23/09/2022
Lokacin babban zaɓe naƙasa saiƙara gabatowa shikai, Muna ƙara kira da babbar murya ga jama'ar jaharmu ta Sakkwato Mai Albarka da aƙara sa Lura adubi chanchanta da nagarta da dattako wurin zaɓen Ɗantakara Wanda zamu damƙama amanar jaharmu mai Albarka da ɗimbin tarihi.
Alal haƙiƙa jaharmu ta Sakkwato da mutanenta Munada ƙima da mutumci a idon duniya' Sakkwato birnin Mujaddadi Shehu Usmanu danfodiyo ta, Sakkwato itace Cibiyar addini da tarbiya da mutumta Ɗan adam batareda nuna ƙyamaba saboda bambancin ƙabila ko yare kokuma addini Tsawon tarihi muna zamne lahiya da kowa, ɗan gari da baƙo.
Yakamata matasammu suƙara maida hankali ayi siyasa mai tsabta batareda cin mutumcin juna ba, ballantana har takaiga Zubda jini. Domin muƙara tabbatarma Duniya haryanzufa Sakkwato birnin Mujaddadi Shehu Usmanu danfodiyo ta,
Muna ƙara kira ga matasanmu sukai zukata nesa bambancin jam'iyya karshi kaimu ga aikata abin ashsha ko ta'addanci, wanda shi zai kaimu ga danasani, Tsabtatattar siyasa itace gimshiƙin samun warakarmu da cigaban jaharmu,
Kowa yasan abinda atdaidai Donhaka musa Lura muzaɓi yan takarar da Mukeda sarai na bazasu haifarda jagaliyanci ko rashin dattako ba,
Mulura da Waɗanda sunkasan girman Magabatanmu da Sarakunan mu da malaman mu dakuma ƙima da martabar Al'ummarmu domin kyautatuwar goben mu data ɗiyanmu da ƙannenmu.
Fatarmu shine asamu Cikakken cigaba wanda zai haifarmuna ɗa mai ido.
Allah shikawo muna ɗauki gameda tsaron jaharmu tareda kawo ƙarshen musibar rashin tsaro da rashin tabbas da muka samu kammu aciki Musamman yankunan Gabashin Sakkwato dama dukkan faɗin ƙasarmu Baki ɗaya.
Sep/24/2022.