05/11/2025
Mijina Yana ɓoye Baƙar Kyalle a Ƙasan pilon Kaina Duk Dare
Kashi na 1
Ban taɓa sanin cewa mijina yana ɓoye wani baƙar kyalle a ƙarƙashin matashin kaina ba duk lokacin da nake barci.
Mun shafe kusan mako guda kacal da aure. Na yi tsammanin zan rika barci lafiya a gefen mutumin da nake so, amma akasin haka, na kan farka da tsakar dare ba tare da wani dalili ba.
Wani lokaci ma, shi ma sai ya farka ya ce cikin sanyi,
“Sweetheart, me yasa baki barci ba?”
Sai in yi dariya in ce, “Ba komai, jiki ne kawai yana sabawa rayuwar aure.”
Ban san cewa mutumin da nake kira forever ɗina ba shi ne mutumin da na zata ba.
Wata rana da daddare, na farka ina jin wani rashin nutsuwa. Na tashi na tafi falonmu, na yi yawo a hankali sannan na dawo na kwanta. Da na gyara matashin kaina… sai na tsaya cak.
Na ga baƙar kyalle.
Tsoro ya shige ni. Na jawo shi a hankali, sai na tashi na tabo shi.
“Honey… honey,” na kira shi cikin rawar murya.
Ya motsa yana cewa, “Me ke faruwa?”
Na nuna masa. “Ka duba wannan! Ni da kaina na canja zanin gado da matashin kai, ban taɓa ganin wannan ba. Ta yaya ya shiga nan?”
Ya yi k**ar ya yi mamaki na ɗan lokaci… sannan ya yi murmushi a hankali.
“Ah, zo mana darling. Wataƙila ya zame daga matashin kai ne. Me yasa k**e tsoro haka?” Ya yi dariya ƙanana sannan ya ɗauke shi.
Na sauke ajiyar zuciya. Ya riƙe hannuna cikin natsuwa yana cewa,
“Ki daina damuwa. Ki kwanta ki huta.”
Na amince, amma zuciyata ta kasa samun nutsuwa. Wataƙila da gaske ne… wataƙila ya fito ne daga matashin kaina.
Sai dai wasu darare, ina jin k**ar ana motsa matashin kaina — k**ar ana saka wani abu a ƙasa. Amma ban taɓa yin tunanin bincika ba.
Sai da wani safiya ya ce min yana da tafiya ta gaggawa ta kasuwanci, zai dawo cikin kwana biyu.
Na karɓa cikin natsuwa, ko da yake na san zan yi kewarsa.
A daren nan muka yi magana a waya na dogon lokaci. Muka yi dariya, muka yi wasa, sannan kafin in rufe idona na ce cikin sanyi,
“Goodnight. Ina kewarka.”
Ya amsa cikin murya mai laushi,
“Kar ki