08/08/2023
Mai girma Justice Dije Abdu Aboki ta zama Alkaliyar Alkalai ta farko a jihar Kano
A Jiya Litinin 7 ga watan Augustar shekarar 2023 Mai girma zababben gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya rantsar da maigirma Justice Dije Aboki a matsayin Alkaliyar Alkalai Mai cikaken Iko. Wannan Nadi na Mai girma Dije Aboki shine irinsa na farko a tarihin jihar Kano Inda aka damka ragamar sashin sharia a karon farko a hannun mace. Muna Yiwa Maigirma Justice Dije Aboki Adduar Allah ya Taya ta riko.