27/02/2026
KASAR NAN FA TANA A HANNUN YAN SARI, KUJI👂 DA KYAU
Duk wanda yake bibiyanr al'amuran da suke gudana a kasar nan yasan cewa akwai matsala sosai ta bangarori masu yawa. Akwai wata matsala da Ministan lafiya Prof. Ali Pate yayi magana akan ta kwanaki, itace budget implementation na 2025 data wuce.
Yace a cikin Naira biliyan 218 da aka ware wa ma'aikatar lafiya a 2025 Naira miliyan 36 kawai aka sakar musu. Fisabilillahi don Allah ya za'a yi a gudanar da 'kasa da irin wannan abun, daga cikin 218 billion an bayar da 36 million rak. Idan ba nayi kuskuren lissafi ba 0.0165 percent fa kenan.
Binciken da Majalisar dattawa data wakilai s**a yi sun gano cewa mafiya yawan ma'aikatun gwamnatin tarayya basu samu kudin da ya zarce kaso biyar cikin dari na abinda aka tsara za'a basu ba, five percent out of hundred, duk irin Bashin kudaden da ake karbowa, don Allah yaya za ayi a tafi a haka?
Sati biyu da s**a wuce Majalisar dattawa s**a kira Ministan kudi s**a ce yazo yayi bayani akan me yasa ba'a yi implementing budget din da akalla kaso 35 ba? sai Ido kawai bai iya gamsar dasu ba. S**a ce masa Bashin da aka yi ta karbowa me aka yi dasu? ina suke? bai basu gamsassun amsa ba.
A lokacin sai s**a aike da sako zuwa ga karamar Ministan kudi tunda tana da hakki akan budget implementation na Nigeria, s**a neme ta sama da kasa matar taki zuwa.
Sai s**a cewa babban Ministan kudi dole ya kawo musu ita yau Al-hamis, yace zai zo da ita, zuwa yanzu ban san me ya faru ba tsakanin 'yan Majalisun da ita karamar Ministan kudi a yau Alhamis.
Federal ministries da yawa haka suke a bushe, babu wani aikin da ake iya aiwatarwa yadda ya kamata saboda ba'a sakar musu kudaden da s**a kamata ba. Kaje duk wata Federal Secretariat a kasar zaka tabbatar da haka.
Idan babban Minista irin Prof. Ali Pate zai fito ya fadi abinda aka basu dan kadan haka, duk irin kawaicin sa, da girman matsayin sa a ciki da wajen Nigeria, da yadda yake ba mutum ne mai yawan magana ba, toh ka san akwai matsala sosai.
Ta yaya kasa zata ci gaba a irin wannan yanayin don Allah?
Daga Karshe Ina rokon Allah ya basu ikon gyarawa ya dora su akan daidai suyi abinda zai taimaki kasar nan da al'umma Idan Kuma basuda rabon gyarawa Allah ya chanza Muna su wadan su shugabanni dake tausayin bayin Allah