27/04/2026
CONSENSUS: TAKOBI MAI KAIFI BIYU A SIYASAR YAU
Daga
HJIYA SARATU SA’A MSW
(DG MATA ZALLA)
Mece Ce Consensus?
Shi ne tsarin da ‘yan siyasa ke zaune su amince da ɗan takara ɗaya ba tare da an je zaɓen fidda gwani ba. Manufar: A hana rabuwar kai da faɗa.
Amma tambaya a nan ita ce: Shin magani ne ko kuwa cuta ce a ɓoye?
AMFANIN CONSENSUS - IDAN AN YI SHI DA GASKIYA
1. Yana Hana Faɗa da Rarrabuwar Kai
Zaɓen fidda gwani yakan haifar da ƙiyayya. Ɗan’uwa ya zama abokin gaba. Consensus na gaske na iya haɗa kan ‘yan jam’iyya su fuskanci babban zaɓe a dunkule.
2. Yana Adana Kuɗi da Lokaci
Zaɓe yana cin kuɗi sosai. Kuɗin da za a kashe ana yaƙi da juna, a ajiye shi a yi amfani da shi a yaƙi da jam’iyyar hamayya.
3. Yana Kawo Mutum Mai Ƙarfi
Idan shugabanni s**a zauna s**a zaɓo wanda ya fi cancanta da gaske, ba wai wanda ya fi kuɗi ba, to jam’iyya za ta samu ɗan takara mai ƙarfi da ya haɗa kan kowa.
ILLAR CONSENSUS - IDAN AN YI SHI DA SON ZUCIYA
1. Yana Kashe Dimokuradiyya
Dimokuradiyya ma’anarta zaɓi ce. Idan mutane 5 s**a zauna a ɗaki su ce “wannan ne”, to sun hana dubban ‘ya’yan jam’iyya ‘yancin zaɓe. Wannan cin amana ne.
2. Yana Haifar da ‘Yan Tawaye
Mutum ya shirya, ya sayar da kadara, ya yi kamfe, sai a ce “an yi consensus”. Gobe zai fita ya nemi wata jam’iyya. Shi ke nan aka raba jam’iyya biyu.
3. Yana Kawo Shugabanni Marasa Inganci
Sau da yawa ba a yin Consensus don a zaɓo nagari ba. Ana yi ne don a zaɓo wanda shugaba yake so. Sakamako? A samu shugabanni marasa kishin al’umma.
4. Yana Sanya Rashin Amincewa
Idan talaka ya ga an hana shi zaɓe, zai ce “to me zai sa in fito ranar zaɓe?”. Wannan yana kashe ƙwarin guiwar ‘yan ƙasa.
Babban Lura:
Babu laifi a yi Consensus a jam’iyya, sai dai niyyar masu yin shi ce matsalar.
Idan niyya gina jam’iyya ce, zai yi kyau.
Idan niyya murƙushe wasu ce, to zai zama sanadin rugujewar jam’iyya.
Don haka, mu ‘yan siyasa:
Kafin ku ce “Consensus”, ku tambayi kanku:
"Shin muna haɗa kan al’umma ne, ko kuwa muna raba su ne da sunan haɗa kai?"
✍Abubakar Lawal Abbah
(Youngsadik_abba)