Jihar Katsina A Yau

Jihar Katsina A Yau An Samar da wannan Jaridarne domin baku ingatattu Kuma sahihan labaru na gida dana kasashen ketare. Fede Gaskiya shine taken mu

Domin gudanar da aikin cikin girmama, tare da hada kan al'umar mu.

Ashiru Nagoma Lokacin da Yake Darakta Yaci Zarafin Mutane Ya Wulakanta Mutane Wasu ma Sun bayyana abubuwan da Yayiwa Mut...
08/06/2026

Ashiru Nagoma Lokacin da Yake Darakta
Yaci Zarafin Mutane Ya Wulakanta Mutane Wasu ma Sun bayyana abubuwan da Yayiwa Mutane ne Suke Bibiyarsa Har takai ga Ya Zauce Ya Samu Matsalar Kwakwalwa Cewar Jarumi Umar Baana

~ Manyan Matan Kannywod ✍️

Ba za mu taɓa saurarawa ƴanbindiga ba - Tinubu Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamn...
08/06/2026

Ba za mu taɓa saurarawa ƴanbindiga ba - Tinubu

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta ƙara ƙaimi wajen rage matsin tattalin arziki da jama’a ke fuskanta, tare da ci gaba da yaƙi da matsalolin tsaro da kuma tabbatar da kuɓutar da mutanen da ke hannun masu garkuwa da mutane.

An bayyana wannan saƙo ne ta bakin Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, a wajen taron addu’ar haɗin gwiwar majami’u da aka gudanar a Abuja domin bikin Ranar Dimokuraɗiyya ta 2026.

Akume ya taya ‘yan Najeriya murnar cika shekaru 27 na mulkin dimokuraɗiyya ba tare da katsewa ba tun daga shekarar 1999, yana mai yabawa jaruman gwagwarmayar ranar 12 ga Yuni da s**a sadaukar da rayuwarsu wajen dawo da mulkin dimokuraɗiyya.

Ya amince da cewa matsalolin tsaro, garkuwa da mutane da kuma ƙaura daga muhallai na ci gaba da addabar al’umma, amma ya ce gwamnati tana sane da waɗannan ƙalubale kuma tana ɗaukar matakan magance su.

Dangane da tsaro, ya jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin jama’a na ci gaba da kasancewa babban fifiko ga gwamnatin tarayya, yana mai cewa gwamnati ba za ta miƙa wuya ga ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga ko masu aikata laifuka ba.

Akume ya kuma yi kira ga matasa da su guji shiga harkokin daba, tashin hankali na siyasa, yaɗa ƙarya, ƙiyayyar ƙabila da rashin haƙuri na addini yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027.

Ya bukaci shugabannin addinai, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin farar hula da kafafen yaɗa labarai su ci gaba da inganta zaman lafiya, haƙuri da haɗin kai domin ƙarfafa dimokuraɗiyya da zaman lafiyar ƙasa.

Zaben Gwaji: Wace Jam'iyya Ce, Zaka Zaba?1. ADC2. APC
30/03/2026

Zaben Gwaji: Wace Jam'iyya Ce, Zaka Zaba?
1. ADC
2. APC

Da ɗumi-ɗumi: Tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi ya sauka a jihar kano domin tarbar Sen Rabi'u Musa Kwankwaso zu...
30/03/2026

Da ɗumi-ɗumi: Tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi ya sauka a jihar kano domin tarbar Sen Rabi'u Musa Kwankwaso zuwa jam’iyyar ADC.

YANZU-YANZU: Gwamna Zulum Ya Sauke Kwamishinoninsa Baki Daya
30/03/2026

YANZU-YANZU: Gwamna Zulum Ya Sauke Kwamishinoninsa Baki Daya

Cibiyar Yusuf Bala Usman na Gabatar da Sakamakon Bincike kan Mulkin Ƙasa da TsaroCibiyar Yusuf Bala Usman na ci gaba da ...
30/03/2026

Cibiyar Yusuf Bala Usman na Gabatar da Sakamakon Bincike kan Mulkin Ƙasa da Tsaro

Cibiyar Yusuf Bala Usman na ci gaba da gabatar da sakamakon binciken da ta gudanar kan harkokin mulkin ƙasa, muhalli da matsalar tsaro a wasu jihohin Arewacin Najeriya.

Binciken ya shafi jihohin Bauchi, Jigawa, Katsina da Kaduna, inda aka mayar da hankali kan gano ƙalubale da kuma nemo hanyoyin magance su.

Ana gudanar da taron ne a yau Litinin, 30 ga Maris, 2026, a Otal ɗin Alhujrat da ke Katsina.

Yadda Turawa Masu Yawon Bude Ido S**a Zo Kallon Hawan Mai Martaba Sarkin Gombe
30/03/2026

Yadda Turawa Masu Yawon Bude Ido S**a Zo Kallon Hawan Mai Martaba Sarkin Gombe

INDA RANKA: An yanke mata hukuncin daurin shekaru 6 a gidan yari bayan ta ƙi auren wanda ya tallafa mata a karatunta.Wat...
30/03/2026

INDA RANKA: An yanke mata hukuncin daurin shekaru 6 a gidan yari bayan ta ƙi auren wanda ya tallafa mata a karatunta.

Wata matashiyar budurwa ‘yar kasar Uganda mai suna Fortunate Kyarikunda, an ba da rahoton cewa an yanke mata hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bayan ta ƙi auren wani ɗan kasuwa da ya tallafa mata a karatunta.

Bisa ga rahoton, su biyun sun fara soyayya ne a shekarar 2015.

Daga baya kuma a shekarar 2018, sun amince za su yi aure, inda sai mutumin ya ɗauki cikakken nauyin kuɗaɗen karatunta da kuma rayuwarta.

Sai dai a shekarar 2026, matar ta ƙi neman auren nasa. Sai ɗan kasuwan ya kai ƙarar ta a kotu.

Bayan kotun Rukungiri ta yi nazari kan shari’ar da kuma nazarin shaidun da aka gabatar, sai ta same ta da laifi kuma ta yanke mata hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari, saboda mutumin ya tallafa mata har tsawon shekaru sama da goma har sai da ta kammala karatunta.

Me kuke tunani Idan haka ta fara Faruwa a Nigeria?INDA RANKA: An yanke mata hukuncin daurin shekaru 6 a gidan yari bayan ta ƙi auren wanda ya tallafa mata a karatunta.

Wata matashiyar budurwa ‘yar kasar Uganda mai suna Fortunate Kyarikunda, an ba da rahoton cewa an yanke mata hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bayan ta ƙi auren wani ɗan kasuwa da ya tallafa mata a karatunta.

Bisa ga rahoton, su biyun sun fara soyayya ne a shekarar 2015.

Daga baya kuma a shekarar 2018, sun amince za su yi aure, inda sai mutumin ya ɗauki cikakken nauyin kuɗaɗen karatunta da kuma rayuwarta.

Sai dai a shekarar 2026, matar ta ƙi neman auren nasa. Sai ɗan kasuwan ya kai ƙarar ta a kotu.

Bayan kotun Rukungiri ta yi nazari kan shari’ar da kuma nazarin shaidun da aka gabatar, sai ta same ta da laifi kuma ta yanke mata hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari, saboda mutumin ya tallafa mata har tsawon shekaru sama da goma har sai da ta kammala karatunta.

Me kuke tunani Idan haka ta fara Faruwa a Nigeria?

Allahu Akbar Malam Mustapha Elrufai Kenan Yake Kuka A Wajen Jana'izar Kakarsa
30/03/2026

Allahu Akbar Malam Mustapha Elrufai Kenan Yake Kuka A Wajen Jana'izar Kakarsa

YANZU-YANZU: Yusuf Nasiru Gawuna, Tsohon Ɗan Takarar Gomna A Jihar Kano Ya Sanar Da Ficewarsa Daga Jam’iyyar APC  Zuwa A...
30/03/2026

YANZU-YANZU: Yusuf Nasiru Gawuna, Tsohon Ɗan Takarar Gomna A Jihar Kano Ya Sanar Da Ficewarsa Daga Jam’iyyar APC Zuwa ADC A Hukumance

Daga Muhammad Kwairi Waziri

Address

Katsina

Telephone

+2348026616435

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jihar Katsina A Yau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Jihar Katsina A Yau:

Shortcuts

Share