Tsangayar Masoya Sardaunan KANO

Tsangayar Masoya Sardaunan KANO Akidarmu itace fafutikar samar jagoranci nagari a kowane mataki domin cigaban Al'umna da samar musu da walwala Wannan tafiya ce ta dukkan Masoyin Mal.

Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano a duk inda yake ko duk ko dan Siyasa ko wanda baya Siyasa muna maraba da kowa domin gwagwarmaya ta Samar da Jagoranci Nagari Allah agaza mana.

ALHAMMDULLAHDukkan yabo da godiya sun tabbata ga sarki Allah mai iko da kowa da komai tsira da aminci su kara tabbata ga...
27/05/2023

ALHAMMDULLAH

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga sarki Allah mai iko da kowa da komai tsira da aminci su kara tabbata ga shugaban mu Annabi muhammadu S.A.W.

Komai yayi farko yana da karkashe a yau 27/may / 2023 Allah ya nufa na dawo wannan kafa ta sada zumunta (New Media) bayan daukar dogon hutu Allah ya nufa na dawo zan cigaba daga inda na tsaya.

Ina fatan kowa yana cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali Ameen.

SHAIDAR DA AKA YI WA SHEKARAUSanata Mallam Ibrahim Shekarau shekararsa 67 a duniya. A cikin wannan shekaru ya yi aikin g...
30/06/2022

SHAIDAR DA AKA YI WA SHEKARAU

Sanata Mallam Ibrahim Shekarau shekararsa 67 a duniya. A cikin wannan shekaru ya yi aikin gwamnati da mulki da siyasa da huldar jama'a ta tsawon shekara 42.

A wadannan shekaru 42, an yi masa shaida, kawarara guda goma.

Na Daya: An shaida ya iya aikin da aka dora masa ko na siyasa ko na jagoranci.

Na biyu: an shaida yana da rikon amana da gaskiya da cika alkawari. Baya karbar cin hanci kuma baya bayar wa.

Na uku: Ba a hada baki da shi a yi cuta ko almundahana, sannan ba zai yi maka karya ba. Shi kwar - tu-kwar ne

Na hudu: Yana da nagarta da riko mai tsanani na koyi da dabi'u na kwarai na addini.

Na biyar: A mulki da aikin kungiya yana karbar shawara da gyara da s**a mai kyau. Yana baiwa duk na kasa da shi 'yanci kuma ba ya shayin ya ciccibaka zuwa mataki na gaba.

Na shida: A siyasa yana da hakuri da juriya da tsabar bin ka'ida da doka da yi wa kowa uzuri. Ba ya rigima, amma ba ya daukar wulakanci.

Na bakwai: In an bashi aiki, yana yinsa bilhakki. Duk nauyin da aka dora masa yana sauke shi gwargwadon iko.

Na takwas: Shekarau yana da dattako da girmamawa ga kowa, yana hulda da kowa. A koda yaushe, fuskarsa a sake take, kofarsa a bude take. Hannunsa a yalwace yake.

Na tara: An shaida yana da tausayi da jinkai da kyauta da taimako.

Na goma: Shekarau mai bin tsarine da ka'ida da doka. Dan dimokuradiyya ne. Mai biyayya ne ga shugaba da shugabanci baya raina kowa da baiwar da Allah ya ba shi.

Wanda s**a san shi a harkar aikin gwamnati da wadanda s**a yi mu'amala da shi a mulki da wadanda s**a yi tarayya da shi a siyasa da wadanda s**a taso tare da shi sun ce Shekarau bai canza halinsa ba. Halinsa kenan shekara 42.

Zaka iya zaginsa ko soke shi ko ka zarge shi, ko ya yi maka kuskure tunda mutum ne shi

AMMA

Wannan ita ce shaidar da aka yi wa gwanina. Kun ji gwanina.

A yau ya bayar da sanarwar ficewa daga cikin jam'iyyar APC a zauren majalisar dattijai. Ya koma NNPP mai kayan marmari, kuma an bashi sabuwar kujerar zama a cikin ay

Address

No 8. Mundubawa Gidan Sardaunan Kano
Kano

Telephone

2348031924570

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tsangayar Masoya Sardaunan KANO posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share