Kabo Reporters

Kabo Reporters Nagartattun Labarai

Sen. Kwankwaso ya Amince da Comr Aminu Abdussalam Gwarzo A matsayin Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar NDCDr Nas...
29/05/2026

Sen. Kwankwaso ya Amince da Comr Aminu Abdussalam Gwarzo A matsayin Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar NDC

Dr Nasiru Gawuna Kuma Dan Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya.

_Saifullahi Hassan

Kwankwaso na shirin ayyana Aminu Abdussalam a matsayin ɗan takarar gwamna na NDC a KanoRahotanni daga majiyoyi masu tush...
28/05/2026

Kwankwaso na shirin ayyana Aminu Abdussalam a matsayin ɗan takarar gwamna na NDC a Kano

Rahotanni daga majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa jagoran Ɗariƙar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na shirin bayyana tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Comrade Aminu Abdussalam, a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a jihar Kano.

A tuna cewa Abdussalam ya yi murabus daga mukaminsa na mataimakin gwamna a watan Maris, makonni kaɗan bayan Majalisar Dokokin Jihar Kano ta aika masa da takardar tsige shi daga mukamin.

Majiyoyi sun shaida wa DAILY NIGERIAN cewa an cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa ta sirri da aka gudanar a tsakanin jiga-jigan tafiyar Kwankwasiyya da abokan siyasa na kusa da Kwankwaso.

Tun da fari dai tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, na daga cikin waɗanda ake ganin su ne na gaba-gaba wajen samun tikitin takarar gwamnan.

Sai dai rahotanni sun ce daga ƙarshe Kwankwaso ya amince da Abdussalam a matsayin wanda zai baiwa takarar.

Rahotannin sun ƙara da cewa Kwankwaso ya yi wa Gawuna tayin kujerar mataimakin gwamna ko kuma tikitin takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, amma ana ganin Gawuna ya ƙi amincewa da tayin tare da jaddada biyayya da ci gaba da aiki domin nasarar jam’iyyar.

Majiyoyi sun ce Gawuna ya shaida wa Kwankwaso cewa ya shiga tafiyar Kwankwasiyya ne ba tare da wani sharadi ba, saboda haka rashin samun tikitin gwamna ba zai sa ya fice daga tafiyar ba.

An kuma rawaito cewa ƙin amincewar Gawuna da tayin ne ya jinkirta sanar da Aminu Abdussalam a hukumance, yayin da wasu masu ruwa da tsaki ke matsa lamba kan a sake duba cancantar Gawuna saboda ƙarfin siyasarsa.

Wasu daga cikin masu goyon bayan Gawuna sun bayyana cewa ya k**ata ɗan takarar da zai fafata da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fito daga Kano ta Tsakiya, kasancewar yankin ne ke da mafi yawan ƙuri’u a jihar.

Sai dai masu goyon bayan Aminu Abdussalam suna ganin tsohon mataimakin gwamnan ya nuna cikakkiyar biyayya, jajircewa da sadaukarwa wajen bunƙasa tafiyar Kwankwasiyya.

Daily Nigerian Hausa

Fubara ya janye takarar sa ne don biyayya ga yarjejeniyar da aka kulla a zaman sulhu - WikeMinistan babban birnin tarayy...
26/05/2026

Fubara ya janye takarar sa ne don biyayya ga yarjejeniyar da aka kulla a zaman sulhu - Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa janyewar gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, daga takarar gwamna a 2027 ya yi daidai da yarjejeniyar sulhun da aka cimma domin dawo da zaman lafiya a jihar.

Wike ya bayyana haka ne bayan duba wasu ayyukan more rayuwa a Abuja, inda ya ce tun farko an cimma matsaya cewa za a dakatar da barazanar tsige Fubara, amma shi kuma ba zai nemi wa’adi na biyu ba.

Fubara dai ya janye daga zaben fidda gwani na jam’iyyar APC, yana mai cewa ya dauki matakin ne domin zaman lafiya, hadin kai da kwanciyar hankali a Rivers bayan tuntuba da iyalansa da magoya bayansa.

Wike ya ce bai yi mamakin matakin ba, yana mai zargin cewa daukar fom din takara tun farko ya saba da yarjejeniyar sulhun da aka cimma bayan rikicin siyasar jihar.

Haka kuma, ya bayyana ɗan majalisar tarayya, Kingsley Chinda, a matsayin wanda ya dace da kujerar gwamna saboda kwarewarsa a bangaren zartarwa da majalisa.

A gefe guda, kungiyar Rivers Professionals ta yaba da fitowar Chinda a matsayin dan takarar APC, tana mai cewa yana da kwarewa da nagartar da za su tabbatar da shugabanci mai adalci da hada kan al’umma a jihar Rivers.

Rikicin siyasar Rivers dai ya samo asali ne daga sabanin da ke tsakanin Wike da magajinsa Fubara kan iko da tsarin siyasar jihar tun bayan hawan Fubara mulki a shekarar 2023.

Daily Nigerian Hausa

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa babu kamshin gaskiya a rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin c...
21/05/2026

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa babu kamshin gaskiya a rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na shirin sauya sunan Najeriya zuwa “United States of Nigeria” tare da soke tsarin Shari’a a jihohin Arewa.

A wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar 21 ga Mayu, 2026, ya ce labarin ƙarya ne da wasu yan siyasa ke yaɗawa domin haddasa rikici da tayar da hankalin jama’a gabanin zaɓen 2027.

Sanarwar ta ce shugaban ƙasa ba shi da wani shiri na tura wata doka mai suna “Project True Federation” zuwa majalisar dokoki kafin babban zaɓe mai zuwa.

Fadar shugaban ƙasar ta kuma bayyana cewa sauya kundin tsarin mulkin ƙasa ba abu ne mai sauƙi ba, domin yana buƙatar amincewar kashi biyu bisa uku na majalisar tarayya da kuma amincewar majalisun jihohi 24.

Sanarwar ta ƙara da cewa shugaban ƙasa Tinubu na mayar da hankali ne wajen aiwatar da gyaran tattalin arziki da samar da ci gaba ga yan Najeriya maimakon shiga batutuwan da za su raba kan al’umma.

YANZU-YANZU: Fubara ya janye neman kujerar Gwamnan Rivers karo na biyuGwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sanar ...
21/05/2026

YANZU-YANZU: Fubara ya janye neman kujerar Gwamnan Rivers karo na biyu

Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sanar da janyewarsa daga zaben fidda gwani na kujerar gwamna na jam’iyyar APC da aka shirya gudanarwa ranar Alhamis.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a daren Laraba, Fubara ya ce ya dauki matakin ne bayan dogon nazari da tuntuba da iyalansa da makusantansa.

Ya bayyana cewa zai mara wa duk wanda ya fito takarar jam’iyyar baya domin tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a jihar.

Fubara ya ce shugabanci yana bukatar sadaukarwa, yana mai cewa akwai lokacin da buri na kai dole ya ba muradun jama’a gaba.

“Jihar Rivers ta fi karfin kowane mutum guda, kuma a wannan lokaci mai muhimmanci, zaman lafiya, kwanciyar hankali da hadin kan jihar su ne ya k**ata su fi kowanne buri muhimmanci,” in ji shi.

Ya kuma gode wa magoya bayansa bisa goyon bayan da s**a ba shi tun daga farkon tafiyar siyasarsa, duk da cewa ya fahimci takaicin da wasu daga cikinsu za su iya ji bayan janyewar tasa.

Fubara ya ce shiru da ya yi a baya-bayan nan ya kasance ne bisa dabarar siyasa da kuma kare muradun jihar.

Har ila yau, ya gode wa jam’iyyar APC bisa damar da ta ba shi tare da nuna godiya ga Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, kan goyon baya da karfafa masa gwiwa.

Gwamnan ya jaddada cewa janyewarsa daga takarar ba alamar tsoro ko gazawa ba ce, illa sadaukarwa domin tabbatar da ci gaban jihar Rivers cikin hadin kai da zaman lafiya.

Ya kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da yi wa al’ummar jihar Rivers hidima har zuwa karshen wa’adinsa.

Daily Nigerian Hausa

Mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata  Barau Jibrin ya ziyarci tsohon minista Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo a...
20/05/2026

Mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibrin ya ziyarci tsohon minista Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo a gidansa da ke Abuja.

Kotu ta bada umarnin kamo dan majalisar tarayya na Kumbotso,  Idris DankawuWata kotun majistare  da ke Bwari a babban bi...
20/05/2026

Kotu ta bada umarnin kamo dan majalisar tarayya na Kumbotso, Idris Dankawu

Wata kotun majistare da ke Bwari a babban birnin tarayya Abuja ta bayar da sammacin k**a dan majalisar wakilai mai wakiltar ƙaramar hukumar Kumbotso a jihar Kano, Hon. Idris Dankawu, bisa zargin damfara wanda hakan ya saba wa sashe na 312 na kundin dokar laifuka( Penal Code).

Kotun tana ba da umarnin kamo dan majalisar ne nbayan wani korafi da kamfanin BAMZ Multi Essential Services ya shigar ta hannun lauyansa, Barrista Ahmad Umar Faroukh, yana neman a kamo dan majalisar saboda kin bayyana a gaban kotu.

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin Dankawu da karbar kudin da s**a kai N77,035,069 ta hannun hadiminsa, Isma’il Yakubu Abubakar, wanda ake zargin ya karbi kudin bisa umarninsa.

A cikin korafin da lauyan mai kara, Barrista Ali Jamilu, ya gabatar, ya bayyana cewa Hon. Dankawu ya tuntubi kamfanin a ranar 18 ga Satumban 2025, inda ya yi alkawarin ba su kwangilar girka fitilu masu amfani da hasken rana da kudinta ya kai N77,035,069.

Lauyan ya ce an tura kudin zuwa asusun hadiminsa, Isma’il Yakubu Abubakar, amma ba a aiwatar da yarjejeniyar ba.

Korafin ya kuma bayyana cewa watanni takwas kafin hakan, Dankawu ya shaida wa kamfanin cewa ya samu kwangilar mazaba ta sany fitilun hasken rana kan tituna da kudinta ya kai N770,000,000, inda ya bukaci a biya kaso 10 cikin 100 na kudin kwangilar, wato N77,000,000, kafin a bayar da takardar kwangilar.

An ce an biya kudin ne a ranar 2 ga Oktoban 2025 zuwa asusun Access Bank na hadiminsa.

Sai dai bayan sama da watanni bakwai, ana zargin dan majalisar da hadimansa sun kasa bayar da kwangilar, suna ta bayar da dalilai mabambanta.

Lauyan mai kara ya kara da cewa bincike ya nuna babu wata irin kwangilar da aka bayar, kuma babu wata hujjar kashe kudin da za ta tabbatar da karbar kudaden.

An yi kokarin tuntubar Hon. Dankawu ko hadiminsa ya ci tura, domin wayoyinsu ba sa shiga.

Daily Nigerian Hausa

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta k**a tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman.An k**a Mamman ne a ya...
19/05/2026

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta k**a tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman.

An k**a Mamman ne a yankin Rigasa da ke jihar Kaduna da safiyar Talata 19 ga watan Mayu, 2026 bayan makonni ana sa ido da tattara bayanan sirri a kansa daga jami’an hukumar.

Da yake jawabi ga manema labarai, shugaban EFCC, Ola Olukoyede ya ce tsohon ministan ya ɓuya ne bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta same shi da laifin karkatar da kuɗaɗen ayyukan lantarki.

Ya ce a ranar 7 ga Mayu, 2026, Mai shari’a James Omotosho ya same shi da laifi a kan tuhume-tuhume guda 12 da s**a shafi karkatar da kuɗaɗen ayyukan lantarki na Zungeru da Mambilla.

Olukoyede ya ce kotun ta yanke hukuncin ne ko da babu Mamman a gabanta bayan EFCC ta tabbatar da hujjojinta ba tare da wata shakka ba.

Radio

Samun takarar mataimakin shugaban kasa da na yi a NDC zai buɗe kofar Kano ta samar da shugaban ƙasa nan gaba - Kwankwaso...
19/05/2026

Samun takarar mataimakin shugaban kasa da na yi a NDC zai buɗe kofar Kano ta samar da shugaban ƙasa nan gaba - Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa ya na da kwarin gwiwar samun tikitin takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar, ya na mai cewa hakan zai iya bude hanya ga jihar Kano ta samar da shugaban kasa a nan gaba.

Tsohon gwamnan Kano ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi kai tsaye da gidajen rediyo daban-daban a karshen mako a Kano.

Kwankwaso da Peter Obi, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben 2023, sun koma jam’iyyar NDC daga ADC a farkon wannan wata.

Rahotanni sun nuna cewa Obi da Kwankwaso sun amince su shiga NDC ne da sharadin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 a karkashin tikitin hadaka, inda ake sa ran tsohon gwamnan Anambran zai tsaya takarar shugaban kasa, yayin da tsohon ministan tsaro zai zama abokin takararsa.

Kwankwaso ya yi nuni da cewa idan aka zabi Peter Obi a matsayin shugaban kasa a 2027 kuma shi ya zama mataimakin shugaban kasa, hakan zai ba shi damar maye gurbin Obi a shekarar 2031.

An yi jana'izar mutum biyu da yan bindiga s**a kashe a yankin Lakwaya da ke karamar hukumar Gwarzo a jihar Kano.Harin da...
15/05/2026

An yi jana'izar mutum biyu da yan bindiga s**a kashe a yankin Lakwaya da ke karamar hukumar Gwarzo a jihar Kano.

Harin dai ya faru ne jiya Alhamis a unguwannin Zurun Mahauta da Jajaye, inda maharan s**a buɗe wuta kan mutane, abinda ya jefa mazauna yankin cikin firgici.

📷 premier radio

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kabo Reporters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share