29/05/2026
Ina mamakin masu cewa an riga an gama zabe tun kafin ranar zabe, ko kuma babu wanda zai iya kayar da wani. Shin sun manta cewa Allah ne Mai bada mulki ga wanda Ya so, kuma Ya na karbe shi a lokacin da Ya ga dama ba tare da shawarar kowa ba?
Mulki amanar Allah ne, kuma ikonSa ne kadai yake tabbata a karshe. Allah Ka bamu shugabanni nagari masu gaskiya, adalci da tausayi ga al’umma. Ameen.