05/06/2025
BUKIN BABBAR SALLAH (2025) A MASARAUTAR KAURA NAMODA
ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH
SANARWA TA MUSAMMAN DAGA MASARAUTAR KAURA NAMODA DAKE JIHAR ZAMFARA NIGERIA
Amadadin Maimartaba Sarkin Kiyawan Kaura Namoda HRH Major ((Dr) Sanusi Mohammed Ahmad Asha (Rtd) FCNA MPhil, ya umurceni dana gayyaci dukkan Al’ummar Masarautar Kaura Namoda da kewaye da kuma dukkan sauran jama’a ciki da wajen Jahar Zamfara zuwa wajen Gagarumin Bukin Babbar Sallah Eid al- Kabir 2025/1446 AH na Masarautar Kaura Namoda wanda yashirya kamar haka:
Ranar Farko (Day 1): Hawan Sallah.
Rana: Friday 6th June, 2025
Wuri: Fadar Mai Martaba Sarkin Kiyawa.
Lokaci: 8:00AM
Rana ta Biyu (Day 2): Hawan Sarki.
Rana: Saturday 7th June, 2025.
Wuri: Daga Gidan Maimartaba Sarkin Kiyawa zuwa Fada.
Lokaci: 4:30PM
Rana ta Uku (Day 3): Hawan Daba.
Rana: Sunday 8th June, 2025.
Wuri: Fadar Maimartaba Sarkin Kiyawa.
Lokaci: 11:00AM
Rana ta Hudu (Day 4): Bajakoli da Al’adunmu.
Rana: Monday 9th June, 2025.
Za’a gudanarda wasanni kamar haka: Wasan Kwaikwayo, Bajakolin Masu Maganin Gargajiya, Mawakan Masarauta, Wasar Langa, Wasar Jan Igiya da Yan Dabin Gogarma, Bajakolin kayan Noma da sauransu.
Wuri: Kaura Namoda Stadium
Lokaci: 4:30PM
Rana ta Biyar ( Day 5): Wasar Sukuwa Tseren Dawaki.
Rana: Tuesday 10th June, 2025.
Wuri: Kaura Namoda Stadium
Lokaci : 4:30PM
Allah yabada ikon zuwa ayi buki lafiya kuma a kare lafiya amin summa amin.
Sanarwa daga Alh. Salisu Abubakar Magatakardan Kaura Namoda. Sakataren Masarautar
Kaura Namoda
Jihar Zamfara.