ABBA 4+4

ABBA 4+4 Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from ABBA 4+4, Political Party, Kano.

21/02/2026

I accepted 2 fan badges from Kano State Hospital Management Board Reporters-SSR/SR and Hon. Mahmoud Tajo Gaya.

Alhamdulillah we made it
21/02/2026

Alhamdulillah we made it

Mun ziyarci ƙaramar hukumar Garko, inda Mai Girma Kwamishinan Ma’aikatar Ƙasa da Safayo, Alhaji Abduljabbar Umar Garko, ...
10/02/2026

Mun ziyarci ƙaramar hukumar Garko, inda Mai Girma Kwamishinan Ma’aikatar Ƙasa da Safayo, Alhaji Abduljabbar Umar Garko, ya rabawa mata da matasa ƴan gwagwarmaya babura guda 100 tare da jari, bisa sahalewar Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf.

Wannan tallafi wata shaida ce ta ƙudurin wannan gwamnati na ƙarfafa tattalin arzikin al’umma, musamman mata da matasa, domin su dogara da kansu su kuma bayar da gudummawa wajen bunƙasa ci gaban jiharmu.

Ina taya al’ummar Garko murna tare da addu’ar Allah Ya sanya alheri da ɗorewa a cikin wannan tallafi. Ga waɗanda ba su samu ba a wannan karon, muna ƙarfafa musu gwiwa da fatan cewa a nan gaba suma za su amfana, domin manufar wannan gwamnati ita ce kowa ya ci moriya ta wani ɓangare.

Dr. Dahir M. Hashim
Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi
Jihar Kano
ABBA 4+4
Gida-Gida Tv

Gwamnan Jihar Kano Ya Kai Ziyarar Ba-Zata Gidan Hon. AA Zaura Domin Taya Shi Murnar Ranar HaihuwaMai Girma Gwamnan Jihar...
08/02/2026

Gwamnan Jihar Kano Ya Kai Ziyarar Ba-Zata Gidan Hon. AA Zaura Domin Taya Shi Murnar Ranar Haihuwa

Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alh Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyara ta ba-zata zuwa gidan Hon. Abdulsalam Abdulkarim (AA Zaura), domin taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa, a wani mataki da ke nuna ƙarfin zumunci da girmamawa tsakanin manyan jiga-jigan siyasar Jihar Kano.

Ziyarar ta gudana ne cikin daren ranar, a daidai lokacin da Hon. AA Zaura ke murnar shiga sabuwar shekara a rayuwarsa, inda gwamnan ya kai wannan ziyara a matsayin ta sada zumunci, ba tare da wani tsari na hukuma ba.

A yayin ziyarar, Gwamnan Jihar Kano Alh Abba Kabir Yusuf ya taya Hon. AA Zaura murnar cikar sa shekaru 49 a duniya, tare da yi masa fatan ƙarin lafiya, tsawon rai, albarka da nasara a dukkan harkokin rayuwarsa, musamman a fagen hidimar jama’a da siyasa.

Majiyoyi na kusa sun bayyana cewa ziyarar ta nuna irin yadda gwamnatin jihar ke ƙarfafa dangantaka ta mutuntaka da girmama juna tsakanin shugabanni, tare da nuna cewa haɗin kai da fahimtar juna na da muhimmanci wajen gina Kano mai ɗorewa.

Bugu da ƙari, gwamnan Kano ya yaba da rawar da Hon. AA Zaura ke takawa a siyasar Kano, musamman wajen haɗa matasa, tallafa wa ayyukan cigaban al’umma, da bayar da gudunmawa a harkokin raya ƙasa, yana mai jaddada cewa irin wannan haɗin kai tsakanin shugabanni shi ne ginshiƙin samar da kwanciyar hankali da cigaba mai dorewa.

Ziyarar ta kuma kasance wata alama ta ƙarfafa zumunci a tsakanin jiga-jigan siyasa, musamman a daidai lokacin da ake buƙatar haɗin kai da fahimtar juna domin tinkarar ƙalubalen zamantakewa, tattalin arziki da siyasa da ke fuskantar jihar Kano.

Lamarin ya ja hankalin al’umma da dama, inda wasu mazauna unguwar s**a bayyana wannan ziyara a matsayin abin koyi na kyakkyawar alaƙa tsakanin shugabanni, wadda ke gina amincewa tsakanin gwamnati da jama’a.

Ziyarar ta ƙare cikin yanayi na mutunta juna, girmamawa da sada zumunci, ba tare da wani rahoto na tashin hankali ko wata matsala a

With Ungogo Local Government – I just got recognized as one of their top fans!
08/02/2026

With Ungogo Local Government – I just got recognized as one of their top fans!

Ongoing construction of  pedestrian bridge at Northwest University gate, by H.E Alhj. Abba Kabir Yusuf In order to ensur...
08/02/2026

Ongoing construction of pedestrian bridge at Northwest University gate, by H.E Alhj. Abba Kabir Yusuf In order to ensure safety of the students while crossing over.

God bless AKY
.
.

Kuma a Ungogo ga Layin mu nan se a shaida.
08/02/2026

Kuma a Ungogo ga Layin mu nan se a shaida.

THE FIRST GENERAL HOSPITAL CONSTRUCTED IN KUMBOTSO LGA...........Ongoing construction of Kumbotso General Hospital, by H...
08/02/2026

THE FIRST GENERAL HOSPITAL CONSTRUCTED IN KUMBOTSO LGA...........

Ongoing construction of Kumbotso General Hospital, by H.E Alhj Abba Kabir Yusuf
+4YOUTHEPOLITICALVANGURDS
God bless AKY
.
.

Ongoing General Rehabilitation of Government Technical College (GTC) Ungogo. By H.E Alhj. Abba Kabir Yusuf    +4YOUTHEPO...
06/02/2026

Ongoing General Rehabilitation of Government Technical College (GTC) Ungogo. By H.E Alhj. Abba Kabir Yusuf


+4YOUTHEPOLITICALVANGURDS

Shugaban ƙasar Najeriya tare da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Gwamnan jihar Kano, H.E Abba Kabir Yusuf, Tare da...
06/02/2026

Shugaban ƙasar Najeriya tare da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Gwamnan jihar Kano, H.E Abba Kabir Yusuf, Tare da sauran Gwamnoni sun halarci daurin auren Ya’yan karamin ministan tsaron kasar Bello Matawalle a National mosque Dake Abuja.
+4YOUTHEPOLITICALVANGURAD
ABBAKACIKAGWARZO

06 02 2026.

05/02/2026
Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya tattauna da yan Kwangila da ke gudanar da ayyuka daban daban a f...
05/02/2026

Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya tattauna da yan Kwangila da ke gudanar da ayyuka daban daban a fadin kananan Hukumomi 44. An tattauna muhimman batutuwa da s**a shafi gudanar da aiki da kammalawa cikin lokacin da aka yi yarjejeniya, tabbatar da ingancin aiki da sauran su.


+4POLITICAL VANGUARD KANO STATE

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ABBA 4+4 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share