Atiku Alkhairiyya Charity Foundation

Atiku Alkhairiyya Charity Foundation The Mission of this foundation is to provide the youths with skill acquisition and empower them

28/12/2022

Yau kenan, yayin da Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kano take karbar Daruruwan Kungiyoyi matasa na jihar da kewaye domin yin aiki dasu Kafa da Kafa domin tabbatar da Nasarar Alh. Atiku Abubakar a Kasa, da kuma Dan takarar Gwamnan Jihar Kano Hon. Sadiq Aminu Wali a kakar zabe ta 2023.

Inda Jagoran Kungiyar Atiku Alkhairiyya Charity Foundation wato, Bin Abdulrahman yayi Jawabin Maraba, tare da fatan samun Nasara.

Allah ya tabbatar mana da Nasara

A yau 11-10-2022 Tsohon ministan harkokin waje na Najeriya, kuma tsohon Jakadan Nijeriya a China, sannan Mahaifi ga dan ...
11/10/2022

A yau 11-10-2022 Tsohon ministan harkokin waje na Najeriya, kuma tsohon Jakadan Nijeriya a China, sannan Mahaifi ga dan takarar Gwamnan Kano a kakar zabe mai zuwa ta 2023 karkashin tutar Jam’iyyar PDP, Ambassador Aminu Wali ya kawo ziyarar kafa da kafa shida mukarrabansa izuwa babban ofishin Atiku Alkairiyya.

Ya samu tarba ta musamman daga Jagoran kungiyar Alh. Bin Abdulrahman inda s**a tattauna dabaru da kuma muhimman abubuwa dan gani an samu nasarar lashe zaben shugaban kasa na Wazirin Adamawa Alh. Atiku Abubakar, Gwamna Alh. Sadik Aminu Wali da kuma ‘yan majalissu duk a karkashin tutar Jam’iyyar PDP.

09/10/2022

Idan Rana Ta Fito Part III - Khadeejah Bauchi

02/10/2022

Idan Rana Ta Fito Part II - Khadeejah Bauchi

25/09/2022

Idan Rana Ta fito Part I - Khadeejah Bauchi

19/09/2022

Karkashin jagorancin da kuma shugaban Alh. Bin Abdulrahman kungiyar Atiku Alkairiyya ta Kaddamar da Coordinator na farko a jihar Borno Alh. BabaGoni Dubai

14/09/2022

A ranar Lahadi wadda tayi daidai da 18-09-2022, kungiyar Atiku Alkairiyya zata kai ziyara jihar Borno domin kaddamar da Coordinator ta na jihar.

Bayan haka shugaban kungiyar Alh Bin Abdulrahman zai gudanar da taron malamai guda 1000 domin saukar karatun Al-Qur’ani mai girma kuma za’ayi tuwassali da Saukar ne domin samun nasarar Alh Atiku Abubakar (Wazirin Adamawa) a zaben shugabancin kasa na 2023.

, ,

03/09/2022

SAKON BAN GAJIYA...

Yadda kungiyar Atiku Alkairiyya Charity Foundation Karkashin jagorancin Alh. Bin Abdulrahman ta tarbi Dan Takarar Shugabancin Kasar Najeriya a Karkashin Tutar Jam’iyyar PDP Alh. Atiku Abubakar (Wazirin Adamawa) a yayin ziyarar da ya kawo jihar Kano dake Arewacin Najeriya.

A madadin Jagoran Kungiyar nan mai albarka muna mika sakon ban gajiya ga dan takarar shugaban kasa, mukarraban da s**a rakoshi, shugabannin kungiya AACF, mambobin kungiyar AACF, kungiyar malamai da daliban jihar kano, Yan Adaidaita sahu jihar kano, kungiyar kaurayen jihar kano, kungiyar matasan jihar kano da sauran kungiyoyi.

Dafatan kowa ya koma gida lafiya. Kuma Allah ya bawa Alh Atiku Abubakar shugabancin kasa a zaben 2023.

27/08/2022

Kungiyar Atiku Alkairiyya karkashin Jagorancin Alh. Bin Abdulrahman na yiwa Wazirin Adamawa Alh. Atiku Abubakar barka da zuwa jihar Kano.

SHUGABAN KUNGIYAR ATIKU ALKHAIRIYYA YA GANA DA SABBIN EXCOS NA MUTUM 25 NA SHIYYOYI 3 (KANO TA AREWA,KANO TA KUDU DA KUM...
07/08/2022

SHUGABAN KUNGIYAR ATIKU ALKHAIRIYYA YA GANA DA SABBIN EXCOS NA MUTUM 25 NA SHIYYOYI 3 (KANO TA AREWA,KANO TA KUDU DA KUMA KANO TA TSAKIYA) DAKE JIHAR KANO.

A cikin Shirye-shiryen kungiyar na ganin Alh Atiku Abubakar ya samu nasara, Shugaban kungiyar Atiku Alkhairiyya Alh. Bin Abdulrahman ya karbi bakuncin sababbin excos din kungiyar na mutum 25 daga yankunan Kudu, 25 daga yankunan Arewa da 25 daga yankunan tsakiyar jihar Kano a ofishin sa a jiya.

A yayin taron masu jawabai daga kowane shiyyoyi ukun sun jaddada goyon bayansu ga burin Alh. Atiku Abubakar ya zama shugaban kasar Najeriya.

Inda s**a shaida masa cewa gwamnatin APC a yanzu ta gaza matuka, wanda hakan ya sa ya zama dole Najeriya ta nemi shugaba mai hangen nesa, tunani da kuma tsare-tsare don kawo wa al’umma ababen more rayuwa da kuma bunkasa kasuwanci.

A nasa martanin, Alh Bin Abdurrahman yace Alh Atiku Abubakar tuni ya fito da tsare-tsare na ceto Najeriya daga kuncin rayuwa da rashin tsaro da ke kawo cikas ga martabar Najeriya.

Yayi Alkawarin yin aiki dasu domin tabbatar da nasarar Atiku Abubakar a kakar zabe ta 2023.

Ya kuma bukaci daukacin Excos da su mika sakon zuwa kananan hukumominsu, domin tunatar da al’umma bukatar su zabi Alh Atiku Abubakar domin cancantar shi a zaben 2023 mai zuwa.

Vote PDP
Vote Alh. Atiku Abubakar
Vote Progress

ATIKU ALKHAIRIYYA 2023 HEAD OFFICE KANO, KANO STATE.
7th August, 2022.

SAKON BARKA DA SALLAH ZUWA GA MUSULMIN DUNIYA — Daga Bakin Jagoran wannan kungiya Alh Bin Abdulrahmanاللَّهُ أَكْبَرُ، ا...
09/07/2022

SAKON BARKA DA SALLAH ZUWA GA MUSULMIN DUNIYA — Daga Bakin Jagoran wannan kungiya Alh Bin Abdulrahman

اللَّهُ أَكْبَرُ، اللَّهُ أَكْبَرُ، اللَّهُ أَكْبَرُ
لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ
اللَّهُ أَكْبَرُ، اللَّهُ أَكْبَرُ
وللَّهِ الحمد

Allah ya karbi sadaukarwar mu, kuma daga rahamar sa yagafarta mana kurakuran mu.
Kamar yadda ya tseratar da rayukan mu don shaida Sallar Idin wannan shekara, Allah ya sa mu kara shaida na shekarun gaba cikin koshin lafiya da wadata.

Sannan muna tawassali da ranar jiya ta Arfa Ubangiji Allah ya bawa kasar mu ta Nigeria zaman lafiya, sannan kuma ya bawa Wazirin Adamawa Alh Atiku Abubakar shugabancin Nigeria a zaben 2023, Sannan ya biya mana bukatun mu duniya da lahira.
Ameen

Eid’l kabir Mubarak!

Address

No 23 Gyadi-Gyadi Zaria Road Opp Gadan Lado. Kano
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Atiku Alkhairiyya Charity Foundation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share