18/01/2018
Wani abinda mutane basu cika lura ba shine: Akwai Girman Kai, akwai kuma Girmama Kai. Hakika suna kamanceceniya da juna wajen furuci da kuma yanayi, amma sun yi matukar shan bamban ga mai hankali wanda Hausa ta ishe shi. Girman Kai rawanin tsiya ne, mai shi zaka ga yana hura hanci yana raina mutane a duk lokacin da mu'amala ta hadasu. Mai Girmama Kai shi ne wanda yake kauce ma duk abinda zai zubar masa da girma da kuma kimarsa a wajen al'umma, amma idan mu'amala ta hadaku sai ka gane ashe saukin al'amura gareshi. Allah Ka yaye mana Girman Kai, Ka bamu ikon Girmama kanmu