10/02/2025
Idan Har Kai Talaka Ne Mutane Bazasu Taɓa Sanin Tasirinka Ba, Amma Daga Lokacin Da Kayi Arziƙi To Hatta Kare Da Doki Da Ɓera Zasu Kirarin Su Danginka Ne.
Domin Hatta Karnuka Da Ɓeraye Suna Ƙulla Alaƙa Ne Da Gidan Masu Kuɗi, Inda Zasu Samu Abinci Isasshe Ba Kamar Gidan Talaka Ba, Inda Ko Ƙamshin Abincin Bazasu Jiba.
Yanada Matuƙar Wahala Ka Iya Tantance Abokanka Na Gaskiya A Lokacin Da Kake Da Arziƙi. Abokanka Na Gaskiya Zasu Ƙaunaceka Koda Baka Mallaki Komai Ba, Sannan Abokan Bogi Zasu Ƙaunaceka Ne Saboda Abubuwan Da Ka Mallaka.
Bazaka Taɓa Rasa Abokan Gaskiya Ba Koda Ka Talauce, Sai Dai Zaka Rasa Abokan Bogi Da Suke Faɗa Maka Cewa Su Abokanka Ne Na Gaskiya.
Da Wannan Fahimtar Babu Lokacin Da Yake Da Inganci Kayi Ƙidayar Abokanka Na Gaskiya Kamar Lokacin Da Kake Cikin Talauci. Karkayi Mamaki Idan Babu Wanda Ya Iya Tunawa Da Sunanka Ko Akaƙi A Saurari Shawararka Akan Kowacce Irin Magana.
A Wannan Rayuwar Idan Bakada Komai Shawarwarinka Ba Abin Kalla Bane Ballantana Sauraro Koda Kuwa Fasaha Da Basira Suna Cikinsu.
Amma Matuƙar Kanada Arziƙi Ko Shahara To Hatta Wawiyar Kalmarka Zata Zama Abin Kamawa. Idan Kana Cikin Talauci Zaka San Sahihan Abokanka, Idan Kayi Arziƙi Abokanka Ne Zasu Sanka.
Saboda Haka Karka Wawantu Daga Ƴan Wasan Kwaikwayon Abokai.
Na Barku Lafiya.🚶