Vision FM Listener's association Sokoto

Vision FM Listener's association Sokoto Wannan Shafin Yana Watsa Ayukkan Da Manufofin Kungiya ne Kawai

05/02/2024

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Mujitaba Mahi Lawal, Muhammad Umar

*VISION-FM LISTENERS ASSOCIATION SOKOTO**_VIFLAS 8 YEAR'S ANNIVERSARY_**Programs Of Events:**Tsarin Ranakun Bukin Cikar ...
21/11/2023

*VISION-FM LISTENERS ASSOCIATION SOKOTO*

*_VIFLAS 8 YEAR'S ANNIVERSARY_*

*Programs Of Events:*

*Tsarin Ranakun Bukin Cikar Shekaru Takwas 8 Na Kungiyar VIFLAS Da Shi Kanshi Gidan Rediyon Vision-Fm Sokoto Da Kafuwa a Wannan Jahar tamu*

Za'a Fara Gudanar Da Bukin ne A ranar Juma'a 24 ga Watan 11, Har Zuwa 27 ga Watan 11, 2023.

*Rana ta Farko:* Jumma'at 24-11-2023.
Za'a Gudanar Da Karatun Al-ƙur'ani Mai Girma Tare Da Yin Addu'o'in Na Musamman Ga Ƙasar Mu Najeriya da Jahar Mu Tare Da Gidan Rediyon Vision-Fm Dama Ƙungiyar VIFLAS.

*Wuri:* A Harabar Masalacin Jumu'a Dake Cikin police Barack A Unguwar Marina Dake Cikin Birnin Sokoto.
*Lokaci:* Da Karfe 09:00am Na Safe.

Duk a Ranar ta Jumma'a...

Za'ayi Wasar Sada Zumunci Tsakanin Ma'aikatan Gidan Radion vision fm Sokoto Da kuma Membobin Kungiyar viflas A Filin Wasa Na Abdullahi Shehu Sport centre Dake Mabera Salame Dai dai gidan man NNPC

Lokaci : 3:30 Na
Yamma

*Rana ta biyu:* Asabar
25-11-2023
Kungiyar VIFLAS Zata Kai Tallafin Kayan Amfani Ga Marayu Da Ƴan Gudun Hijira Dake Zaune a Shiyar Gandu Kasuwar Daji.

Kayan Sun haɗa da...
Tufafi
Manshafawa
Sabulun Wanki
Sabulun Wanka
Omo Da Dai Sauran Su.

*Rana ta Ukku:* Lahadi 26-11-2023.
A Ranar Ne Ƙungiyar VIFLAS Zata Gudanar Da Gagarumin Taron Bukin Cikar Ƙungiyar Da Gidan Rediyon Vision-Fm Sokoto Shekaru takwas (8) da kafuwa a Jahar Sokoto.

Tare Da Yaye Dalibai Dari Da Hamsin Wadanda Kungiya ta dauke Nauyin koyama Sana'o'in Hannu kala-kala Da kuma Gabatar musu da Shaidar Karbar Horo.

Hakama Za'a Gabatar da Ƙasida Akan Muhimmancin Dogaro dakai A cikin Al'umma

Tare da Karrama Wasu Fitattun Mutane Daga kowane Ɓangare Na Al-umma.

*Wuri:* A Makarantar Sultan Macciɗo Institute sokoto.
*Lokaci:* karfe 09:30am Na Safe

Duk dai Acikin Shagulgulan Murnar Cikar VIFLAS Da Vision-Fm Sokoto Shekaru Takwas

Kungiyar VIFLAS Zata Kai Tallafin Kiwon Lafiya, A Karamar Hukumar Mulkin Rabah . Karkashin Jagorancin chiarman Na viflas Na Rabah Cmrd bilyaminu Umar ...

Tallafin Kiwon Lafiyar Dai Ya Keɓanta Ne Ga Mata Musamman Masu Juna Biyu Tare Da Ƙananan Yara inda Za'a iya Masu Gwaje-gwaje Akan Cutar Maleria Da Kuma Bayar Da Magunguna A Ƙyauta.

Tare da Wayar Da Kai Akan Muhimmancin Kula da Lafiya Da Zuwa Asibiti Akai-akai Tare Da Kwana Cikin Gidan Sauro.

Muna Godiya Fatan Mu Allah Ya Bamu Nasara Yasa Muyi Waɗannan Tarukan Lafiya Mu Kammala Lafiya.

*Sanarwa Daga:*
Daga offishin Jami'in Hulda Da Jama'a ( P R O)

02/10/2023

Sanarwa Sanarwa Sanarwa

A Cigaba da kokarin da Takeyi na ganin al. Umma sun dogara da kansu, Musaman matasa maza da Mata, yanzu haka Kungiyar viflas ta fito da Tsaren koyar da Sana.oin Hanu, ga Dimbin Matasan Dake fadin wanan jihar ta Sokoto.

Duka wanan sherin An fito dashi ne, Domin bukin muranr Cikar Kungiyar viflas da gidan Radion vision fm shikara takwas da kafuwa anan jihar Sokoto.

Da Haka Kungiyar ke Farinchikin sanar da Al. Umma cewa za.a fara sayarda foam din koyon wadanan Sana.oin daga gobe talata zuwa jumu.a

Wurin saida foarm din=
Waziri model primary School kofar Rini

Time =
Karfe shadaya na Rana zuwa karfe biyu na Rana

Ranakun saida foarm din =
Daga gobe talata zuwa ranar jumu.a

GA masu neman Karin bayani kuna iya tuntubar wadanan numbobin wayar kamar Haka :

07068517369
07068849871

02/09/2023

GENERAL MEETING !!!
Gayyata Ga Dukkan Membobi da Masu Sha'awar Shiga, Gobe Lahadi 04:00pm at- GDSS K/marke

BARKA DA SALLAH...Amadadin Ƙungiyar VIFLAS da Gidan Rediyon VISION-FM Sokoto muke Gayyatar Ilahirin Al'ummar Sokoto da K...
29/06/2023

BARKA DA SALLAH...

Amadadin Ƙungiyar VIFLAS da Gidan Rediyon VISION-FM Sokoto muke Gayyatar Ilahirin Al'ummar Sokoto da Kebbi da Zamfara Zuwa Bukin Babbar Salla da zai Fara daga Gobe Jumma'a har zuwa Ranar Lahadi...

Tare da Ƴan Wasa na Cikin Gida dana Waje ciki harda...

Ummi ƙarama_ LABARINA
Rayyah_ KWANA TASA’IN

da sauran Fitattun Mawaƙa da waɗannan Jahohi, za’a Gudanar da Waɗannan Wasanni kamar haka:

Ranar Jumma'a:
A Vision-Fm Bankin Manoma_ ƙarfe 03:00pm zuwa 06:00pm

Duk a Ranar Jumma'a:
A Mai gero Theater_ Ƙarfe 07:00pm zuwa 10:00pm.

Haka ma A Ranar Assabar:
A Vision-Fm Bankin Manoma_ ƙarfe 03:00pm zuwa 06:00pm

Duk a Ranar Assabar:
A Mai gero Theater_ Ƙarfe 07:00pm zuwa 10:00pm.

Sai kuma Ranar Lahadi.
A mai Gero Theater (kusa da Government House)_ Ƙarfe 06:00pm Zuwa 09:00pm.

Gate pass= ₦500 Only.

Kuɗin Shiga kowace daga cikin Waɗannan Wasanni Akan Naira ɗari ne biyar kacal kowace.

Muna Maraba da Zuwan Ku.

Samarwa:
Ofishin Yaɗa Labarai na VIFLAS.

VIFLAS GENERAL MEETING...©Photos...
19/06/2023

VIFLAS GENERAL MEETING...
©Photos...

Address

Birnin Sakkwato
Sokoto

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Vision FM Listener's association Sokoto posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Vision FM Listener's association Sokoto:

Share