Abdullahi Ibrahim Bashir - Maikanon Kwankwasiyya

Abdullahi Ibrahim Bashir - Maikanon Kwankwasiyya Abdullahi Ibrahim Bashir (Maikano Kwankwasiyya) Political Movement...

Sakon Barka da SallahA madadina da iyalai na ni Hon. Abdullahi Ibrahim Bashir, tsohon Shugaban Karamar Hukumar Tarauni, ...
06/06/2025

Sakon Barka da Sallah
A madadina da iyalai na ni Hon. Abdullahi Ibrahim Bashir, tsohon Shugaban Karamar Hukumar Tarauni, muna mika sakon fatan alheri da barka da Sallah Babba ga daukacin al’ummar Tarauni da musulmin Najeriya baki ɗaya.

Allah ya karɓi ibadunmu, ya karɓi hadayunmu, ya albarkaci rayuwarmu da zumuncinmu. A wannan lokaci na sadaukarwa da tausayi, muna rokon Allah ya kawo zaman lafiya, cigaba da albarka ga ƙasarmu Najeriya.

Barka da Sallah!

05/06/2025

Ni Hon Abdullahi Ibrahim Bashir
A madadi na na tsoho Shugaban Karamar Hukumar Tarauni "MaiKanon Kwankwasiyya", muna taya ku murnar wannan rana mai albarka. Ranar Arafa, daya daga cikin mafi girma kuma mafi falala cikin kwanakin Musulunci.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya karɓi ibadunmu, ya gafarta mana zunubanmu, ya albarkaci rayuwarmu da iyalanmu, ya tsare mana imaninmu da lafiyarmu. Allah ya sanya mu cikin bayinSa da zai yafe musu, ya kuma amsa mana dukkan addu’o’in da muke yi a wannan rana mai albarka.

Ga waɗanda ke cikin aikin Hajji, Allah ya sauƙaƙa musu ibada, ya maida su gida lafiya, ya karɓi hajjin nasu ya kuma basu ladan Hajjin da aka karɓa.

Muna roƙon zaman lafiya, arziki, da cigaba ga al’ummar Tarauni, Jihar Kano, da Najeriya baki ɗaya. Allah ya albarkaci kasarmu da shugabanninmu, ya bamu jagoranci na gari, da zaman lafiya mai dorewa.

Ranar Arafa rana ce ta addu’a, istigfari, da neman gafara. Mu yi amfani da wannan dama wajen komawa ga Allah da dukkan zuciyarmu.

Muna yi muku fatan alheri da fatan Allah ya karɓi ibadunmu duka.

Wannan sako yana zuwa ne daga tsohon shugaban karamar hukumar Tarauni, Ina fatan alheri da addu’a ga dukkan al’umma.

Barka da Ranar Arafa!

Address

Karkasara, Tarauni LGA
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abdullahi Ibrahim Bashir - Maikanon Kwankwasiyya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share