24/06/2026
Rubutawar Aminu Soja
BAN SAN MAI UNGUWAR DORAYI TA TSARE WA WASu MUTANE BA.
Duk Lokacin da wani Abu ya faru a unguwar DORAYI sai mutane su ta kururuta shi, k**ar unguwar abin ya taɓa faruwa a tarihi,
Bari in Fara da maganar Daba wato fadan Daba, akasarin mutane sun dauki DORAYI unguwar ce ta yan Daba , saboda kururuwar da gidajen Radio s**a dinga yi akan DORAYI lokacin da aka samu fadace fadacen, tsakanin unguwannin yan gargajiyar DORAYI guda biyu wato Gobirawa da makera, abin da yasa wannan fadan daban ya dauki hankalin mutane saboda Babban t**in DORAYI wato Sheikh Ja'afar Road ya raba t**in unguwannin da suke fadan duk lokacin da suke fadan sai sun kashe Babban t**i, wannan shi ya ke daukar hankalin mutane, sai ka ga ana ta posting ana fadan Daba a DORAYI.
To ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba abun a dake fada akan DORAYI kashi 80 karya ne. Ni haifaffen cikin birnin Kano ne kuma a Kano na girma kuma na ke zaune, na san tarihin Daba a Kano, da unguwannin da aka yi fadace fadacen Daba na sama da shekara Arba'in kuma har yanzu ana yi, amma DORAYI bata k**a rabin wasu unguwannin ake fadan ba.
Misali
Na san ana fadan Daba tsakanin Zage da kofar Wambai, Fagge da kofar Wambai, Koki da Fagge, Mandawari Dan Agundi Kofar Na'isa Gwammaja duk wadannan unguwannin babu wacca ba ta da tarihin fadan Daba daga Shekara 40 zuwa yau, kwanannan aka dinga fadan Daba tsakanin Zango zuwa kofar mata na kwana da kwanaki amma babu zabiyar, ta shiga Radio ta yi kwarmato a Koki ne fa akwai inda ake cewa Zirin Gaza sai a kwana bakwai ana fadan Daba amma da ya ke a lungu ne babu wanda yake magana, criminals din da suke a tsakanin Kurna Rijiyar Lemo, Bachirawa, a layi daya sai ka samu criminals din da s**a linka na DORAYI, akasarin yan damfarar Kano suna Birget da tarin criminals a tsakanin Rimin kebe Birget Tudun Wada Gayawa da Kwana Hudu kwanar Jaba da PRP da Badawa ban ji ku na kwaroroto akan su ba ko don unguwannin Baki ne, kare kare Gwari Gwado Bendel da Buzaye?
Ba kwanannan aka ce ma'aikata sun kashe wani yaro da ya addabi Gwammaja ba? Waye Bai san Sule Manke ba dan dabar Fagge? Wanda a BBC na ji mutuwarsa sabo da shahara,
Wasu ma cewa suke yi Burekata dan DORAYI ne , ba su san cewa Daga cikin gari uwarsa ta taso ta sai gida a DORAYI da tumunin takabarta,
Lokacin da Wani Umar dan unguwar Sheka wanda kowa ya san yadda ta yi kaurin suna a fadan Daba da criminals.
Umar ya baro sheka ya kashe wata mata Fatima da ya'yan ta a unguwar charanci, amma mutanen dorayi aka dinga tsinewa Ba a ma san ba unguwa daya ba ce, kowacce ma Dagacin ta daban.
Yadda aka ji haushin yan dorayi ba ma ji haushin Wanda ya yi kisan ba, laifin yan dorayi kawai an yi kisa a unguwar su ba su hana abin da ba su san lokacin da aka yi ba, Umar din fa ake zargin da kashe wasu mata da kona su a tudun Yola amma ba a zagi yan unguwar tudun Yola ba sai DORAYI, shin wanda ya kashe HANIFA dan dorayi ne? Ko ya yaron da ya kashe iyayensa tsohon ma'aikcin DSS a Kundila dan DORAYI ne? Ko wanda ya kona mutane a Masallaci dan Dorayi ne ?
Sai ku dinga yi wa al'umma Sama da mutum dubu dari hukunci da laifin da wasu tsirarin da ba su kai mutum dari ba hukunci, Wallahi ba kai ba ko hukuma aka ce ta kamo yan Daba dari a dorayi an bata aiki, amma sai a dinga cewa yayanku yan Daba k**ar duk yaron da yake DORAYI dan Daba ne,
Abin takaici sai ka ga mutum daga ƙauyuka irin su Yobe Gombe da Bauchi wai suna zagin doray sun baro yan boko haram din su da yan kalare da yan Sara s**an su, wani ma bai taba zuwa kano ba bare unguwar DORAYI.
Wai Tarihin Alkhairin dorayi a ke so a share ne maye da sharri da kazafi?
To dorayi dai bata fi shekara 30 da zama Alkarya ba, da yan ƙauyuka ne da wasu, sai lokacin da za a yi t**in Tal'udu , mutanen Mandawari Dandago, sani mai nagge, da aikin ya taso da s**a dawo, wannan shi ya sa Dorayi k**ar kowacce unguwa ta cikin fadalawa, 95% Hausawa da Fulani ne Usul , kuma 70% yan cikin gari ne, Akwai muhimman abubuwan a cikin ta Irin su BUK old site ITF, Gandun Sarki wanda ake Hawan Dorayi, marigayi Sarkin dutse Alh sunusi Nuhu Gashi a Dorayi ya zauna har aka masa Sarkin dutse, , Gado da masu , Wanda kowa ya san yayan sa Furofesoshi ne , da da lauyoyi, su sani Gadanya. Da gidan police Kwamishina biyu a dorayi,
Wai mutane sun manta Sheikh Ja'afar Mahmud Adam a dorayi ya rayu da Masallacinsa na almuntada tare da iyalansa ?
Dr Ahmad Ibrahim Buk ko ina ce Dakta Ahmad Ahmad Bamba ya zauna da makarantar sa sama da shekara ashirin kafin Allah ya h**e masa ya koma tudun Yola har yanzu makarantar sa tana cikin Dorayi,
Bana ji akwai unguwa a cikin birni Kano ban da garin kura da ta take yaye Mahaddata Alkur'ani k**ar DORAYI, Makarantar mus'ab ta Mallam Ammaru Khalid Allah kadai ya san adadin Mahaddata Kur'anin da ta yaye, shi kan Mallam Ammaru Ya ta ba ciyo wa Nigeria da Kano gasar karatun Kur'ani, kuma daliban sa sun ci ciyo wannan gasar ta kasa da ta duniya,
Akwai makarantar malam Mahadi da ake cewa Mahadi sai yaye mutum dubu da s**a yi saukar Kur'ani.
Makarantar Sallau da Mai Kumsa duk fa a dorayi suke. Ko Ni na kafa makaranta mai suna Darul Quran Dorayi da ban san adadin Mahaddatan da ta yaye ba, Akwai kuma ire iren su da yawa.
Amma ba a fadan Duk wadannan Alkhairan sai abin da wasu tsirarun fitinannu yara suke yi.
BABBAN MUNAFUNCIN DA YA DAGA MIN HANKALI SHI NE MA'AIKATAR FILM
A July 2016 Dan majalisar Kiru da Bebeji Hon Abdulmumin Jibrin kofa ya kawo Film industry a mazabar sa ta kofa aka yi cha gaba daya garin Kano aka hada baki aka ce ba a yarda ba har yanzu film industry da ba a yi ba kenan wajen yana nan kilomita 60 tsakanin sa da birnin Kano ba da a cikin birnin Kano ba.
Yau Tarihi zai maimaita kansa mutanen dorayi sun kwaikwayi mutane kano su ce ba su yarda ba, MUNAFUKAI Sun yi chaaa , daga masu cewa Hassada sai masu cewa Talauci da jahilci, har da marar kunyar da ya ce wai da yadda manyan Dorayi s**a ba da himmar yakar Film da haka s**a ba da himmar yakar Daba da shaye shaye, sai na ga tsantsar jahilci a wannan kalaman daga wajen wanda ake wa kallon wai mai ilimi, to kaddara ma mayan Dorayi basa kome akan daba da shaye shaye, to kuma sai su bari a kawo musu fasikanci cikin unguwa?
Ina daya daga cikin Dattawan Dorayi Ni na san Fadi tashin da muka yi da domin kawo karshen fadan daban a Dorayi da ire irena Da Abdullahi danfodiyo, da Dagacin Dorayi da masu unguwanni da irin su. Barrister Wada Bashir, su Mallam Aminu Library su Amb Tijjani Aminu Adam.mallam iliya mal Ibrahim dan Bunkure su baba soja da DPO kunyar da sharada.
Wani ma cewa ya yi unguwar Ghetto da talakawa kuma har. Yanzu bai fada mana lambar gidan uban shi A Sultan Road Sokoto Road ko Lamido Cresent ba,
Shi ma Yaron wai rashin Aikin yi ne ya sa ake haka.
Ba na gari ne da dani za a ganin a videon Amma wanda ya yi magana da yawun mu Dr Yusuf PhD ya videon ya ce shi lecturer an North west university kuma malamin lissafi ne, a bayan da na ga Mal Bukhari mai makarantar Anas bin Malik kamin su Mahsin da Muslim, na ga Malam Ibrahim dan Bunkure mai makarantar Salafussali, da malam Bashir Aliyu masu Foundation din na marayu da sauran muhimman mutane, wai wadannan, dan namaye ya ke cewa rashin aikin yi ne,
To a karshe Ni yanzu na tashi na bar Unguwar DORAYI ba na cikin ta kuma irin wadannan sharrance sharrance da kazafi da karereyin yin ya sa na tashi, dama ba a Dorayi aka haife ni ba zama ne ya kai Ni, duk da haka ina tare da mutanen dorayi dari bisa dari, na zauna DORAYI tsawon shekara ashirin yawanci ya'yan anan aka haifesu, ina da gidaje a dorayi mutane Dorayi mutanen kirki ne matasan Dorayi yaran kirki ne masu neman na kansu, ba su yi kaurin suna wajen shaye shaye k**ar muke ganin NDLEA suna kaiwa da komowa a cikin wasu unguwannin.
Sannan mutanen Dorayi da matasan ta da masu ilimin cikin ta da masu kudi da ma kowa da kowa Ku fito ku kare martabar unguwar ku da muhibbarta, tunda aka fara maku wannan sharrance sharrance darajar gidaje ya karye a Dorayi, samari ba sa son shigowa neman aure, yan'uwa da suke waje kullum hankalin su na tashe,
Ina yan social media Ku yi posting ku fada mutane ainihin gaskiyar abin da yake faruwa ina manyan yan jaridar Dorayi Irin su Nasiru Ahmad Karaye Maryam Baba yaro, Musa Na Huguma da sauransu su.
Aminu Soja Dorayi
'