25/11/2025
The insecurities in Nigeria has worsen. It's a big Slap and a Shame to the so called Giant of Africa to be in this state of turmoil. Surprisingly, after the threat by Donald Trump, the situation has escalated. The killing of Brig Gen Uba, abduction of innocents students, citizens (Muslims and Christians) and barbaric killings of innocent souls need to be addressed at once. To me, our government was never serious on this cases, we should have learnt from Chibok and Dapchi tragedies.
Another calamity is the closure of our schools especially in the Northern part of this country, it shows how weak we are as a country. Does that mean the hooligans are winning? How did we come to this stage? Our economy, educational sysytem, security, welfare, health system, unity and peaceful coexistence are deteriorating. The enemies of this country are igniting civil war in this country but they will never succeed. We need more efforts from the Federal and state governments. The genocide in this country affects all of us regardless of your religion, region and tribe.
Rashin tsaron Najeriya kullun kara ta6ar6arewa yake yi, ba karamin abin kunya bane kasa k**ar Najeriya tana cikin halin kakanikayi. Abin mamakin shine tun bayan da Donald Trump yayi ikirarin kawo hari Najeriya, abubuwan s**a kara ta'azzara. Kisan gillar da aka yiwa Janar Uba, sace daliban makaranta, kashe al'umma (Musulmai da Kiristoci) ya k**ata a magance ta cikin lokaci kankani. Ni a gani na gwamnati bata mayar da hankali kan tsaro tun farko, ya k**ata ace mun koyi darasi akan daliban Chibok da na Dapchi.
Wani karin tashin hankali shine rufe makarantu musamman a arewacin Najeriya, ya nuna irin raunin mu a matsayin mu na kasa mai cikakken iko. Shin hakan yana nufin yan bindiga sun yi nasara a kanmu kenan? Ya akai muka tsinci kan mu a irin wannan yanayi? Tattalin arzikin mu, ilimin mu, lafiyar mu, tsaron mu, hadin kai da zaman lafiyar mu kullun lalacewa suke yi. Na fuskanci makiyan Kasar nan tamu so suke su kunno mana wutar yakin basasa kuma ba zasu yi nasara ba. Muna bukatar gwamnatin tarayya da na jihohi su kara mayar da hankali wurin samar da tsaro. Hakika wannan kisan kare dangi da ake magana, ya addabi kowa, ba ruwan sa da addinin ka, yaren ka ko 6angaren ka.
Abdulwahab Dayyabu Abdulwahab
President