29/03/2026
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana matuƙar alfaharinta da ƙauna ga mijinta, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yayin da yake bikin cika shekaru 74 da haihuwa.
A yau Lahadi ne Shugaba Tinubu ya cika shekaru 74 a duniya, inda ‘yan Najeriya daga sassa daban-daban s**a aike masa da saƙonnin fatan alheri da addu’o’i.
A cikin wata sanarwa da ta fitar kuma ta sanya wa hannu da kanta, Uwargidan Shugaban Ƙasar ta bayyana cewa tana alfahari da irin jagorancin da Shugaban ke bayarwa.
Ta kuma roƙi Allah da ya ƙara masa lafiya, ƙarfi da natsuwa, tare da yi masa fatan samun nasara wajen jagorantar ƙasar nan zuwa ga ci gaba mai ɗorewa.