01/12/2025
YAUSHE AKA DAUKI MATAKIN?
Da farko k**ar kullum ban cika son yin magana kan irin wadannan abubuwan da ke faruwa ba, amma taba janibin jagora abu ne da bai k**ata ayi shiru a kansa ba. Duk da haka na yi kokarin kaucewa yin magana don abinda ke iya zuwa ya komo, amma wani bawan Allah da yayi rubutu a kokarinsa na barranta Shaikh Yakubu Yahaya daga wannan rubutun shi ya tilasta ni ba don ina so ba ince wani abu. A kan haka nake rokon Allah (T) ya sa Yan uwa su mini kyakykywan fahimta, su fahimci sakon da nake son isarwa da budadden zuciya, su fahimci manufan rubutun nan ba jinginawa Shaikh Yakubu ko wani alhakin rubutun da Abu-Taliyyah yayi ba ne, su fahimci manufan rubutun shine gamsar da wani bawan Allah da ya yi rubutu da nufin kore hannun Malam Yakubu daga Abu-Taliyyah cewa hujjojinsa ba gamsassu bane.
Audio da ya kawo na saurari audion amma kuma banga alakansa da abinda ya faru ba, a cikin Audio din Shaikh din yana kokarin kore abubuwa da ake jingina masa na yabo ne, yana nuna shi matsayinsa bai kai nan ba, wannan Shaikh ya sha magana a kai musamman da yake duk wanda ya san shi, ya san yana da tawadhi'u k**ar yadda mai rubutun yace haka yaran suke fada in ya kobe su a kan sakin bakinsu da sukeyi. Wannan kadai zai nuna maka cewa ana taka musu birki ne a kan abinda ya shafi abinda Shaikh din yake gani sun kai shi matakin da bai kai bane kawai, kuma duk misalan da shi wannan bawan Allah ya kawo a kan su ne k**ar cewar wata rana yaran su na fadin Labbaika Ya Shaikh Yakubu, take ya taka musu birki ya ce musu nima Labbaika Ya Elzakzaky nake cewa. Bama haka ba duk hujjojin da mai rubutun ya kawo har da audio din ba abinda suke magana a kai illa kokarin Shaikh din wajen kore jingina masa matsayin da shi yake ganin bai kai shi ba. Babu wani abu banda wannan.
Alhali abinda ake magana a kai kuma shine a kan yaran da suke yima Shaikh din biyayya su na taba janibin Jagora da iyalan Jagora amma ba a taba jin Shaikh din ya yi jawabi a kan su ya barranta kansa da su, ya kuma nuna bacin ransa a kan abinda s**a yi, bare kuma ya kiraye su a kan lalle su tuba su sake rubutu su nemi gafaran Yan uwa. Babu yadda za a tuhumeka da rashin Akhlak sai wani da yake son wankeka ya kafa hujjah da cewa kai mai ilimi ne, ka koyar a waje kaza, yayi ta kawo hujjoji a kan iliminka. In an tuhumeka a kan rashin Akhlak sai wani yana son wankeka k**ata yayi ya kawo hujjoji ne a kan yadda kake muamala da mutane, da yadda mutane suke yabon hakayenka da sauransu ba ya buge da kawo hujjoji kan iliminka ba, in yayi haka bai gamsar da masu tuhuma ba. Kamar haka ne wannan rubutun ba yadda zai gamsar da masu tuhuma. In ana son gamsar da masu tuhuma to wajibi ne a kawo audio inda da aka taba janibin Jagora Shaikh din yayi jawabi ya nuna bacin ransa har kuma ya barranta kansa da masu s**an, kuma da misalan matakan da Shaikh din ya dauka. In anyi haka to tabbas za a gamsar da masu tuhuma.
Masu tuhuman nan cewa sukeyi wadannan yaran masoyan Shaikh ne na sosai kuma suna s**an nasun ne ma don kare Shaikh din. Cewa sukeyi idan mutum masoyinka ne ya san kana son babanka babu yadda zai koma yana s**an babanka da iyalan babanka sannan ya dawo ya zauna tare da kai, dolensa in dai ya san har yanzu kana tare da baban naka baka bar shi ba, to sai dai ya yaba mishi, in ma yaga wani abu na ba daidai ba a tare da baban naka, ba zai yarda yayi maganan a fili inda ya san maganan zai koma maka ba, sai dai yayi s**ansa a boye. Amma in zai fito a duniya ya soki babanka kai tsaye sannan washegari a gan shi a gunka kuna tare dole Yan uwanka su yi zargin anya kana son baban nakun nan kuwa. Za su ce in kana son sa to fa dole ko wanda ya soki babankun yayi mursusi yazo wajenka za ka koreshi, don ba masoyinka bane.
Cewa masu tuhumar suke yi me ya sa ba aji daga sauran amirai masu son su suna taba janibin Jagora da iyalansa ba sai mabiya Shaikh din? Cewa sukeyi ai sauran amiran ma akwai yan gani kasheninsu amma ko kusa ba a taba jin wani ya soki Jagora ko iyalan Jagora ba, saboda sun san malamin nasu ba zai taba barinsu ba, sannan kuma ma kullum yana dora su ne a kan bin Jagora da girmama iyalansu, shi ya sa ba za su iya suna masoyan amiri din kuma suna s**an Jagora ko iyalan Jagora ba.
Cewa sukeyi su ba sun ce Shaikh ne yake saka su ba, amma kuma wajibi ne ga Shaikh in akwai son Jagora ko da digo daya ne a ransa ya fito ba sai an yi ta kiraye kiraye ba ya nuna bacin ransa ga maganan da sukeyi ya barranta da su, ya ambaci sunansu ya fada cewa daga yau ba shi ba su in har ba su tuba ba, in yayi haka gobe wani ba zai sake yin mak**ancin hakan ba daga cikin masoyansa.
Cewa sukeyi a baya Hamza Lawan da haka aka fara, almajiransa masu nuna masa soyayya sosai su s**a fara s**an Jagora, a lokacin Hamza Lawan baya hana su, anyi ta kiraye kiraye a kan lalle in ba ya tare da su to ya hana su, Amma shiru shima sai dai a kafa hujjah da cewa ai ba shi yakeyi ba kuma ba ya tare da raayin su alhali kuma ana ganinshi tare da su, aka gagara gane hikiman cewa ba ka tare da raayin masu s**an malaminka alhali kuma su masoyanka ne za su soki malaminka kuma su kasance da kai, baka taba barranta kanka da su ba, baka taba hana su ba amma kuma kana cewa kai almajirin malamin da suke zagin ne. Wace kwakwalwace za ta iya yarda da hakan. Haka aka yi ta yi shi Hamza Lawan din bai hanasu ba ba a ji a bayyane yayi zagin ba shi, bai kuma hana su zagin ko rabuwa da su ba. A lokacin an tuhumi Hamza Lawan da cewa shima yana da raayin zagin don in ba sun san yana da raayin hakan ba da ba yadda masoyansa za su zagi masoyinsa jagoransa, don a bayyane yake makiyin masoyinka makiyanka ne, in kuma ka dauki makiyin masoyinka a matsayin masoyinka to tabbas a bayyane yake ka dawo makiyin wannan da ya kasance masoyin nakan. A karshe me ya faru? Hamza Lawan ya bayyana ya bi sahun almajiran nasa na yin zage zage ga Jagora.
A kan wadannan tuhume tuhumen mai rubutun ya k**ata ya kawo hujjojinsa ba kan tawadhi'un Shaikh ba.
- Miji Naseer -
13/03/2025