23/05/2023
Hukumar NEPCO ta Kasa Reshen Jahar Katsina ta bayarda tallafin IRI na noman SOBO ga 'ya'yan Kungiyar so6on a kananan Hukumomin Mashi da Kaita.
A ranar Lahadin da ta gabata wanda yayi daidai da 28/05/2023 har Ila yau wannan hukuma ta NEPCO reshen Jahar Katsina a karkashin Jagorancin Alh Kabiru Y Sadoh ta kai daukin tallafin iri na dobo ga Manoman sobo na kananan hukumomin Mashi da Kaita kwana daya bayan da ta raba tallafin iri na Ridi ga manoman ridi na Jahar Katsina, wanda tayi tattaki takanas har wadannan kananan Hukumomi guda biyu.
Yayin kaddamar da jawabin Maraba Shugaban Hukumar Alh. Kabiru Y Sadoh ya shaidawa Al'umma cewar a bincike da ya gabata Jahar Katsina ita ce Jaha ta farko kuma mafi inganci da nagarta wajen noman Ridi da kuma sobo a domin hakannema hukumar tasu ta maida hankali gurin ganin an habbaka noman sobo gadan-gadan a Jahar katsina sannan bayan nazari da bincike sai s**aga yadace su tallafawa Manoma da nagartaccen iri wanda yafi kowane kyau domin samun yabanya mai yawa mai amfani, v SDsannan ya tabbatarwa da manoman cewar da a hankali - a hankali zasu cigaba da kawo masu tallafi kala daban - daban don ganin an habbaka noman ridi a Jahar katsin.
A nasa jawabin Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Manoma ta Kasa reshen Jahar Katsina Dr. Imam Umar Nadada ya jawo hankalin manoma musamman na karamar hukumar Mashi da su sani cewar Bincike ya nuna a kaf fadin duniya Sobo na kasarmu ta Najeriya yafi na kowace kasa kyau, sannan kuma Sobon Jahar katsina yafi na kowace Jaha kyau a kasarnan, haka zalika Sobon karamar hukumar Kaita yafi na kowace karamar hukumar kyau ( wanda hakan na nufin a duk duniya Karamar hukumar Kaita sunfi ko ina noma Sobo mai yawa kuma ingantacce hakanne yasa shugaban yaja kunnensu da su zabura su dage don ganin sun rike wannan kambu nasu ba tare da barin wasu sun karbeba.
Daga cikin manyan bakin da s**a halarci taron akwai:
Shugaban karamar hukumar Kaita wanda ya samu wakilci,
Shugaban hukumar NEPCO, reshen Jahar katsina,
Shugaban hukumar KIPDECO,
Shugaban Kungiyar AFAN reshen Jahar Kstsina,
Shugaban Kungiyar sobo na Jahar katsina,
Manyan 'yan kasuwa da s**a hada da Alh Yusuf Gafai Katsina
Sarkin Noman Jibia. da sauran shuwabannin Manoma da manoma na jaha da kanaanan Hukumomi da sauransu..