07/11/2024
Murnar mu na neman komawa ciki!
Kwanakin baya farashin kayan abinci ya sauka matuƙa, amma zuwa yanzu lamarin sai addu'a, farashin sai hawa yake k**ar wutar shuci.
Ba komai ya haddasa haka ba illa rashin kishi irin na mu na talakawa da muke karyar da kayan amfanin mu da mu ka noma wata da watanni ga ƴan jari hujja, waɗanda su ke bin mu har gona su na sayewa araha domin niƙawa a kamfanunuwan su na shinkafa.
Na biyu rashin imani na ƴan jari hujja, masu mai da talaka bayi domin buƙatun su na wofi.
Allah Ya gyara Ƙasar nan.