28/04/2026
Kwamitin Gawunan Kwankwaso Project karkashin jagorancin Shugaban Kwamitin, Hon. Muhammad Badaru Umar Ungogo, ya kai ziyarar ban girma ta musamman ga jigo cikin Jam'iyyar ADC amatakin jihar Kano, Sheikh Malam Ibrahim Khalil, a ofishin sa dake Cibiyar Majalisar Malamai ta jihar Kano dake Gyadi-Gyadi, Court road, Kano.
Ziyarar wadda ta gudana cikin yanayin girmamawa da k'arin fahimtar juna, inda aka tattauna muhimman batutuwa da s**a shafi cigaban al’umma da k'arin karfafa zumunci tare da jaddada buk'atar dad'in had'in kai domin cimma nasarori masu dorewa.
Ajawabin sa Malam Khalil ya bayyana irin zumunci da yadda aka taho tun abaya tsakanin sa da Dr. Nasiru Yusuf Gawuna cikin mu'amalar siyasa ta mutuntaka da girmamawa, inda daga k'arshe ya rufe taro da addu'ar fatan alkairi gami da fatan Allah Ya kawowa k'asar ingantaccen zaman lafiya da yalwar arzi'ki.
Abubakar Musa DK
Media Aide to H.E Dr. Nasiru Yusuf Gawuna.
Litinin 27/Afrilu/2026.