Mrs Ubandoma campaign Team

Mrs Ubandoma campaign Team Her Excellency Asiya Saidu Umar Ubandoma Forum

14/08/2024
Nasrun minallah, inshaAllah
24/01/2024

Nasrun minallah, inshaAllah

KADDAMAR DA BADA TALLAFI GA ALUMMAR MAZABAR GAGI ‘C’Mai girma matar dan Takarar gwamnan jahar Sokoto Karkashin Tutar Jam...
28/07/2023

KADDAMAR DA BADA TALLAFI GA ALUMMAR MAZABAR GAGI ‘C’

Mai girma matar dan Takarar gwamnan jahar Sokoto Karkashin Tutar Jam'iyyar PDP Malama Asiya Saidu Umar Ubandoma, tareda Tawagarta a jiya Alhamis ta halarci bukin kaddamar da bada tallafi ga marayu, 'yan uwa da kuma Al'umma mutun dari biyu da Hamsin (250) da buhun gumi dan gote kwara dari biyu da Hamsin ( 250) ga mata da maza, wadan da s**a fito daga karamar hukumar mulkin Sakkwato ta kudu, mazabar Gagi ' C' wanda Abdullahi Hayatu ( Barawan gabas) ya dau nauyi.

Malama Asiya tayi takaitaccin jawabi wajen kaddamar da wannan tallafi ga marayu, inda ta fara da godiya ga Allah SWT da ya kawo rayuwar mu wannan rana mai albarka kuma rana wanda tayi dai dai da azumin Ashura da Tasu'a, tareda mika jinjina ga Bafarawan Gabas akan irin namijin kokari da ya keyi, Malama Asiya ta roki Allah SWT daya saka masa da Mafificin Alheri kuma yabashi ladar wannan tallafi da ya bada.

Bafarawan gabas yayi godiya matuka da kuma jin jina ga matar Malama Asiya akan halartar wannan taro na bayan da tallafi ga wadannan mutanen, wanda a cikin jawabin sa yake godiya ga Allah da yabashi ikon aiwatar da wannan tallafi da kuma kara godiya ga Allah SWT da yakawo muna Irin Malama Asiya a jahar sokoto a matsayin jajirtattar Macce



28-07-2022

Eid Mubarak 🌙May this Eid bring you and your family abundant happiness, prosperity, and peaceMay Allah shower His blessi...
28/06/2023

Eid Mubarak 🌙

May this Eid bring you and your family abundant happiness, prosperity, and peace

May Allah shower His blessings upon you and fulfill all your wishes and aspirations.

Taqaba Allahu minna wa minkum ✨🤲🏽

Happy Eid-Adha 🐏 to all Muslims Umma

HALARTAR WALIMAR NADIN SARAUTAR SARAUNIYAR SHARIFFAI..A ranar Lahadi wanda yayi dai dai day 1/05/2023, Matar Dan Takarar...
25/05/2023

HALARTAR WALIMAR NADIN SARAUTAR SARAUNIYAR SHARIFFAI..

A ranar Lahadi wanda yayi dai dai day 1/05/2023, Matar Dan Takarar Gwamnan Jahar Sokoto Karkashin Tutar Jam'iyyar PDP Malama Asiya Saidu Umar Ubandoma tare da Tawagarta sun Halarci Walimar Nadin Sarautar Mai baiwa gwamna shawara akan hukumar kare hakkin bil adama da kungiyoyi masu zaman kansu Inna Ubaida Muh'd Bello A matsayin Sarauniyar Shariffai ta Farko a jahar Sokoto wanda aka Gudanar a Gidan ta dake Arkilla Millionaires Quarters.

Malama Asiya Ta roki Allah SWT daya Sanya Alheri ga wannan Sarauta Kuma ya taya Riko, ta kuma Roki Allah ya Albarkaci wannan Sarauta Kuma Yabada ikon Sauki Wannan Nauhi da ya Rataya Akan ta.


Jumu’at Kareem Your Excellency 🕋📿
05/05/2023

Jumu’at Kareem Your Excellency 🕋📿

Eid Mubarak 🌙🎉❤️May this Eid bring you and your family abundant happiness, prosperity, and peaceMay Allah shower His ble...
22/04/2023

Eid Mubarak 🌙🎉❤️

May this Eid bring you and your family abundant happiness, prosperity, and peace

May Allah shower His blessings upon you and fulfill all your wishes and aspirations.

Taqaba Allahu minna wa minkum ✨🤲🏽

ZIYARAR BAN GIRMA DA NEMAN TUBARRAKI A FADAR ME ALFARMA SARKIN MUSULMI.Matar Gwamnan jahar Sokoto Dr. Mariya Aminu Wazir...
16/03/2023

ZIYARAR BAN GIRMA DA NEMAN TUBARRAKI A FADAR ME ALFARMA SARKIN MUSULMI.

Matar Gwamnan jahar Sokoto Dr. Mariya Aminu Waziri Tambuwal, Matar dan Takarar Gwamnan Jahar Sokoto Karkashin Tutar Jam'iyyar PDP Malama Asiya Saidu Umar Ubandoma Tare da sauran tawaga sun Ziyarci Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubukar Mni CFR domin isar da Gaisuwar ban Girma tare da Neman tubarraki da shawarwari a fadar sa dake garin jahar Sokoto.


16-03-2023

TARON KARSHE NA MATA, NA GANGAMIN YEKUWAR NEMAN ZABEN GWAMNONI TARE DA YAN MAJALISUN JAHA NA ZABEN 2023 A Jiya Laraba ne...
16/03/2023

TARON KARSHE NA MATA, NA GANGAMIN YEKUWAR NEMAN ZABEN GWAMNONI TARE DA YAN MAJALISUN JAHA NA ZABEN 2023

A Jiya Laraba ne, Mai girma Gwamnan Jahar Sokoto Hajiya Mariya Aminu Waziri Tambuwal tare da Matar Dan takarar gwamnan jihar Sokoto Karkashin tutar Jam'iyyar PDP Malama Asiya Saidu Umar Ubandoma, hadi da Shuwagabannin Jam'iyyar PDP Mata na jahar Sokoto sun Halarci taron yekuwa na karshe na neman zaben dan takarar gwamnan jahar Sokoto da yan Majalisun jaha wanda ya gudana a women Development center dake kan titin dasuki road, a cikin garin Sokoto Central Senatorial District.

Inda aka yi jawabi na musamman daga mata shuwagabannin Jam’iyar PDP, daga karshe avikin jawabin matar Dan da karat gwamnan jihar sokoto Malama Asiya Tayi Kira ga mata musamman iyaye Akan suyi tunanin goben su da Na diyan su akan shugaban da zasu zaba, Tayi fatan nasara ga Jam’iyar PDP baki daya.

Taron ya samu halatar matar gwamnan jihar sokoto inda ta samu wakilcin Prof. Aisha Madawaki, Matar Dan takarar gwamna,Matan chairman din Jam’iyar PDP, matan sakataren Party, BOT ta kasa ta jam’iyar PDP, matan comishinoni, comishinoni mata, matan Chaimomi, Zonals, DG’s, Ma’aikatan gwamnati na din dindin, SA’s da sauran jiga jigan matan ya Siyasa da mata yansiyasa.


16-03-2023.

A yayin da Matar Dan Takarar Gwamnan Jahar Sokoto Karkashin Jam'iyar PDP Malama Asiya Saidu Umar Ubandoma Ta Isa Gurin J...
25/02/2023

A yayin da Matar Dan Takarar Gwamnan Jahar Sokoto Karkashin Jam'iyar PDP Malama Asiya Saidu Umar Ubandoma Ta Isa Gurin Jefa Kuri'a

Malama Asiya Ta Iso runfar ta domin kada kuri’arta a mazabar magajin Rafi ‘B’ Runfar makama 012.

Muna Rokon Allah (SWA) Ya Tabbatar Muna Da Nasara Da Rabo Mai Albarka Daga Sama Harkasa

PDP Power


25-02-2023

A JIYANE MATAR DANTAKARAR GWAMNAN JIHAR SOKOTO KARKASHIN TUTAR JAM’IYAR PDP MALAMA ASIYA SAIDU UMAR UBANDOMA TA YAYE DAL...
24/02/2023

A JIYANE MATAR DANTAKARAR GWAMNAN JIHAR SOKOTO KARKASHIN TUTAR JAM’IYAR PDP MALAMA ASIYA SAIDU UMAR UBANDOMA TA YAYE DALLIBBAN DA S**A KOYI SANA’O’I FANNI DABAN DABAN TARE DA BASU TALLAFI DOMIN DOGARO DA KANSU

WANDA KUNGIYAR FAFUTUKAR KARFAFAWA MATA DOMIN DOGARO DA KANSU KAKASHIN JAGORANCIN UWAR KUNGIYAR MALAMA ASIYA ITACE WADDA TA DAUKI NAUYIN KOYA WA MACCE (300) DAKE RINJIN SAMBO .

Address

Sokoto

Telephone

+2349064388038

Website

http://Asiya.org.com/

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mrs Ubandoma campaign Team posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Mrs Ubandoma campaign Team:

Share