11/02/2025
Wani jigo a jam’iyyar APC ta jihar Sokoto, Comrade Faruk A. Shehu, ya bayyana damuwarsa kan yadda ake tafiyar da jam’iyyar a jihar, yana mai gargadin cewa idan ba a dauki matakin gyara ba, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba zai samu nasara a jihar a zaben 2027 ba.
A cewarsa, jagororin jam’iyyar APC a jihar na nuna rashin kulawa da masu ruwa da tsaki da s**a taka rawar gani wajen samun nasarar Tinubu a zaben 2023, musamman tsohon Sanatan Sokoto ta Kudu, Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba.
Ya ce Sanata Danbaba ne ya fi kowa kokari a jihar wajen ganin nasarar APC, inda ya kashe dukiya mai tarin yawa fiye da sauran jiga-jigan jam’iyyar. Haka kuma ya yi amfani da iliminsa da fasaharsa wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar, amma yanzu ba a ba shi wani matsayi a matakin kasa ko jiha.
A cewarsa, da ya kamata a bashi kujerar Minista amma ba a yi hakan ba, sannan kuma ba a bai wa magoya bayansa wani mukami a jihar ba – babu kwamishina, babu S.A, hatta shugabancin kananan hukumomi ba a ba su ba, duk da cewa Sanata Danbaba ne ya ba da kaso 45% na kuri’un da APC ta samu a 2023.
Comrade Shehu ya yi gargadin cewa idan Sanata Danbaba ya fice daga APC, jam’iyyar ba za ta iya samun nasara a Sokoto ba saboda kusancinsa da talakawan jihar.
Ya bukaci Shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da ya dauki matakin gaggawa don ceto jam’iyyar a jihar Sokoto, tare da ba da hakki ga Sanata Danbaba domin ya cigaba da hidimtawa al’umma.
A cewarsa, idan ba a dauki mataki ba, magoya bayan Sanata Danbaba za su fito zanga-zanga ta lumana domin nuna rashin amincewa da irin yadda ake tafiyar da jam’iyyar a jihar.