23/05/2026
KWAMISHINAN LAMURAN ADDINI YA ZIYARCI AIKIN SABUNTA MASALLACIN SHEHU USMAN ƊAN FODIYO
A cigaba da bibiyar muhimman ayyukan ci gaban addini da gwamnatin jihar Sokoto ke gudanarwa, Mai girma Kwamishinan Lamuran Addini na jihar Sokoto, Dr. Jabir Sani Maihula, ya kai ziyarar gani da ido a aikin sabunta Masallacin Sheikh Usmanu Ɗan Fodiyo da ke gudana a jihar.
Aikin sabunta masallacin na gudana ne karkashin jagorancin Mai girma Gwamnan Jihar Sokoto, Dr. Ahmed Aliyu Sokoto, PhD, tare da kulawar Ma’aikatar Lamuran Addini ta Jihar Sokoto, a matsayin wani bangare na kokarin gwamnatin jihar na bunkasa harkokin addini da kyautata wuraren ibada.
Kamar yadda aka sani, fifita lamuran addini da tallafawa harkokin addinin Musulunci na daga cikin muhimman ajandodin gwamnatin Dr. Ahmed Aliyu Sokoto.
Yayin ziyarar, ɗan kwangilar da ke gudanar da aikin ya bayyana cewa aikin ya kai kusan kashi hamsin cikin ɗari (50%) na matakin kammalawa. Ya kuma bayyana cewa jinkirin da aka samu ya samo asali ne daga yadda aka fara aikin tun daga tushe domin tabbatar da inganci da ɗorewar ginin.
Haka kuma, ya tabbatar da cewa sun tanadi dukkanin kayan aikin da ake bukata tun kafin lokaci, abin da ya ce zai taimaka wajen hanzarta aikin da kuma tabbatar da kammala shi cikin kankanin lokaci, in sha Allah.
A nasa jawabin, Dr. Jabir Sani Maihula ya bayyana cewa wannan ita ce ziyara ta uku da yake kaiwa wajen aikin tun bayan fara shi, domin tabbatar da cewa ana gudanar da aikin yadda ya kamata.
Kwamishinan ya yaba da yadda ya tarar ana cigaba da aiki yadda ya dace, tare da jinjinawa ɗan kwangilar kan ƙoƙari da himmar da yake nunawa wajen tabbatar da nasarar aikin.
Haka kuma, ya yi kira gare shi da ya ƙara zage damtse domin ganin an kammala aikin cikin lokacin da aka tsara.
Jabir Abubakar Wakili
Ofishin Kwamishinan Lamuran Addini na Jihar Sokoto