13/07/2020
RUNDINAR 'YAN SANDAN NIGERIA ZATA DEBI SABBIN JAMI'AI
Rundinar 'yan sandan Nigeria karkashin jagorancin Maigirma shugaban rundinar 'yan sanda IGP Muhammad Abubakar Adamu tana sanar da al'umma cewa zata debi sabbin jami'ai masu mukamin Constable
Idan Allah Ya kaimu nan da kwana uku wato ranar talata 14-7-2020 za'a bude shafin yanar gizo wanda za'a shiga a cike ga masu sha'awar shiga aikin na 'yan sanda, za'a rufe cika online form ranar 23-8-2020
Akwai ka'ido da dole sai an cike kafin wani ya samu damar shiga kamar haka:
-Dole sai kana da shaidan haihuwa na zama 'dan Nigeria, kuma kana da nambar rijistan katin 'dan kasa (NIN)
-Sai wanda yake da credit biyar na jarrabawan kammala karatun sakandare wanda akwai English da Mathematics
- Sai wanda ya kai shekarun haihu 17 sannan bai wuce shekaru 25 ba
- Sai wanda yake da cikakken hankali da lafiya, ga maza wanda tsayinsa ya kai 1.67m, ga mata 1.64m
-Sannan sai wanda fadin kirjinsa ya kai 86cm (34 inches) ga maza kadai
-Ga mata wacce take dauke da juna biyu ba zata samu shiga ba
Wadanda suke da matsala na gani da ji, da sarkafewar hakora, baudewar kafa ko wata lalura kada su cika, kuma ba'a taba kamaka da wani laifi ba, sannan baka shaye-shaye, don idan kaje wajen tantancewa suna ganin alamar kana shaye-shaye zasu koreka
Ga wadanda s**ayi applying s**a cika wadannan ka'idoji za'a kirasu tantancewa ranar 24-8-2020 wanda za'a kammala ranar 30-8-2020 a dukkan jihohin Nigeria da babban birnin tarayya Abuja, ga wadanda s**a samu nasara za'a bayyana sunayensu a jaridun kasa da sauran kafofin yada labarai ranar 14-9-2020 inda za'a turasu sansanin horar da aikin 'dan sanda
Wannan shine shafin yanar gizo wanda za'a shiga a cike form din kamar haka:
www.policerecruitment.gov.ng
Kafin ka cika form din ka tabbata ka mallaki email adress mai kyau, kuma NIN na katin 'dan kasar ka daidai ne
Rundinar 'yan sanda tana sanar da al'umma cewa wannan tsarin kyauta ne, a gujewa fadawa tarkon 'yan damfara, masu korafi zasu aika sakon su ta nan:
08100004507
[email protected]
[email protected]
Sanarwa daga kakakin rundinar 'yan sandan Nigeria na kasa
DCP Frank Mba
Allah Ya sa a dace Amin