20/10/2025
Jagoran Gaskiya da Amana Mai Girma Hon. Salihu Adamu Yanga
muna ɗaga murya cikin farin ciki da godiya ga Allah Madaukakin Sarki saboda ni’imar da ya yi mana ta kasancewar Hon. Salihu Adamu Yanga a matsayin jagoranmu, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen inganta rayuwar al’umma ta Karamar Hukumar Kwaya Kusar.
Yanga mutum ne mai cike da hangen nesa, tsantsar gaskiya, da jajircewa. A duk lokacin da aka ambaci shugabanci nagari, an ambace shi. Ya tashi da halin tausayi, gaskiya, da kishin ci gaban jama’a. A aikinsa babu son kai, babu nuna bambanci adalci da gaskiya ne ginshiƙin tafiyarsa.
Allah Ubangiji Ya ƙara maka lafiya da nisan kwana. Ya ƙara maka nutsuwa da ƙarfin guiwa wajen cigaba da gudanar da jagoranci na gaskiya da amana. Ubangiji Ya ba ka albarkar da ba ta ƙarewa, Ya sa albarka cikin iyalinka da duk al’amuranka.
Tabbas, addu’ar iyaye da al’umma tana da tasiri matuƙa, kuma wannan bawan Allah yana cikin waɗanda addu’ar jama’a ke bi da rahma da kariya. Muna addu’a Allah Ya ci gaba da kare ka daga dukkan sharri, Ya tsare gabanka, bayanka, dama da hagunka.
Daga lokacin da Hon. Yanga ya hau kujerar jagoranci, al’amuran Karamar Hukumar Kwaya Kusar sun canza zuwa hanya mai kyau. Ya kafa misali na shugaba mai hangen nesa, mai son cigaba, wanda ba ya gajiya da taimakon jama’a. Kowane ɗan ƙasa ya san an samu sauyi, kuma an samu shugaba mai gaskiya da amana.
Hon. Salihu Adamu Yanga Jagora wanda yake da zuciya mai taushi, mai sauraron jama’a, mai mutunta kowa da kowa, kuma mai ɗaukar nauyin al’umma kamar yadda uba ke ɗaukar nauyin ’ya’yansa.
A yau muna fatan alheri da nasara gare ka. Allah Ya ci gaba da ba ka hikima, basira, da ƙarfin zuciya wajen jagorantar al’umma cikin gaskiya da adalci.
Muna fatan ganin ci gaba mai ɗorewa a ƙarƙashin jagorancinka, da Allah Ya sanya sunanka cikin jerin shugabanni nagari da za a riƙa tunawa da su da alfahari.
Jagoran Gaskiya da Amana Hon. Salihu Adamu Yanga, mu a Kwaya Kusar muna alfahari da kai!
Allah Ya kara maka lafiya, nisan kwana, da albarka mara iyaka.
Sign Y-R-T
Yanga Reporters team
20/October/2025