06/01/2026
KATSINA SOCU
Ofishin Kula da Tattara Bayanan Mutane Marasa Ƙarfi na Jihar Katsina - KATSINA SOCU - ya buƙaci ƙananan Hukumomin Kankia, Kusada, Ingawa da Charanchi da su taimaka ga ƙoƙarin da Ofishin ke yi na sauƙaƙa samar da Lambar Shaidar Zama Ɗan-ƙasa NIN ga waɗanda ke ciki da waɗanda za su shiga shirin.
Shugabar Ofishin taJihar Katsina, Hajiya Karima Abdulkarim, ce ta miƙa wannan buƙata ga Shuwagabannin Ƙananan Hukumomin lokacin da ta kai ziyarar wayar da kai a Ƙananan Hukumomin.
Ta buƙaci shuwagabannin, tare da masu riƙe da sarautun gargajiya a yankunan, da su ci gaba da bayar da hadin kai da ya dace domin samun nasarar aikin, tana mai bayyana cewa, nan ba da jimawa ba za a turoJami'an da za su yi rajistar Lambar Shaidar Ɗan Kasa - NIN (Frontline End Partners) a fadin jihar don cika sharuddan samun tallafi a ƙasar nan.
Hajiya Karima Abdulkarim ta ce samar da ƙarin jami'an da za su yi ma mutane rijistar daga ƙananan hukumomin, za ya taimaka wajen shiga lungu da saƙon yankunan, kuma ya sauƙaƙa da gaggauta samar da shaidar NIN ga waɗanda ba su da lambar.
Ta ƙara da cewa, samar da Lambar Shaidar Ɗan Ƙasar, za ya taimaka wajen bambancewa tsakankanin mutane da kuma ƙara sahihancin Kundin Mutane Masu Ƙaramin Ƙarfi.
Shugabar ta ce Ofishin wanda ke ƙarƙashin kulawar Ma’aikatar Tsare-tsaren Kasafin Kudi da Tattalin Arziki ta Jihar Katsina, za ya gudanar da aikin faɗaɗa Kundin, bisa tallafin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ta hanyar Shirin Samar da Tallafi na KT-CARES.
A jawabinsa,Jami'i Mai Kula da Sashen Ingancin Aiki, Malam Tukur Ibrahim, ya ce ana gudanar da ayyukan ne kyauta, kuma yanzu haka, ana gudanar da aikin sabunta Kundin Bayanan Mutane Masu Ƙaramin Ƙarfi (Social Register Update) kuma ba da jimawa ba, za a fara aikin faɗaɗa Kundin, don shigar da waɗanda ba su cikin shirin.
A nasu jawaban, Shugaban Ƙaramar Hukumar Kankia, wanda Dakatan Ilimi da Bunƙasa Rayuwar Al'umma, Garba Sani Mawashi ya wakilta, ya jaddada muhimmancin sabunta Kundin Rijistar, wanda a cewar sa, hakan zai amfanar da al'umma da dama musamman waɗanda ibtila'in ambaliyar ruwa ya shafa a yankin.
Kankiyan Katsina, Alhaji Musa Hassan Sada wanda Alhaji Surajo Kauyen Maina ya wakilta, ya sha alwashin bayar da goyon bayan samun nasarar shirin, kuma ya yi kira ga al'ummar yankin da su fito ƙwansu da kwarkwata don yin wannan rijista.
Su ma Shuwagabannin Ƙananan Hukumomin Ingawa, wanda mataimakinsa, Alhaji Abdul-Aziz Abfu Yandoma ya wakilta, da na Kusada, Malam Sani Aliyu Dangamo, da na Charanchi, Alhaji Ibrahim Sani Koda, sun sha alwashin samar da ƙarin jami'ai da za su samar da Shaidar ɗan ƙasar kafin zuwan sauran jami'an da za a turo a yankunan nasu.