Sunna zallah

Sunna zallah Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sunna zallah, Library, Moramty opp 333 army barracks, Maiduguri.

11/12/2020

Daurawa Fans
ALLAH MADAUKAKI YANA KUSA !!!
Idan kullum kana tunanin cewa, abubuwan da kake fatan mallaka sun yi nesa da kai, Toh kullum ka ringa tuna cewa ALLAH Yana kusa da kai.
Acikin Alqur'ani maigirma ALLAH (ﷻ) Yana cewa:
وَإِذَا سَأَلَكَ عِبَادِي عَنِّي فَإِنِّي قَرِيبٌ أُجِيبُ دَعْوَةَ الدَّاعِ إِذَا دَعَانِ فَلْيَسْتَجِيبُوا لِي وَلْيُؤْمِنُوا بِي لَعَلَّهُمْ يَرْشُدُونَ
“kuma idan bayina s**a tambayeka game dani, Toh lallai Ni makusanci ne, ina karban kiran mai kira idan ya kirani, saboda haka su nemi karbawata, kuma suyi imani da Ni, tsammaninsu su shiryu.” [Albaqara: 186]
ALLAH (ﷻ)ne yake cewa Annabi Muhammad (ﷺ) cewa idan bayina s**a tambayeka game dani ka fada musu cewa ina kusa....
Ku sani wannan kusancin ALLAH yafi jijiyoyin dake cikin jikinmu wanda suke gudana da jini kusanci damu.
Sannan Yace Ubangijinmu mai jin addu'ar mai roko ne idan ya roke shi kuma muyi imani dashi ko zamu samu shiriya.
Idan har bawa ya tuna wannan ayar zancen Mahaliccinsa kuma yana ikirarin imani da ALLAH toh babu abunda zai dame shi ya kasa daga hannu ya kai kukansa inda za'a share masa hawaye.

11/12/2020

🍀AMFÃNIN TAƘAWA A DUNIYA🍀
2020
✍🏼 Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda ya sanya jin tsõronsa ya zamanto mafi alherin guziri inda Allah (SWT) yake cewa:

{{وَتَزَوَّدُوا فَإِنَّ خَيْرَ الزَّادِ التَّقْوَى وَاتَّقُونِ يَا أُولِي الْأَلْبَاب}} البقرة: ١٩٧

📚 Ma’ana:- “…Kuma kuyi guzuri. To, mafi alherin guzuri yin taƙawa. Kuma ku bi Ni da taƙawa, ya ma’abuta hankula.”.

Da kuma faɗinSa Maɗaukakin Sarki:

{{يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ حَقَّ تُقَاتِهِ وَلَا تَمُوتُنَّ إِلَّا وَأَنْتُمْ مُسْلِمُون}} آل عمران: ١٠٢

📚 Ma’ana:- “Yã ku waɗanda s**a yi imãni! Ku bi Allah da taƙawa, a kan hakkin binSa da taƙawa, kuma kada ku mutu fãce kuna mãsu sallamawa (Musulmi)”.

👉🏽 Sannan Allah ya haɗa jin tsõronsa “Taƙawa” da kõwane irin aikin da Musulmai za suyi a rãyuwarsu da ibãdarsu da mã mu’ãmalarsu.

👉🏼 MA’ANAR TSÕRON ALLAH (SWT) “TAƘAWA”:

📗 --Taƙawa a Lãrabce: kalma ce da take nufin kãriya ko kuma duk wani abu da mutum zai yi amfãni da shi don ya kãre kansa daga wani abu da yake tsõro.

📗 --Amma a wajen Malaman Musulunci Taƙawa nã nufin mutum ya sanya wani shãmaki ko kãriya tsakaninsa da abin da Allah ya haramta don gujewa azãbar Allah.

👉🏼 --Sayyidna Aliyyu ɗan Abi ɗãlib (R.A) ya fassara jin tsõron Allah “Taƙawa” da cewa:

📚 “Taƙawa ita ce jin tsõron Allah mai Girma da kuma aiki da Alƙur’ãni, sai kuma wadãtar zuci ga duk abin da Allah ya baiwa bãwa, da kuma tãnadi don tafiya ƙiyãma”.

✍🏼 Alƙur’ãni mai girma ya faɗakar game da taƙawa a ãyõyi da dãma, sannan ya ambaci amfãni da fã’idõjin taƙawa a duniya da mã lãhira, gã kaɗan daga cikin amfãnin da taƙawa ke janyõwa bãyi tun a rãyuwar duniya:

👉🏽 1—Taƙawa na janyo al’amuran bãwa suyi sauƙi, ba tãre da shan wahalã ba; kamar yadda Allah (SWT) Ya faɗa:

{{وَمَنْ يَتَّقِ اللَّهَ يَجْعَلْ لَهُ مِنْ أَمْرِهِ يُسْرًا}} الطلاق: ٤

📚 Ma’ana:- “…Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, (Allah) zai sanya masa wani sauƙi daga al’amurinsa”.

👉🏽 2—Taƙawa na sanyã wa bãwa kãriya game da cutar-war shaiɗan; kamar yadda Allah (SWT) yake cewa:

{{إِنَّ الَّذِينَ اتَّقَوْا إِذَا مَسَّهُمْ طَائِفٌ مِنَ الشَّيْطَانِ تَذَكَّرُوا فَإِذَا هُمْ مُبْصِرُون}} الأعراف: ٢٠١

📚 Ma’ana:- “Lalle ne waɗanda s**a yi taƙawa idan wani tãshin hankali daga Shaiɗan ya shãfe su, sai su tuna (Allah) sai gã su, sun zama masu basira”.

👉🏽 3—Taƙawa na janyo buɗe albarkatu daga sama da ƙasa; kamar yadda Allah (SWT) yake cewa:

📚 {{وَلَوْ أَنَّ أَهْلَ الْقُرَى آمَنُوا وَاتَّقَوْا لَفَتَحْنَا عَلَيْهِمْ بَرَكَاتٍ مِنَ السَّمَاءِ وَالْأَرْض…}} الأعراف: ٩٦

📚 Ma’ana:- “Kuma dã lalle ne mutãnen alƙaryu sun yi imãni kuma s**a yi taƙawa, dã, haƙiƙa, Mun buɗe albarkõki a kansu daga sama da ƙasa…”.

👉🏽 4—Taƙawa na janyõ wa bãwa dãcewa wajen ban-bance tsakãnin ƙarya da gaskiya; kamar yadda Allah (SWT) yake cewa:

📚 {{يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنْ تَتَّقُوا اللَّهَ يَجْعَلْ لَكُمْ فُرْقَانًا وَيُكَفِّرْ عَنْكُمْ سَيِّئَاتِكُمْ وَيَغْفِرْ لَكُمْ وَاللَّهُ ذُو الْفَضْلِ الْعَظِيم}} الأنفال: ٢٩

📚 Ma’ana:- “Yã ku waɗanda s**a yi imãni ! Idan kun bi Allah da taƙawa, zai sanya muku mararraba (da tsõro) kuma Ya kankare ƙananan zunubanku daga barinku. Kuma Ya gãfarta muku. Kuma Allah ne Ma’abocin falala mai girma”.

👉🏽 5—Taƙawa na fitar da bãwa daga wahala da tsanani, sannan ya sãmu hanyõyin arziƙi ta inda bãwan bai sani ba; kamar yadda Allah (SWT) yake cewa:

📚 {{وَمَنْ يَتَّقِ اللَّهَ يَجْعَلْ لَهُ مَخْرَجًا () وَيَرْزُقْهُ مِنْ حَيْثُ لَا يَحْتَسِب…}} الطلاق: ٢ - ٣

📚 Ma’ana:- “…Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, Allah zai sanya masa mafita (*) Kuma Ya arzuta shi daga inda bã ya zato…”

👉🏽 6—Taƙawa na sanyã wa bãwa dãcewa ga jiɓintar al’amarin Ubangiji, da kuma kasancewa cikin waliyyan Allah; kamar yadda Allah (SWT) yake cewa:

📚 {{…إِنْ أَوْلِيَاؤُهُ إِلَّا الْمُتَّقُونَ وَلَكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُون}} الأنفال: ٣٤

📚 Ma’ana:- “…Bãbu majiɓintanSa fãce mãsu taƙawa. Kuma mafi yawansu ba su sani ba”.

👉🏽 Da kuma faɗinsa Maɗaukakin Sarki:

📚 {{…وَاللَّهُ وَلِيُّ الْمُتَّقِين}} الجاثية: ١٩

📚 Ma’ana:- “…Kuma Allah ne Majiɓincin mãsu taƙawa”.

👉🏽 7—Taƙawa na zama sababin daina jin tsõro daga mãkircin kãfirai; kamar yadda Allah (SWT) yake cewa:

📚 {{…وَإِنْ تَصْبِرُوا وَتَتَّقُوا لَا يَضُرُّكُمْ كَيْدُهُمْ شَيْئًا إِنَّ اللَّهَ بِمَا يَعْمَلُونَ مُحِيطٌ}} آل عمران: ١٢٠

📚 Ma’ana:- “…Kuma idan kun yi haƙuri kuma kuka yi taƙawa, ƙullinsu bãya cutar ku da kõme. Lalle ne, Allah ga abin da suke aikatãwa Mai kewayewa ne”.

👉🏽 8—Taƙawa na sanya bãwa rashin cutar ƴan uwansa bãyin Allah; kamar yadda Allah (SWT) yake cewa:

📚 {{قَالَتْ إِنِّي أَعُوذُ بِالرَّحْمَنِ مِنْكَ إِنْ كُنْتَ تَقِيًّا () قَالَ إِنَّمَا أَنَا رَسُولُ رَبِّك}} مريم: ١٨ - ١٩

📚 Ma’ana:- “Ta ce, “Lalle ni, ina neman tsari ga Mai rahama daga gare ka, idan ka kasance mai tsõron addini!” () Ya ce, “Abin sani kawai, ni Mnazon Ubangijinki ne…”.

👉🏽 9—Taƙawa na janyo girmama shari’o’in Ubangiji Maɗaukakin Sarki; kamar yadda Allah yake cewa:

📚 {{ذَلِكَ وَمَنْ يُعَظِّمْ شَعَائِرَ اللَّهِ فَإِنَّهَا مِنْ تَقْوَى الْقُلُوب}} الحج: ٣٢

📚 Ma’ana:- “Wancan ne. Kuma wanda ya girmama ibãdõdin Allah, to, lalle ne ita (girmamãwar) tanã daga ayyukan zukãta na ibãda”.

👉🏽 10—Taƙawa na janyõ wa bãwa Allah ya karɓi ayyukansa kyãwãwa, sannan kuma ya yafe masa ayyukansa munãna; kamar yadda Allah (SWT) yake cewa:

📚 {{يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَقُولُوا قَوْلًا سَدِيدًا () يُصْلِحْ لَكُمْ أَعْمَالَكُمْ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُم}} الأحزاب: ٧٠ - ٧٢

📚 Ma’ana:- “Yã ku waɗanda s**a yi imãni! ku bi Allah da taƙawa, kuma ku faɗi magana madaidaiciya () Ya kyautata muku ayyukanku, kuma Ya gãfarta zunubanku…”.

👉🏽 11—Taƙawa na sanya sauƙaƙa murya a inda Manzon Allah (SAW) yake a lõkacin rayuwarsa da ma bãyan wafãtinsa, kai har ma yã yinda ake karanta Hadisansa; kamar yadda Allah (SWT) yake faɗa:

📚 {{إِنَّ الَّذِينَ يَغُضُّونَ أَصْوَاتَهُمْ عِنْدَ رَسُولِ اللَّهِ أُولَئِكَ الَّذِينَ امْتَحَنَ اللَّهُ قُلُوبَهُمْ لِلتَّقْوَى لَهُمْ مَغْفِرَةٌ وَأَجْرٌ عَظِيم}} الحجرات: ٣

📚 Ma’ana:- “Lalle waɗanda ke runtsewar saututtukansu a wurin Manzon Allah, waɗannan ne waɗanda Allah ya jarrabi zukãtansu ga taƙawa. Sunã da wata irin gãfara da ijãra mai girma”.

👉🏽 12—Taƙawa na janyo Allah Ya so bãwansa; kamar yadda Allah (SWT) yake cewa:

📚 {{بَلَى مَنْ أَوْفَى بِعَهْدِهِ وَاتَّقَى فَإِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ الْمُتَّقِينَ}} آل عمران: ٧٦

📚 Ma’ana:- “Na’am! Wanda ya cika alkawarinsa, kuma ya yi taƙawa, to, lalle ne Allah Yana son mãsu taƙawa”.

👉🏽 13—Taƙawa na janyõ wa bãwa sãmun ilimi mai albarka; kamar yadda Allah (SWT) yake cewa:

📚 {{…وَاتَّقُوا اللَّهَ وَيُعَلِّمُكُمُ اللَّهُ وَاللَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيم}} البقرة: ٢٨٢

📚 Ma’ana:- “…Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma Allah Ya sanar da ku. Kuma Allah ga dukkan kõme Masani ne”.

👉🏽 14—Taƙawa na janyõ wa bãwa sãmun rahamar Ubangiji a duniya da kuma lãhira; kamar yadda Allah (SWT) yake cewa:

📚 {{…وَرَحْمَتِي وَسِعَتْ كُلَّ شَيْءٍ فَسَأَكْتُبُهَا لِلَّذِينَ يَتَّقُونَ وَيُؤْتُونَ الزَّكَاةَ وَالَّذِينَ هُمْ بِآيَاتِنَا يُؤْمِنُون}} الأعراف: ١٥٦

📚 Ma’ana:- “…kuma rahamaTa, ta yalwaci dukkan kõme. Sa’an nan zã Ni rubutã ta ga waɗanda suke yin taƙawa, kuma sunã bãyar da zakka, da waɗanda suke, game da ãyõyinMu muminai ne”.

👉🏽 15—Taƙawa na janyõ wa bãwa rashin tawayar lãdan ayyukansa a duniya da lãhira; kamar yadda Allah (SWT) yake cewa:

📚 {{…إِنَّهُ مَنْ يَتَّقِ وَيَصْبِرْ فَإِنَّ اللَّهَ لَا يُضِيعُ أَجْرَ الْمُحْسِنِين}} يوسف: ٩٠

📚 Ma’ana:- “…Lalle ne, shi wanda ya bi Allah da taƙawa, kuma ya yi haƙuri, to, lalle ne Allah bã Ya tõzarta lãdar mãsu kyautatãwa”.

📚 16—Taƙawa na janyõ wa bãwa sãmun bushãra a nan duniya da kuma lãhira; kamar yadda Allah (SWT) yake cewa:

📚 {{…الَّذِينَ آمَنُوا وَكَانُوا يَتَّقُونَ () لَهُمُ الْبُشْرَى فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَفِي الْآخِرَة}} يونس: ٦٣ - ٦٤

📚 Ma’ana:- “Waɗanda s**a yi imãni kuma s**a kasance sunã yin taƙawa () Sunã da bushãra a cikin rãyuwar duniya da ta Lãhira….”.

👉🏽 17—Taƙawa na janyõ wa bãwa sãmun kyakkyãwar shiriya tagari; kamar yadda Allah (SWT) yake faɗa:

📚 {{الم () ذَلِكَ الْكِتَابُ لَا رَيْبَ فِيهِ هُدًى لِلْمُتَّقِين}} البقرة: ١ - ٢

📚 Ma’ana:- “A. L. M. () Wancan ne Littafi, bãbu shakka a cikinsa, shiriya ne ga mãsu taƙawa”.

📚 18—Taƙawa na sanya bãwa ƙin yin zãlunci yãyin wasiyya a lõkacin mutuwa; kamar yadda Allah (SWT) yake cewa:

📚 {{كُتِبَ عَلَيْكُمْ إِذَا حَضَرَ أَحَدَكُمُ الْمَوْتُ إِنْ تَرَكَ خَيْرًا الْوَصِيَّةُ لِلْوَالِدَيْنِ وَالْأَقْرَبِينَ بِالْمَعْرُوفِ حَقًّا عَلَى الْمُتَّقِين}} البقرة: ١٨٠

📚 Ma’ana:- “Kuma an wajabta, a kanku, idan mutuwa ta halarci ɗayanku, idan ya bar wata dukiya, wasiyya dõmin mahaifa da dangi bisa ga abin da aka sani; wajabce a kan mãsu taƙawa”.

👉🏽 19—Taƙawa na sanya bãwa biyan haƙƙin mãtarsa yãyin da rabuwa ta shiga tsakaninsu; kamar yadda Allah (SWT) yake cewa:

📚 {{وَلِلْمُطَلَّقَاتِ مَتَاعٌ بِالْمَعْرُوفِ حَقًّا عَلَى الْمُتَّقِين}} البقرة: ٢٤١

📚 Ma’ana:- “Kuma waɗanda aka saki suna da dãɗaɗãwa gwargwadon hãli, wajabci a kan mãsu taƙawa”.

👉🏽 20—Taƙawa na janyõ wa bãwa makõma tagari mai dãɗi a ƙiyãma; kamar yadda Allah (SWT) yake cewa:

📚 {{هَذَا ذِكْرٌ وَإِنَّ لِلْمُتَّقِينَ لَحُسْنَ مَآب}} ص: ٤٩

📚 Ma’ana:- “Wannan tunãtarwa ce, kuma lalle mãsu bin Allah da taƙawa, suna da kyakkyãwar makõma”.

👉🏽 Da kuma faɗin Allah (SWT):

📚 {{…فَاصْبِرْ إِنَّ الْعَاقِبَةَ لِلْمُتَّقِين}} هود: ٤٩

📚 Ma’ana:- “…Sai ka yi haƙuri. Lalle ne ãƙiba tanã ga mãsu taƙawa”.

✍🏼 Abba Lawan Hassan {Abu Aysha}

KU YAƊA WANNAN ZUWA 'YAN UWA MUSULMA

10/11/2020

Daurawa Fans
DUNIYAR MUTUWA // 08
Rubutawa:- Mal. Adam Abu-Umayrah
(Kada ku mance, Muna kan gabar da Suratul Mulk suke magana da wannan mamaci ne gamed a mafita daga Uqubar da ya shiga a sanadiyar basuss**a da ake bin sa bai biya ba har ya mutu).
Suratul-Mulk ta ce min: Mafita dai dayan abu 3 ne kawai! Na ce mene ne su?
Ta ce:
1: Kodai wanda ke bin ka kudin nan ya yafe maka.
Na ce: ai da yawansu ma sun mance suna bi na bashi, wasu ma basusan da mutuwata ba, wasu qila sun mance ni ma b***e su yafemin, mene ne mafita na gaba?!
Ta ce: 2: Ko kuma magadanka su biya maka bashin. Na ce: yaya magadana za su san da ana bi na bashi ko halin da nake ciki yanzu?
Ni ga shi ban rubuta wata takarda da ke dauke da haqqoqin (bashin) mutane ba b***e su biyamin, domin mutuwa ta zomin ne ba zato, ban shirya mata ba ban kuma kawo ta nan kusa ba!
Ta ce: To yanzu ya rage saura abu 1, zan yi maka qoqarinsa, wata qila ya zama sanadiyar kubutarka, zan gaya maka shi idan na dawo in sha Allah, amma yanzu na tafi! Na ce: Don Allah kar ki tafi, kada ki tafi domin ina jin tsoro da firgici duriya bisa zafin jikina dake qaruwa.
Suratul Mulk ta ce: Ba zan nesa da yawa ba, kuma zan tafi ne don neman mafitarka.
Sai ta tafi, na rage ni kadai cikin baqunci da duhu, damuwa da baqin ciki sun tarun mini, sai na tuna wata addu'a:

"ﻳﺎ ﻣﻦ ﻻ ﻳﺄﻧﺲ ﺑﺄﻧﻴﺲ ﺃﺑﻘﺎﻩ , ﻭﻻ ﻳﺴﺘﻮﺣﺶ ﻣﻦ ﺷﻴﺊ ﺃﻓﻨﺎﻩ , ﻭﻳﺎ ﺃﻧﻴﺲ ﻛﻞ ﻏﺮﻳﺐ , ﺍﺭﺣﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﻘﺒﺮ ﻏﺮﺑﺘﻲ , ﻭ ﻳﺎ ﺛﺎﻥ ﻛﻞ ﻭﺣﻴﺪ , ﺁﻧﺲ ﻓﻲ ﺍﻟﻘﺒﺮ ﻭﺣﺪﺗﻲ"

(Ya Allah wanda baya debe kewa da wani abu don ya bar shi ko ya yi baqunci bisa wani abu da ya qaarar da shi, kuma ya ma'abocin duk wani baqo, ka jiqan baquncina a qabarina, ya na biyun dukkan guda -domin mutum shi 1 ne aqabari-, kadeben kewata cikin qabarina), sai na tuna ashe yanzu ba a duniya nake ba, na riga na wuce gidan aiki, nan ina gidan saka mako ne!
Ban aune ba sai na ji sautin mahaifina mai qaunata, yana cewa: Assalamu alaikum, (sai na amsa masa cikin tsumaye, amma kasshshe bazai ji amsawaata ba)! Na ji yana cewa: Ya Allah ka yafe masa, Ya Allah ka haskaka mashigarsa (qabari), ka debe kewarsa!
Sai na ji shi yana kuka yana cewa: Allah ka kare shi, ya Allah ka shaida ni mai yarda ne agare shi, ya Allah ka yarda da shi! Sai ya wuce! Sai na ga haske ya cika Qabarina bayan duhun da ke ciki san da mahaifina ke mani addu'a, Mala'ikun da ke ciki ba su cemin komai ba har sai da ya wuce, qabarina ya ci gaba da zamowa cikin haske, Mala'ikun nan s**a cemin: Addu'ar Mahaifinka za'a dagata har sama madaukakiya, kuma da sannu Allah zai amsa masa, domin Addu'ar Mahaifa karbabbiya ce!
Kaicona! na so ace Mahaifina bai daina Addu'arsa ba gare ni, yanayin yan da na ji dadinta a qabarina hatta a jikina! Na cewa Mala'ikun: in tambaye ku wani abu? S**a ce: Eh! Na ce: Tun yaushe na rasu? Kuma yanzu qarfe nawa ne? S**a ce: Kwananka 3 da rasuwa yanzu, yanzu kuma lokacin sallar azahar ne!
Na yi mamakin gudun lokaci, yanzu duk wadannan abubuwa a tsawon kwanaki 3 akai kachal? Yanzu duk wannan tsananin duhu da nake gani kafin hasken da ya haska qabarina a dalilin Addu'ar mahaifina, yanzu duk lokacin Azahar ne?
Malaa'ikun s**a ce: Tafiyar da ke gabanka mai tsayi ce, fatanmu Allah ya taimake ka! Na soma kuka mai tsanani wanda ban taba irinsa ba a rayuwata, na ce cikin raina: Tsarki ya tabbata ga Allah! Sau nawa na zamo mai mantuwa game da wannan hali?

08/11/2020

Free Mode See Photos

Facebook logo
Go to Home

You can use data to see photos
See All Photos
Previous Next
Like
React
Comment
Share
Fatawoyin Malaman Sunnah
KYAUTAR BIKIN CHIRISMAS: HALAL KO HARAM?

-Da yawa musulmi suna tambayar shin ya halatta su karbi kyautar kiristoci a ranar kirsemiti, musamman wadanda suke zaune lafiya tare dasu, ko suke aiki a guri daya. Ga bayaninda malamai s**ayi dangane da haka:
1. Ba ya halatta ga musulmi yanuna farincikinsa da wannan ranar, ta hanyar aikawa da gaisuwa ko kyauta ko furanni, ko makamantansu.
2. Ba ya halatta gare shi yaci abinda aka yanka da sunan wannan rana.
3. Ya halatta yakarbi kyautar da zasu bashi a wannan ranar, Kamar yadda ya halatta gare shi yaci abinda za su bashi wadanda ba yankawa akayi ba. Kamar kayan marmari.
Dalili kuwa shine:
A) Baihaqi ya rawaito acikin Littafinsa As-Sunanul Kubra 9/234 cewa, Muhammad Bin Sirin yace: ankawo wa Ali, Allah yakara yarda agare shi, kyautar idin majusawa Nairuz. Sai yace mene wannan kuma? Sai s**ace masa, ya Sarkin Muninai yau ranar idin Nairuz ce. Sai yace, to kullum ma suyi 'Nairuz'. Wato ya karba, tare nuna yaji dadin kyautar.
B) Ibn Abi Shaibah acikin littafinsa Al-Musannaf 5/126 daga Sahabin nan Abu Barzata Al-A
slamy cewa: yana da makwabta majusawa, kuma a duk ranar bukukuwansu suna aiko masa da kyaututtuka gidansa, Sai yakan cewa iyalinsa, yaya abin yake?; idan kayan marmari ne to kuci, wanda kuma ba kayan marmari bane, to kumayar musu kayansu.
C) Haka kuma ya rawaito 5/126 cewa, wata mata ta tambayi Nana A'isha tace, muna tare da mata majusawa masu sana'ar shayar da jarirai, to duk ranar idinsu suna aiko mana da kyauta. Sai A'isha, Allah yakara yarda a gareta tace mata, abinda aka yanka domin wannan ranar kada kuci. Kuci kayan marmari na itatuwa.
Ibn Taimiyya yace, wannan ya nuna idinsu ba shi da wani tasiri wajen yahana akarbi kyautarsu. Karbar kyautarsu a ranar da ba idin ba duk hukuncin daya ne domin wannan ba shine taimaka musu ba akan aikinsu na kafirci.
Duba Littafinsa Iqtidha' Siradil Mustaqim 2/52
Sannan akarshe yana dakyau mufahimci cewa, Ba ya halatta musulmi ya taimaka da yi musu yanka a wannan ranar.
Kuma koda musulmi ne ya yanka musu baza a ci ba.

Allah Kashiryar damu tafarkinka madaidaici, kowa yataimaka wajen yada wannan sako a matsayin nasa gudunmawar.
Dec 3, 2015 · Public · in Timeline Photos
View Full Size · Send as Message · Find support or report photo
LikeLoveHahaMuhd Marzuk Abdullahi and 3.1K others
Write a comment...
·
Dady Waziri
Yakamata malan yakawo inda aka hana musulmi yayi musu yanka kuma koda musulmi ne yayi musu yanka baza'aci ba. Yakamata malan yakawo nassi akan wannan ko ijma'i na malamai. Mungode Allah yakara ma malan lafiya
1 · Like · React · Reply · More · Dec 20, 2017
يوسف عبدالله
Allah yasaka da alkhairi
Like · React · Reply · More · Dec 24, 2017
Abubakar Sadiq
Bali dai
Like · React · Reply · More · Dec 18, 2016
Abubakar Sadiq
Halamun yan shi'a ne wanna
Like · React · Reply · More · Dec 18, 2016
Nasiru Muhammed Ambursa
Ba tambaya zakayiba malam maganar ilmice babu masu hikima sunce saidai idon akwai wata hujja to muganta amma kamar yadda malan ya kawo hujja tare da hadisai da manzo koma sahabai ko kayi shuru abinka banda s**a idonko kayi s**a to munganeka.
1 · Like · React · Reply · More · Dec 27, 2017
Richard Adumu Brown
allah yasakawa malam da alkairi
Like · React · Reply · More · Dec 17, 2015
Prince Fabian Ezenwata
Who cares?. Their greediness will not allow them reject the christmas meat. They have taken over my house waiting for christmas goat meat. Please my brethren obey what you preach. NO HYPOCRISY.
Like · React · Reply · More · Dec 26, 2017
Muhammad Noory Ibraheem II
Amma Ya Shaikh,sai inga kyautar basu bada ta ga musulmi ba sai a wannan rana,niyyar nike duba ya Shaikh,kamar yanda kyautarsu ta hakanan itama niyyarta daban,duk da cewa ba wani Nafsi Qarara na daga Aya ko Hadisi dayake nuna a kar6an. Allaah ya taimaki Shaikh.
Like · React · Reply · More · Dec 21, 2016
Isah Rabe Kambarawa
Allah Ya karba, amin
Like · React · Reply · More · Dec 11, 2015
Jibrin Abdullahi
Zuwa ga malam sani rijiyar lemo. Ni banji hujja daga alkurani kokuma bakin annabi ba a cikin baya nan ka. Hadisai da dama sunzo munji yadda manzon Allah (SAW) yayi zaman lafiya da makwabtan sa, har ya kan ziyarce su da sauransu. Kuma da yawan su s**an sayo nama a wajen mahautan mu ko kuma a zo gida a gyara musu abin da s**a siya don gudanar da BIKIN ranar da take da matukar mahimmaci a wajen su. Ta yaya zaman lafiya zai yiwu idan kana mayar musu da abin da s**a yi maka kyauta dashi da sunan ranar farin cikin su, mu kuma an hana mu basu namu? Wai shin yaya annabi isa(Jesus) yake a wajen mu ne? Ana bamu abincin mauludai(inyas,kaulaha d.s.) wasu mutanen daban kuma bakwacewa komai kuma suna yin yanka ne don wannan ranar.....Malam, a duba dai.

10/09/2020

Allah yasa mucika da imani

Address

Moramty Opp 333 Army Barracks
Maiduguri
234

Telephone

09016401313

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sunna zallah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category