Ganduje Media For Tinubu

Ganduje Media For Tinubu Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Ganduje Media For Tinubu, Political organisation, No. 18b Magaji Rumfa, Nassarawa, Kano, Kano.

GODIYA TA MUSAMMAN GA HON. DG BAFFA BABBA DANAGUNDI. DG. TSG  Ba kowace kyauta ce ake aunawa da kuɗi ba; wasu kyaututtuk...
08/09/2026

GODIYA TA MUSAMMAN GA HON. DG BAFFA BABBA DANAGUNDI. DG. TSG

Ba kowace kyauta ce ake aunawa da kuɗi ba; wasu kyaututtukan ana aunawa ne da lokaci, kulawa da mutunta ɗan Adam.

Muna miƙa godiya ta musamman, wadda ba za ta gajiya ba, ga Hon. DG Baffa Babba Danagundi bisa yadda ya turo da wakilansa na musamman har cikin unguwanninmu, domin duba halin ’yan ƙungiyarmu da s**a haɗu da tsautsayi lokacin taron ƙaddamar da TSG a Kano.

Sun zo cikin mutuntawa da karramawa, s**a duba su, s**a yi musu addu’a, tare da ba su tallafin kuɗin magani domin ci gaba da samun kulawa.

Wannan hali na kula da mutum, girmama shi da zuwa kafa-da-kafa domin duba ɗan ƙungiya, ko da kuwa ba shi da wani babban matsayi, ya nuna irin kyakkyawar mu’amalar da Hon. DG yake da ita.

Abin burgewa shi ne, wannan dabi’a ta DG tana da kamanceceniya da salon Baba Ganduje wajen daraja mutane, kusantar jama’a da ganin kowa yana da muhimmanci.

A siyasa, ra’ayoyi kan bambanta, amma kyakkyawar mu’amala tana karya shingen siyasa. Irin wannan hali ne yake sa mutum ya samu ƙarin daraja da ƙauna daga jama’a, har ma wanda ba ya tare da shi a siyasa zai iya cewa: “Wannan mutum ya cancanci goyon baya.”

Allah Ya saka da alheri, Hon. DG Baffa Babba Danagundi. Allah Ya ƙara maka basira, hikima da ikon yi wa jama’a hidima. 🇳🇬

05/09/2026

YAWAN JAMA’A A KADDAMAR DA APC TINUBU SUPPORT GROUP (TSG) YA NUNA CEWA “AJANDAR SABUWAR FATA” TANA AIKI .... BABA GANDUJE

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa dimbin jama’ar da s**a halarci ƙaddamar da Tinubu Support Group 37 Coordination a Jihar Kano, wata babbar shaida ce da ke nuna cewa Ajandar Sabuwar Fata (Renewed Hope Agenda) ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na samun ƙarin karɓuwa da goyon baya a Kano da Najeriya baki ɗaya.

Ganduje ya bayyana Shugaba Tinubu a matsayin jagora mai kishin ci gaba, wanda ke da kyakkyawan hangen nesa da manufa wajen gina Najeriya mai ƙarfi da tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.

Ayyuka, jajircewa da haɗin kan jama’a su ne ginshiƙan samun ci gaba. 🤝

Kano ta nuna matsayinta. Najeriya na ci gaba da tafiya. 🇳🇬

Bajinta, Haƙuri da Sauƙin Kai Alamar Jagoranci! Baba Ganduje 🇳🇬🏅Taron kaddamar da Tinubu Support Groups (TSG) a Kano ƙar...
05/09/2026

Bajinta, Haƙuri da Sauƙin Kai Alamar Jagoranci! Baba Ganduje 🇳🇬🏅

Taron kaddamar da Tinubu Support Groups (TSG) a Kano ƙarƙashin jagorancin Hon. Baffa Babba Danagundi, tare da shigowar wasu fitattun ’yan siyasar adawa, ya sake nuna yadda siyasa ke zama gada ta haɗin kai da nasara.

A matsayina na mai kallon siyasar Kano, ba zan gajiya da yaba Baba Ganduje ba; sauƙin kansa, haƙurinsa, dabararsa da kuma iya bai wa kowa dama su ne daga cikin abubuwan da s**a sa yake iya haɗa mutane tare da jagorantar su zuwa nasara.

Jagora na gari ba ya rufe hanya, yana buɗe hanya ga kowa.

Allah Ya ƙara wa Baba Ganduje basira, lafiya da hikima wajen hidimtawa al’umma. Ya Hayyu Ya Qayyum. 🤲

19/08/2026

Sakon Godiya

A madadin Shugaban Ƙungiyar TTP (Tinubu Transformation Project), Comrd. Rufai Mustapha Daneji, muna miƙa saƙon godiya na musamman ga Alh. Sharu Mahmud Dan Larabawa, Shugaban TTP, da Alh. Hamza Darma, bisa rabon taki da aka yi wa ’yan ƙungiya.

Muna matuƙar godiya da wannan kyakkyawar kulawa da aka nuna wa ’yan ƙungiya. Allah Ya saka da alheri, Ya ƙara ɗaukaka ku, Ya kuma sanya wannan taimako ya zama sanadin ƙarin ci gaba da albarka. Ameen.

Shugaban Ƙungiyar TTP
Comr Rufai Mustapha Daneji

All Blacks

SHUGABA TINUBU YA GANA DA JAGORORIN SIYASAR NIGERIA DOMIN ƘARFAFA HAƊIN KAN JAM'IYYA,Daga Tinubu Transformation ProjectA...
27/07/2026

SHUGABA TINUBU YA GANA DA JAGORORIN SIYASAR NIGERIA DOMIN ƘARFAFA HAƊIN KAN JAM'IYYA,

Daga Tinubu Transformation Project

A wani muhimmin Zama na ƙarfafa haɗin kai da bunƙasa dimokuraɗiyya a Nigeria, jagoran siyasa, Shariff Mahmoud Danlarabawa, ya jagoranci Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Sanata Rufai Hanga, tare da tsohon Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, zuwa Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja domin ganawa da Shugaban Ƙasa kuma Babban Kwamandan Rundunar Sojojin Najeriya, Mai Girma Bola Ahmed Tinubu, GCFR.

Ganawar ta gudana cikin yanayi na fahimtar juna, inda aka tattauna batutuwa masu muhimmanci da s**a shafi ci gaban ƙasa, haɗin kan al'umma, da yadda za a ƙara inganta tafiyar gwamnatin APC.

Bayan kammala taron, an bayyana cewa ganawar ta kasance mai armashi kuma mai amfani, tare da nuna aniyar ci gaba da haɗa kan shugabanni daga sassa daban-daban domin tallafa wa manufofin da za su kawo ci gaba mai ɗorewa ga Najeriya.

Haka kuma, ana kallon irin wannan ganawa a matsayin wani ɓangare na ci gaba da ƙoƙarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tuntuɓa da haɗa kan manyan masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa domin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.

A wani ɓangare kuma, ana ci gaba da yaba wa rawar da Shariff Mahmoud Danlarabawa ke takawa wajen aiwatar da ayyukan da Shugaba Tinubu ke dora masa, ciki har da isar da saƙonni da gudanar da muhimman tuntuba da manyan shugabannin ƙasa, ciki har da ziyarar da Shugaban Ƙasa ya aike shi zuwa wajen tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, a matsayin wani yunƙuri na ƙarfafa haɗin kai da ci gaba da gina Najeriya mai cike da zaman lafiya da ci gaba.


Comr Rufai Mustapha Daneji
All Blacks

18/07/2026

Jawabin Baba Ganduje, wajen taron addu'a da musuluntar da maguzawa 373 zuwa addinin musulunci, wanda gidauniyar Ganduje Foundation ta dauki nauyi.




SAKON GAYYATA ZUWA KADDAMAR DA TALLAFIN RABON TAKIN ZAMANI GA SASSAN TINUBU SUPPORT GROUP NA JIHOHI 7 NA AREWA MASO YAMM...
17/07/2026

SAKON GAYYATA ZUWA KADDAMAR DA TALLAFIN RABON TAKIN ZAMANI GA SASSAN TINUBU SUPPORT GROUP NA JIHOHI 7 NA AREWA MASO YAMMA, KARKASHIN JAGORANCIN HON. BAFFA BABBA DAN'AGUNDI, DG NPC

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.

Bisa umarnin Jagora Hon. Baffa Babba Dan'agundi, Darakta Janar na National Productivity Centre (NPC), ina amfani da wannan dama wajen gayyatar daukacin mambobin Tinubu Support Group (TSG) zuwa bikin kaddamar da rabon tallafin takin zamani, wanda za a gudanar kamar haka:

Rana: Asabar, 18/07/2026
Lokaci: 10:00 na safe
Wuri: Babban Ofishin Tinubu Support Group, Audu Bako Way, Kano.

Rukunin wadanda za su ci gajiyar shirin sun hada da:

1. Rukunin Kungiyoyin Tinubu Support Group daga Jihohi 7 na Arewa maso Yamma.

2. Rukunin al'umma wadanda suke noma da s**a fito daga Jihohin 7 na Arewa Maso Yamma.

2. Kano Central Tinubu/Abba Support Group dake Kananan Hukumomi 15 da Mazabu 172, tare da karin Kananan Hukumomin Kibiya da Sumaila.

3. Chairmomi da Sakatarorin APC na Kananan Hukumomi 15 da Mazabu 172 na Kano ta Tsakiya.

4. Rukunin manyan 'yan siyasa masu gudanar da harkar noma a fadin Jihar Kano.

5. Rukunin Malamai (Mahadar Alkhairi) dake Kananan Hukumomi 44 da Mazabu 484 na Jihar Kano.

6. Rukunin Tsofaffin 'Yan Hisbah (Khairul Umma) dake Kananan Hukumomi 44 da Mazabu 484 na Jihar Kano.

7. Rukunin Tafiyar Siyasar Gidan Marigayi Alhaji Musa Gwadabe.

8. Tsofaffin Shugabannin ANPP na Coalition.

9. Rukunin Mafarauta dake Kananan Hukumomi 15 da Mazabu 172 na Kano ta Tsakiya.

10. Ragowar rukunin al'umma, musamman manoma daga Kananan Hukumomi 44 na Jihar Kano.

Wannan gayyata ta shafi dukkan sassan Tinubu Support Group, maza da mata.

A karshe, ina kara jaddada muhimmancin kasancewa a wurin taro akan lokaci, tare da sanya shiga ta kamala da kuma yalayen hulunanmu kamar yadda muka saba.

NB: Dukkan sauran Jihohi 6 na Arewa Maso Yamma Suma zasu kaddamar da wannan rabon taki a wannan Rana ta Asabar 18-07-2026. Karkashin kulawar SSA na DG

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya sanya albarka a wannan shiri, Ya ba shi nasara, Ya kara daukaka tafiyarmu, Ya kuma ci gaba da yi wa shugabanninmu jagora da kariya. Ameen.

Hon. Nasiru Usman Na'ibawa (Zico)
S.L.A ga Shugaban Majalisar Dattijai
17/07/2026

The Need for President Bola Ahmed Tinubu to Reintroduce Discipline and Moral Order in NigeriaA Position Paper by   (TTP)...
17/07/2026

The Need for President Bola Ahmed Tinubu to Reintroduce Discipline and Moral Order in Nigeria

A Position Paper by (TTP)

No democratic nation can achieve sustainable progress without discipline, respect for the rule of law, and a strong moral foundation. As Nigeria continues on the path of national renewal, there is an urgent need to strengthen moral values and restore a culture of responsibility across all sectors of society.

The administration of President Bola Ahmed Tinubu has demonstrated commitment to reforms aimed at repositioning the country for long-term growth. However, national development requires not only economic and institutional reforms but also a deliberate effort to promote discipline, integrity, patriotism, and responsible citizenship.

One of the major challenges confronting Nigeria today is the gradual decline in societal values. Political thuggery, youth manipulation, criminality, corruption, and disregard for the rule of law have weakened public confidence and hindered national development. These challenges require collective action from government, community leaders, religious institutions, families, and citizens.

It is also important for political leaders at every level to demonstrate exemplary leadership by promoting peace, accountability, and merit rather than encouraging violence or irresponsible conduct among young people. The future of our nation depends on the values we instill in the next generation.

The conduct of some Nigerians abroad has also affected the country's international image. While many Nigerians continue to make the nation proud through excellence and hard work, the actions of a few individuals have damaged Nigeria's reputation in some parts of the world. This calls for renewed commitment to ethical conduct, respect for the laws of host countries, and responsible representation of our nation wherever Nigerians reside.

Restoring discipline and moral order should not be viewed as the responsibility of one administration alone. It is a national responsibility that requires continuity beyond the present government. Every current and future leader must prioritize policies that encourage integrity, civic responsibility, respect for the law, and national unity.

Nigeria's progress depends not only on infrastructure and economic reforms but also on the character, discipline, and values of its people. By promoting moral responsibility and responsible leadership, we can build a stronger, safer, and more prosperous nation for future generations.

(TTP)
Comr Rufai Mustapha Daneji

Promoting Good Governance, National Development, and Responsible Citizenship.

Yanzu-yanzu, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da Sanata Kashim Shettima a matsayin wanda zai yi masa takarar ...
16/07/2026

Yanzu-yanzu, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da Sanata Kashim Shettima a matsayin wanda zai yi masa takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027, inda ya miƙa masa takardar shaidar tabbatarwa.

Address

No. 18b Magaji Rumfa, Nassarawa, Kano
Kano
234

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ganduje Media For Tinubu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share