tare da al’ummar ƙananan hukumomin Yabo da Shagari yayin da s**a bayyana goyon bayansu ga takarar neman sake zaɓena tare da gabatar min da kuɗaɗen da al’umma s**a tara domin sayemin foam ɗin sake tsayawa takara domin cigaba da waƙiltar Mazaɓar Tarayya ta Yabo/Shagari a zaɓen shekarar 2027 ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ADC.

Wannan gagarumin nuna amincewa, haɗin kai, goyon baya da kuma sahalewar da al’umma s**a nuna min abin alfahari ne kuma abin godiya matuƙa. Wannan karamci da aka nuna ba wai kawai alamar yarda da amincewa da shugabancinmu ba ne, yana ƙara mana ƙwarin gwuiwa ne wajen cigaba da bayar da waƙilci nagari, adalci, haɗa kai da kuma hidima ga al’umma.

Ina miƙa godiya ta musamman ga al’ummar Yabo da Shagari bisa wannan sahalewa, addu’o’i, cikakken goyon baya da kuma cigaba da yarda da manufarmu ta ci gaban mazaɓar mu.

Da ikon Allah Maɗaukakin Sarki (SWA), zan cigaba da gudanar da ayyukan waƙilci cikin gaskiya, riƙon amana da adalci. Na gode.

- Dan Majen
Bilya Yabo Muhammad

Yanzu Inba Sokoto ba Ina aka Haka?Al’ummar cikin Gari na Fama da Rashin Ruwan sha Amma Anzo a Gina Borehole cikin Rounda...
27/04/2026

Yanzu Inba Sokoto ba Ina aka Haka?

Al’ummar cikin Gari na Fama da Rashin Ruwan sha Amma Anzo a Gina Borehole cikin Roundabout.🥹

HOTUNA: Matasan ADC a Sokoto Sun Yi Zanga-Zanga a Sokoto, Sun Nemi Amupitan Ya Yi MurabusMatasan jam’iyyar African Democ...
22/04/2026

HOTUNA: Matasan ADC a Sokoto Sun Yi Zanga-Zanga a Sokoto, Sun Nemi Amupitan Ya Yi Murabus

Matasan jam’iyyar African Democratic CongressADC rashen jihar a safiyar yau sun gudanar da zanga-zanga a ofishin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC da ke Sokoto.

Masu zanga-zangar sun bukaci shugaban jam’iyyar na kasa, Mr.Joash Amupitan, da ya yi murabus daga mukaminsa.

Sun na dauke da alluna masu dauke da sakonni kamar: “ADC Ba ta Sayarwa Ba Ce”, “Amupitan Ya Riga Ya Lalace”, da kuma “Dimokuradiyya Tattaunawa Ce, Ba Mulkin Kai Kadai Ba.”

TARONDA HON BELLO MUAZU WALIN KWARE YA SHIRYA NA KARBAR KATIN ZAMA HALASTACCEN DAN JAM IYAR ADC DAKUMA TABBATAR DA ANNIY...
19/04/2026

TARONDA HON BELLO MUAZU WALIN KWARE YA SHIRYA NA KARBAR KATIN ZAMA HALASTACCEN DAN JAM IYAR ADC DAKUMA TABBATAR DA ANNIYARSA TA TSAYAWA TAKARAR KUJERAR DANMAJALISAR TARAYYA MAI WAKILTAR KANANAN HUKUMOMIN KWARE DA WAMAKKO

Hon. Bello Mu’azu (Walin Kware) ya karɓi katin zama cikakken ɗan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a wani muhimmin taronda da dubban al ummar dake yankuna da dama dake karamar hukumar mulkin kware s**a halarta a jiya taron ya gudana ne a karamar hukumarsa ta Kware.

An gabatar masa da katin ne ta hannun Shugaban Rijistar na Ward dinsa dake Kware, Malam Mansur, dakuma ƙarƙashin jagorancin Shugaban Rijistar Jam’iyya kuma Shugaban Elders na Karamar Hukumar mulkin Kware, Alhaji Isah Sahabi Bankanu.

Bisa kira da goyon bayan al’umma, Hon. Bello Mu’azu ya yi amfani da wannan dama wajen bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Dan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Kware/Wammako.

Taron ya samu halartar zababben shugaban jam iya Alh Danda Hamma'ali da ma ajinsa Alh Abdurrahaman jaros tareda sakataren jam iya na sokoto ta tsakiya Dr Aminu Jabbi durbawa shugaban elder, Alh Isah sahabi Bankanu tsohon shugaban karamar hukumar mulkin kware Hon Basansan tsohon shugaban jam'iyar PDP Dandare jingine dadai sauran shuwagabanni masu ruwa da tsaki na jam iyar ADC, da shugabanin mata da maza da matasa sauran yan kasuwa da yan boko da sauran al ummar Karamar Hukumar mulkin kware.

Hon. Bello Mu’azu ya nuna godiya ga dukkan shugabanni, magoya baya, da masu fatan alheri bisa halartar su da goyon bayan su, tare da jaddada kudurinsa na hidimtawa al’umma da tabbatar da cigaban Kware/Wammako.


,Maryam Garba WamakkoBiographyMaryam Garba Wamakko hails from Birnin Kimba in Wamakko LGA, with a rich ancestral heritag...
18/04/2026

,Maryam Garba Wamakko

Biography

Maryam Garba Wamakko hails from Birnin Kimba in Wamakko LGA, with a rich ancestral heritage rooted in both scholarly and historical traditions.

Paternal Lineage (Birnin Kimba, Wamakko LGA)
Muhammadu Kimba a participant in the Sokoto Jihad during the time of Sheikh Usman Danfodiyo
Safna Muhammadu Gwaggo-
Ibrahimu-
Garba (Buba)-
Maryam Garba Wamakko

Maternal Lineage (Wamakko LGA)
Barade Muhammadu Mancunga (1804–1807)-
Barade Muhammadu Hafsa (1807–1820)-
Barade Gainako (1850–1882)
Aishatu (Utiya)-
Muhammadu Gidado
Hauwa’u Gidado (Haj Yarsarki)
Maryam Garba Wamakko

Profile Summary

Maryam Garba Wamakko is an indigene of Wamakko LGA by origin ,a dedicated academic and seasoned public administrator with extensive experience in teaching, research, and governance. She has demonstrated strong leadership across educational institutions and public service, rising through the ranks from lecturer to senior executive roles, including Director General and a pioneer female Permanent Secretary in Wamakko LGA..

Masha Allah. Alhamdulillah.

GAYYATA TA MUSAMMANA madadin Tsohon Shugaban Matasan Sokoto ta Tsakiya, Na sanar da al’umma gaba ɗaya, musamman masu ruw...
16/04/2026

GAYYATA TA MUSAMMAN

A madadin Tsohon Shugaban Matasan Sokoto ta Tsakiya, Na sanar da al’umma gaba ɗaya, musamman masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ADC cewa:

Za a gudanar da taron karɓar katin zama cikakken ɗan jam’iyyar ADC tare da Sanarwa tsayawa Takara.

Wanda za a gudanar kamar haka:

Rana: Asabar, 18 ga Afrilu 2026
Lokaci: 10:00 na safe
Wuri: Gidan Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Sokoto,
His Excellency Hon. Dr. Muhammad Manir Dan Iya FCNA(Walin Sokoto), Tudun Wada, Kware

Ana sa ran halartar ku domin nuna goyon baya ga ɗan uwanku kuma abokin ku, Bello Muazu (Walin Kware).

Allah (SWT) Ya ba mu ikon halarta. Amin.


13/04/2026

Jawabin Mataimakin shugaban Jam'iyar ADC Na jahar sokoto Watau Bello isheeku kigan A wurin Kaddamarda shugabanin jam'iyar ADC.

Alhamdulillahi Dan majalisar tarayya Mai wakiltar Tambuwal/Kebbe Hon Abdussamad Dasuki ya karbi katinsa na zama cikakken...
08/04/2026

Alhamdulillahi

Dan majalisar tarayya Mai wakiltar Tambuwal/Kebbe Hon Abdussamad Dasuki ya karbi katinsa na zama cikakken Dan jam 'iyar ADC Alheri a mazabar sa dake Dogon daji Tambuwal.

Kungiyar SOSMO Sunyi gaisuwar ta'aziyyar mahaifiyar Jami'in hulda da jama'a na wannan kungiya A garin Shagari Ammar Muha...
28/03/2026

Kungiyar SOSMO Sunyi gaisuwar ta'aziyyar mahaifiyar Jami'in hulda da jama'a na wannan kungiya A garin Shagari Ammar Muhammad Shagari bisa ga Rashin da yayi na mahaifiyar sa.

Shugaban Kungiyar na tareda rakkiyar Mataimakin sa Hon Usman Yahaya Sarda da Sakataren kungiya Buhari Lawal Baban Maheer da Zonal sakatare Sokoto ta tsakiya Yahaya Akora da shugaban Kungiyar coordinators na kananan hukumomi Shamsudeen Bello Hamma'ali.

An gudanarda adduo'i na neman Rahama ga Ruhin mamaciyar

INNALILLAHI WA INNA ILAIHIN RAJI'UN Mai girma wakilin Kebbe/Tambuwal a majalisar tarayyar Najeriya Hon. Abdussamad Dasuk...
25/02/2026

INNALILLAHI WA INNA ILAIHIN RAJI'UN

Mai girma wakilin Kebbe/Tambuwal a majalisar tarayyar Najeriya Hon. Abdussamad Dasuki (SanTurakinSakkwato), ya yi gaisuwar ta'aziya ga abokin aikin sa Hon. Bashir Usman Gorau, akan rasuwar mahaifinsa wanda Allah ya yiwa cikawa abisa cikar wa'adi.

An gudanar da addu'o'e na musamman domin neman gafarar Allah ga margayin , da fatar Allah ya jikanshi ya gafarta masa ya yafe dukkanin kura-kurransa. Allah ya kyautata tamu bayan ta su, Amin summa Amin.

Address

Sokoto

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sokoto State Social Media Organization posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share