02/10/2025
Sakon fatan Alheri wanda kakaki majalisan dokokin
Karamar hukumar zaria yayí ranan murnan Nigeria ta cika
Shekaru sitin da biyar (65) da samun yan'cin kai
Maigirma kakakin majalisan dokokin karamar hukumar zaria Honourable Auwal balarabe Yana Taya jama'ar karamar hukumar zaria murnan zagayon Nigeria ta cika shekaru sitin da samun yan'cin kai, kakakin majalisan dokokin karamar hukumar zaria ya Mika sakon fatan Alheri ne yayin da yake hira da yan'jaridu a opishin shi a zaria.
Mal Auwal balarabe yayí tulawan nasarori da gwabnatoci das**a shude s**a samun biyo bayan samun yan'cin kai Nigeria musamman bangaren ilimin , Aikin gona , Samar da lafiya , Sadarwa , tattalin Arzuki , Samar da Aikin Yi , Gina hanyoyi da bunkasa masana'antu .
Saboda haka shugaban majalisan dokokin karamar hukumar zaria hon Auwal balarabe ya roki al ummar karamar hukumar zaria dasu cigaba daba da goyan baya ga gwabnati musamman shugabanci shugaban karamar hukumar zaria honourable Injiniya Jamil Ahmad Jamil (jaga)
Domin bunkasa karamar hukumar zaria musamman bangaren dokoki wanda zasu kawo cigaba a karamar hukumar zaria.
Akarshe maigirma shugaban majalisan dokokin Alh Auwal balarabe yayí Amfani da wanan Daman taya maigirma Gwabnan jihar Kaduna Santa uba sani da maimartaba sarkin zazzau Ambasada Ahmad Nuhu bamali da yan'majalisun dokoki jihar Kaduna da kakakin majalisan tarayya iyan zazzau Dr Abbas Tajuddeen da shugaban kasa Mal bola tunubu da SAURAN dukan shuwagabani kasa murnan zagayowan ranan yan'cin kai Allah taimaki zaria local government yataimaki jihar Kaduna da kasa Baki Daya .
Musa Ibrahim
Public Relations Officer
Zaria legislative council