23/10/2026
KCPC Ta Sasanta Korafi Tsakanin Mai Saye da Kamfanin MAROOSH COCO BREAD Kan Wani Ssbani na kasuwanci
Hukumar Kare Haƙƙin Mai Saye ta Jihar Kano (KCPC) ta samu nasarar sasanta wani korafi da wani mai saye, mai suna Keymond Augustine, ya shigar kan kamfanin MAROOSH COCO BREAD da ke Kano, bisa zargin samun rashin jin dadi a biredin da ya saya
Mai korafin ya bayyana cewa ya sayi biredin ne a babban shagon Barakat, inda ya saba gudanar da siyayyarsa. Sai dai ya ce abin da ya gani a cikin biredin ya ba shi mamaki tare da fusata shi, lamarin da ya sa ya tuntubi kamfanin domin sanar da su abin da ya faru, amma hakan ya haifar da rashin fahimtar juna tsakaninsa da su
Bayan karɓar korafin, jami’in hukumar KCPC mai kula da irin waɗannan matsaloli ya gayyaci wakilan kamfanin domin jin ta bakinsu da tabbatar da gaskiyar lamarin.
Da yake mayar da martani, shugaban kamfanin biredin, Mista Maroosh, ya bayyana cewa abin da ya faru kuskure ne da ba su taɓa fuskantar irinsa a baya ba. Ya nemi afuwar mai korafin, tare da roƙonsa da ya yafe musu, yana mai tabbatar da cewa za su ɗauki matakan da s**a dace domin kauce wa sake faruwar irin wannan matsala.
Haka kuma, ya bai wa hukumar KCPC tabbacin cewa kamfanin zai ci gaba da kula da ƙa’idoji da dokokin da s**a shafi kare haƙƙin mai saye, musamman wajen tabbatar da inganci da tsaftar kayayyakin da suke samarwa.
Tun da farko, a nasa jawabin, Sakataren Zartarwa na hukumar KCPC, Dr. Ibrahim Garba Muhammad, ya bayyana cewa irin wannan sasanci na daga cikin hanyoyin da hukumar ke bi domin wayar da kan jama’a game da haƙƙoƙinsu a matsayin masu saye.
Ya jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da kare haƙƙin masu saye ba tare da la’akari da girman ko ƙarancin kuɗin cinikin da s**a yi ba.
Dr. Ibrahim Garba Muhammad ya kuma yi kira ga kamfanoni, manyan shaguna da ƙananan masana’antu da su riƙa bin ƙa’idoji da dokokin da hukumar ta gindaya, domin tabbatar da ingancin kayayyaki da kare lafiyar masu saye.
Hukumar KCPC ta sake jaddada aniyarta ta tabbatar da cewa masu saye sun samu kayayyaki masu inganci da aminci, tare da kare su daga duk wani abu da zai iya cutar da lafiyarsu ko tauye haƙƙoƙinsu.
Dagq
Daraktan Wayar da Kai na Hukumar KCPC
Jamilu Mustapha yakasai