19/02/2025
Atiku Ne zai farfado da Martabar Najeriya ta dawo cikin hayyacinta, - Youth Awareness
Kungiyar PDP youth awareness karkashin shugabancin Comrd. Ibrahim sabiu kawo ta gano cewa Atiku shine yafi chanchanta ya zama Shugaban kasa a zaben 2027 mai zuwa.
Fitacciyar kungiyar Masu wayar da kan ya'ayan Jam'iyyar PDP na kasa, karkashin shugabancin Comrd. Ibrahim Sabiu Kawo ya bayyana cewa sunyi tattaki zuwa jihohi 7 a halin yanzu, don tattaunawa da al'umma da jin irin koken su akan yan takarkaru da ake bukatar tsayarwa a matakin shugaban kasa.
A cewar shugaban kungiyar Ibrahim Sabiu mafi yawan yan Najeriya a halin da ake ciki suna goyon bayan Atiku ne. Duba da son kawo hadin kan kasa da cigaba a Najeriya.
Musamman tabbatar da tsare-tsaren tattalin arziki yadda ya kamata wajen dawo da martbar Najeriya a idon duniya.
Ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a ranar Litinin. Hakazalika Shugaban kungiyar Matasa masu wayar da kan al'umma reshen jihar Kano Comrad
Umar (UDAK) kano state Chairman ya bayyana aniyarsu na ganin Atiku ya kai ga nasara don farfado da Najeriya cikin hayyacinta.