15/10/2024
HONOURABLE ADAMU ADAMU MATAZU (JAGORAN GAMAYYAR ƘUNGIYOYIN MATASAN AREWACIN NAJERIYA) YA ZIYARCI DAN TAKARAR SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR SABON GARI HON. SHEIKH JAMILU ABUBAKAR ALBANI TARE DA TAWAGAR SA KUMA SUN TABBATAR DA GOYON BAYAN SU A GARE SHI.
A daren Lahadin ta gabata Shugaban gamayyar ƙungiyoyin matasan Arewacin Najeriya, kuma haifaffen garin Samarun Sabon Garin, Zaria Hon. Adamu Adamu Matazu ya ziyarci dan takarar shugaban karamar hukumar Sabon Gari Hon. Sheikh Jamilu Abubakar Albani tare da tawagar sa domin mara masa baya bisa takarar shugaban karamar hukumar Sabon Gari da yake yi.
Hon. Adamu Adamu Matazu a bayanin sa ya bayyana cewa ya kawo wannan ziyara ne tare da jama'arsa domin su nuna goyon baya ga Hon. Sheikh Jamilu Abubakar Albani a bisa wannan takarar da yake yi na Shugaban karamar hukumar Sabon Gari. Ya kara da cewa sun duba sunga a kaf cikin yan takarkarin ba wanda yafi shi cancanta, kuma a damammakin da ya samu a baya na shugabanci yayi iya bakin kokarin sa gurin taimakon jama'a da ciyar da yankin mu gaba. Saboda haka ne ya ga ya dace a mara masa baya domin samun cigaban al'ummar mu da yankin mu baki daya.
Daga bisani, Hon. Sheikh Jamilu Abubakar Albani yayi godiya kuma ya nuna farin cikinsa ga wannan goyon baya tare da tabbatar da cewa In Sha Allah idan Allah ya bada wannan dama zasu yi duk iya abinda zasu iya don ciyar da wannan yanki namu gaba.
Taron ya samu halartar dimbin matasa daga sassa daban-daban, da Shuwagabannin addini da masu sarauta da sauran su.
Muna Addu'a Allah ya bama Hon. Sheikh Jamilu Abubakar Albani Naasara a wannan zaɓe da muke fuskanta ya kuma musu jagora.
Ameen.
Umar Ahmad Abu Mus'ab
SABON_GARI_FIRST