20/07/2026
MA'AIKATAR ILIMIN FARKO DA SAKANDARE TA JIHAR SOKOTO
SANARWA
Ma'aikatar Ilimin Farko da Sakandare ta Jihar Sokoto, ta hannun Sashen Harkokin Jarrabawa, ta samu rahotannin cewa wasu ɗaliban aji na SS3 na shirin gudanar da bikin da ake kira "Sign-Out" da kuma wasu ayyuka da ba a amince da su ba bayan kammala jarabawarsu.
A sakamakon haka, Ma'aikatar tana gargaɗin dukkan ɗaliban SS3 da su guji shiga ko shirya duk wani bikin "Sign-Out" ko wani aiki da zai iya haddasa tashin hankali, tayar da hankalin jama'a, lalata kadarorin makarantu, jefa rayuka cikin haɗari, ko kuma bata sunan makarantunsu da na Ma'aikatar Ilimi.
An bayyana cewa duk wani ɗalibi da aka samu da hannu a irin waɗannan ayyuka zai fuskanci matakan ladabtarwa da s**a dace bisa ƙa'idoji.
Haka kuma, Ma'aikatar ta umarci dukkan Shugabannin Makarantu da Jami'an Kula da Jarrabawa da su ɗauki matakan kariya da s**a dace domin hana gudanar da duk wani bikin "Sign-Out". An kuma buƙace su da su wayar da kan ɗalibai kafin kammala jarabawarsu, su ƙara tsaurara sa ido a cikin makarantu da kewaye da su, tare da gaggauta sanar da hukumomin da s**a dace idan aka samu wata saɓawa domin ɗaukar matakin gaggawa.
Ma'aikatar na kira ga iyaye, masu kula da yara, shugabannin al'umma da sauran masu ruwa da tsaki da su ba da cikakken haɗin kai wajen tabbatar da cewa an kammala jarabawar cikin lumana, tsari da nasara.
ABDULLAHI ABUBAKAR
Daraktan Harkokin Jarrabawa