Ssr Film Institute Kano

Ssr Film Institute Kano SENIOR SPECIAL REPORTER ON FILM INSTITUTE TIGA KANO, TO THE GOVERNOR OF KANO STATE HIS EXCELLENCY ALHAJI ABBA KABIR YUSUF

SSR- Munir Ibrahim Takai✍️

🕋✨ Mina na iya zama wajen da mutum zai rikice musamman ga masu zuwa Hajji karo na farko. Yin shiri da kula sosai na taim...
24/05/2026

🕋✨ Mina na iya zama wajen da mutum zai rikice musamman ga masu zuwa Hajji karo na farko. Yin shiri da kula sosai na taimakawa wajen sauƙaƙa ibada cikin aminci da kwanciyar hankali.

Ga wasu muhimman shawarwari domin kada ka ɓata hanya a Mina:
📍 Da zarar ka isa, ka gano tantinka a taswira sannan ka haddace ainihin wajen.

📞 Ka adana lambar jagoran ƙungiyarku a waya kuma ka tabbata tana da sauƙin samu.
👥 Ka kasance tare da ƙungiyarka a koda yaushe. Idan kuka rabu, ka sanar da jami’i ko ma’aikaci nan take.

🪧 Ka kula da allunan hanya, lambobin sashe da wuraren da s**a shahara domin su taimaka maka wajen gano hanyar dawowa.

🗺️ Kafin ka fita daga tantinku, ka tsara hanyar dawowarka domin samun sauƙin komawa.

Ka ajiye wannan jagora domin tafiyar Hajjinka, ko ka tura shi ga ‘yan uwa da abokan arziki masu shirin zuwa Hajji 🤍

🕋 Muna hidimar Alhazai tun shekarar 1982
Aroma Travel Service Pvt Ltd
“Sunan da za ka iya yarda da shi.”

ALHAMDULILLAH… ✈️🕋⏰ 5:00amYanzu haka muna a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano International Airport domin shirye-shi...
20/05/2026

ALHAMDULILLAH… ✈️🕋

⏰ 5:00am

Yanzu haka muna a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano International Airport domin shirye-shiryen tashi zuwa Ƙasar Saudiyya, inda zamu sauka kai tsaye a Birnin Jeddah domin sauke farali na aikin Hajjin bana 2026.

Ina matuƙar godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da Ya nuna min wannan rana mai albarka. Haka kuma ina miƙa saƙon godiya ta musamman ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa wannan dama da kulawa da ya bai wa al’ummar jihar Kano. Allah Ya saka masa da alkhairi, Ya ƙara masa lafiya da nasara wajen jagoranci.

Ina kuma addu’ar Allah Ya kawo wa duk wanda bai samu damar zuwa bana ba nasa lokaci cikin sauƙi da alkhairi. 🤲

Ina roƙon addu’o’inku na Allah Ya sa tafiya lafiya, Ya karɓi ibadunmu, Ya sa mu dawo gida lafiya cikin rahama da gafara.

A matsayina na ɗan Adam, ina neman yafiyar duk wani kuskure ko ɓata rai da na taɓa yi wa kowa, cikin sani ko rashin sani.

Allah Ya sa Hajjinmu ya zama Hajji Mabrur. Ameen. 🕋🤍

Munir Ibrahim Takai
Ssr Film Institute Kano,
To the Executive Governor of Kano State.

Highlights

Gadai Ainihin Yadda Wajen Taron Oga Ake, Amma kunzo kunata Sakawa Mutane Tsohon hoton lokacin da muke tare Daku.        ...
18/05/2026

Gadai Ainihin Yadda Wajen Taron Oga Ake,

Amma kunzo kunata Sakawa Mutane Tsohon hoton lokacin da muke tare Daku.

#

*SANARWAR!!!!! SANARWA!!!!!*   Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano na sanar da Alhazan da s**a fito daga ƙananan huk...
18/05/2026

*SANARWAR!!!!! SANARWA!!!!!*


Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano na sanar da Alhazan da s**a fito daga ƙananan hukumomin:

- TOFA
- RIMIN GADO
- MADOBI
- KABO
- GARKO
- AJINGI
- WUDIL
- TAKAI
- SUMAILA
- GAYA
- KARAYE
- ROGO

Cewa su fito Sansanin Alhazai na Jihar Kano (Hajj Camp) domin tantance su zuwa ƙasa mai tsarki.

Za su fito ne a yau Litinin, 18 ga Mayu, 2026 da misalin ƙarfe 12:00 na dare.

Ana buƙatar maniyyata su fito cikin uniform ɗinsu tare da ƙananan jakunkunan da aka ba su domin tafiya ƙasa mai tsarki.

Sanarwa daga:
Sulaiman Abdullahi Dederi
P.R.O

18/05/2026

Wai Tunda Allah ya yi duniya babu wani abu da ya taɓa wani abu” ana danganta wannan da abin da masana ke kira Electromagnetic Force da kuma Quantum Physics.

A ilimin kimiyya, idan ka taɓa tebur ko bango, a zahiri ƙwayoyin zarra (atoms) na hannunka da na abin da ka taɓa suna kusa sosai ne kawai, amma ƙarfin lantarki da ke tsakanin electrons yana hana su haɗuwa kai tsaye.

Wannan shi yasa kake jin “taɓawa” wato tura juna da ƙarfin electromagnetic, ba lallai haɗuwar jiki kai tsaye ba.

Sai dai a lura:
A ilimin kimiyya na yau da kullum, ana amfani da kalmar “taɓawa” saboda abubuwa suna hulɗa sosai.
Don haka faɗin “babu wani abu da ya taɓa wani abu” hanya ce ta bayyana yadda ƙananan zarra ke aiki, ba wai komai ƙarya ba ne gaba ɗaya.

“A cewar Quantum Physics, abin da muke kira taɓawa ba haɗuwar abubuwa kai tsaye ba ce, illa hulɗar Electromagnetic Force tsakanin zarra. Wato tun farkon duniya babu wani abu da ya taɓa wani abu kai tsaye!”

Alhamdulillah 🙏
17/05/2026

Alhamdulillah 🙏

Jajirtaccen Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf , ya sasanta saɓanin da ke shirin ɓarkewa tsakanin Hon. Alhassan Rurum ...
17/05/2026

Jajirtaccen Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf , ya sasanta saɓanin da ke shirin ɓarkewa tsakanin Hon. Alhassan Rurum da Sen. S A Kawu Sumaila, OFR Ph.D domin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da cigaban siyasar Jihar Kano. 🙏

Munir Ibrahim Takai
Ssr Film Institute Kano
17/05/2026

17/05/2026

Jawabin ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Rano/Kibiya/Bunkure, bayan kammala zaman sulhu da Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya jagoranta tsakaninsa da Sanata Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila, domin tabbatar da haɗin kai da cigaban Jihar Kano da kuma jam’iyyarmu mai albarka.

Address

Kano
712103

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ssr Film Institute Kano posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Ssr Film Institute Kano:

Share