13/07/2024
Kawai ana nema a fake da cewar ana yiwa Malamai rashin kunya don kawae a daqile mutane daga nemawa kansu mafita,
Wallahi idan ba a yabawa Talakan Nigeria ba bai kamata a kushe masa ba, wane irin cin kashi ne Shugabanni basu masa ba amma yayi hakuri, amma daga ambaton zai nema wa kansa mafita anfito ana yaqarsa, meyasa ba zaku yaqi su Shugabannin ba.
Ba fa wani abu muka nema ba, cewa kawai mukayi a bamu dama mu iya cin abinchi, abamu tsaro muyi noma, abamu ilimi mu banbanta da Dabbobi,
Yanzu doAllah a wannan menene lefin mu?
To zanga zanga sai mun fito idan mutum yaga dama ya fitar damu daga Musulunchin.