29/07/2022
Kowane shugaba a Arewa idan zai bada misali akan wani sha'ani na cigaba kamar abunda ya shafi harkar ilimi, cigaban kasuwanci, bunqasar tattalin arziqi, harkar tsaro, sai kaji yace kudu sunyimana nisa.
Kuma abun takaici shine wanda yake bada misalin zaka sameshi ya taba riqe wata babbar dama a Nigeria amma bai iya kawowa mutanensa wani cigaba ba, sai surutu a kafar yada labarai.
Mu al'ummar Arewaci haqiqa mutanen kudu sunyimana nisa sosai ta fuskar cigaba, sakamakon sunfimu sanin 'yancin kansu.
Domin a yankinsu babu wani mutumin da ya isa yafito takara face kafin yafito yayiwa al'ummarsa wani abun cigaba, amma mu a Arewa kawai idan mutum yanada kudi koda baitaba taimakon wani to sai kaga yafito takara kuma yayi nasara koda kuwa ansan cewa azzalumi ne.
Sannan kuma a yankin kudu kafin mutane su yadda da cewa zasu zabeka sai kafadi irin abubuwanda zakamusu idan ka hau mulki, sannan kuma idan ka hau bakamusu ba duk inda kabi zasu jefeka su nunamaka basasonka a fili, sannan kuma suyi qoqarin kayar dakai su hanaka yin tazarce.
Amma mu a Arewa wani kamma baitaba ganin wanda ya zaba ba, sannan kuma idan ka tambayeshi meye yayi na alkairi wanda har yasa ya zabeshi zai cemaka kawai yanasonsa ne haka kawai.
To yakamata mu 'yan Arewa mu farka musan halinda muke ciki, domin har yanzu 'yan siyasanmu na Arewa basason mu donhaka muma yakamata kafin mubawa mutum dama yanadakyau mu tabbata yayimana wani abu sannan kuma yafadamana qudirinsa na alkairi kafin mubashi dama, donhaka sai mu kiyaye Allah yasamudace.
Sign📝📝📝
Comr. Musa Saminu
Kaduna State Nigeria
Ku cigaba da bibiyarmu ta wannan shafin.