Dan Iyan Dallatun Zazzau

Dan Iyan Dallatun Zazzau Alhamdulillah Ala Kulli Halin

Gaskiya da riƙon Amana, su ke samar da Shugaba da Wakili nagari.Al'ummar ZONE ONE - ga naku Alh Dr Mukhtar Ramalan Yero ...
21/08/2026

Gaskiya da riƙon Amana, su ke samar da Shugaba da Wakili nagari.

Al'ummar ZONE ONE - ga naku Alh Dr Mukhtar Ramalan Yero (Dallatun Zazzau), A matsayin ɗan takaran kujeran Sanata.

Ku zaɓi mutumin kirki a yau, ku samu wakilci nagari a gobe. DALLATU Alkhairi ne 😊

Sanatan ZONE ONE mai jiran gado da yardan Allah.
17/08/2026

Sanatan ZONE ONE mai jiran gado da yardan Allah.

Aikin Media bai tsaya a iya tallata ɗan Takara ba, hatta al'umma sunada haƙƙi akan ɗan Media wajen tabbatar da ya kawo m...
16/08/2026

Aikin Media bai tsaya a iya tallata ɗan Takara ba, hatta al'umma sunada haƙƙi akan ɗan Media wajen tabbatar da ya kawo masu tallar ɗan takara nagari.

Idan ɗan Media ya yaudari al'umma s**a zaɓi ɗan takaran daya tallata masu, alhalin yasan ɗan takaran ba nagari bane, to duk halin da al'umma s**a tsinci kansu mara daɗi a ƙarƙashin shugabanci ko wakilcin ɗan takaran bayan yaci zaɓe, ɗan Media yanada kaso mai tsoka na nauyi da zaiyi wa Allah bayani a ranar sak**ako. Wannan yasa muke ƙoƙarin wayar da kan al'ummar ZONE ONE, su fahimci alkhairin da muke tallata masu.

DALLATU - ɗan takara ne nagari, mutumin kirki mai son cigaban al'ummar sa. Munada tabbacin Dallatu zai kafa tarihi na zama best Senator a Zone One.

Al'ummar ZONE ONE, ku ba Dallatu dama ya zama waliki a gareku a majalisar dattawa, Dallatu zai zama waliki nagari a gareku, ba shakku akan haka.

Dallatu Alkhairi ne 😊

Ina taya al'ummar ZONE ONE murnar samun Sanata mai kishin su da son cigaban su, Alh Dr Mukhtar Ramalan Yero (Dallatun Za...
15/08/2026

Ina taya al'ummar ZONE ONE murnar samun Sanata mai kishin su da son cigaban su, Alh Dr Mukhtar Ramalan Yero (Dallatun Zazzau). Mutum mai haƙuri ga son Jama'a. Ƴan Siyasa masu tsoran Allah irin Dallatu basuda yawa, shiyasa wasu ke ganin bai k**ata Dallatu ya zama ɗan Siyasa ba, sunfi ganin ɓangaran wa'azi yafi dacewa dashi. To amma Siyasa musamman irin na ƙasar nan, muna buƙatan mutanan kirki irin Dallatu, kamili mai amana.

Daga cikin ƙyawawan ɗabi'un Dallatu wanda ya sha banban da sauran ƴan Siyasa, DALLATU ba ya alƙawarin bogi, idan yace zaiyi, to zaiyi. Dallatu ba ya ƙarya dan ya burge ko a yabeshi, bai yarda da wani yaci mutuncin wani akan sa ba. Dallatu kenan.

Babu shakka al'ummar ZONE ONE zasuyi farin ciki mara misaltuwa da samun Dallatu a matsayin wakili a garesu. Tabbas zasuyi dacen SANATA.

Eh, Sanata mai jiran gado da yardan Allah.

Dallatu Alkhairi ne, ku zaɓi Jam'iyar APC Sak.

Kanason cigaban yankin ka Zone One ko ƙiyayya ce a zuciyar ka? Idan kana son cigaban yankin ka, to kazo mu haɗu mu nemaw...
13/08/2026

Kanason cigaban yankin ka Zone One ko ƙiyayya ce a zuciyar ka? Idan kana son cigaban yankin ka, to kazo mu haɗu mu nemawa yankin naka mafita, ta hanyar kira ga al'ummar ka su zaɓi Alh Dr Mukhtar Ramalan Yero (Dallatun Zazzau) a matsayin Sanata.

Ba sai nayi maka dogon bayani ba, ka san waye Dallatu, kasan cewa yanada kwarewar da zai samar da abubuwan cigaba ga al'ummar yankin ka.

Zaɓan mutumin kirki a yau, makoma mai ƙyau a gobe. DALLATU ne mafitar Zone One a zaɓen 2027.

Mutumin kirki, Nagartacce, mai faran zuciya Alh Dr Mukhtar Ramalan Yero (Dallatun Zazzau).Wato duk bayanin da za'ayi mak...
12/08/2026

Mutumin kirki, Nagartacce, mai faran zuciya Alh Dr Mukhtar Ramalan Yero (Dallatun Zazzau).

Wato duk bayanin da za'ayi maka gameda ƙyawawan halayen Dallatu, sai ka kusanceshi za ka san waye shi. Kaɗan daga cikin ƙyawawan halayen Dallatu mutum ne mai haƙuri da son jama'a, ba ya munafurci, duk zancen da za ka kai masa indai ba gaskiya bane, to sai kaji kunya. Dallatu kenan.

Mutane s**an ce "EL Khaleel maigidan ku bai k**ata yayi Siyasa ba, halin shi ba na ƴan Siyasa bane, shi duk abinda zaiyi ba ya manta Allah".

Shiyasa yake da ƙyaƙƙyawar alaƙa da ɗaukacin ƙungiyoyin Addinai, suna respecting ɗinsa.

Indai nagartan ɗan takara al'ummar Zone One za su duba a zaɓen 2027, to Dallatu yaci zaɓe. Saboda shi kansa Sanata na yanzu Barrister Ibrahim Khalid Soba yasan indai maganar nagarta akeyi, Dallatu ya fishi nagarta ta kowani fuska, Dallatu ya fishi son al'umma, Dallatu ya fishi kishin al'umma, Dallatu ya fishi farin jini da karɓuwa wajen al'umma.

DALLATU fa, ya riga ya zama Sanatan ZONE ONE, lokaci kawai muke jira, da yardan Allah.

Kowa na iya neman shugabanci amma ba kowa ke iya zama waliki ko shugaba nagari ga al'umma ba.Zaɓan mutumin kirki, shi ke...
11/08/2026

Kowa na iya neman shugabanci amma ba kowa ke iya zama waliki ko shugaba nagari ga al'umma ba.

Zaɓan mutumin kirki, shi ke samar da shugabanci nagari ga al'umma, bisa gaskiya da riƙon amana.

Al'ummar shiyya ta ɗayan jihar kaduna (Zone One) ku zaɓi Dallatun Zazzau a matsayin Sanata a zaɓen 2027 mai ƙaratowa, domin samun wakilci nagari.

Zaɓi nagari a yau, domin makoma mai ƙyau a gobe.

Me k**ar zuwa ake aika - DALLATU dattijon ƙwarai.Wato shi bawan Allah nan, ko maƙiyan sa sun yarda dattijon ƙwarai ne, m...
10/08/2026

Me k**ar zuwa ake aika - DALLATU dattijon ƙwarai.

Wato shi bawan Allah nan, ko maƙiyan sa sun yarda dattijon ƙwarai ne, mutumin kirki mai son jama'a.

Shi kaɗai ne ɗan Siyasa a jihar kaduna da maƙiyan sa suke kusheshi suke yabon sa a lokaci guda, da za a tambayesu dalilin kushewar, su kansu basu san dalili ba. Ƙiyayya ce kawai mara dalili.

Dallatu, Al'janna mai masoya da yawa, Amanar Balaraben Gwamna Dr Malam Uba Sani CON.

Dallatu Sanatan Zone One mai jiran gado da yardan Allah. Lokaci kawai muje jira.

Ko a fuska Dallatu baiyi k**a da maciya amana ba, waɗanda su kansu sunsan su maciya mana ne.

Al'ummar ZONE ONE, ku zaɓi Jam'iyar APC Sak ✍🏻

ZONE ONE 2027 | Ina taya al'ummar shiyya ta ɗayan jihar kaduna murnar samun ɗan takaran Sanata mai haƙuri da son cigaban...
09/08/2026

ZONE ONE 2027 | Ina taya al'ummar shiyya ta ɗayan jihar kaduna murnar samun ɗan takaran Sanata mai haƙuri da son cigaban yankin, Alh Dr Mukhtar Ramalan Yero (Dallatun Zazzau). Abin alfahari ne Dallatu ya zama wakili a gareku. A matsayin sa na ɗan Adam zai iya aikata kuskure yayin gudanar da wakilcin amma inada tabbacin ba za ku sameshi da cin amana ba, Dallatu mutum ne mai gaskiya mai gudun abin kunya. Shiyasa har El-Rufai ya gama shekaru takwas a matsayin Gwmana bai samu Dallatu da laifin cin amanar al'ummar jihar kaduna ba. Wannan abin alfahari ne, abin a yaba masa ne.

Ina tabbatar maku, A ƙarƙashin wakilcin Dallatu, Zone One za ta samu cigaba na ban mamaki, ba na shakka akan haka, saboda na san manufar Dallatu.

Saboda haka, ina kira gareku, kada ku bari mayaudara su yaudareku, kada ku sake jefa ƙuru'un ku a inda ba zai amfanar daku ba. Na sani, Sanatan ku mai ci Barr Ibrahim Khalid Soba bai ƙyauta maku ba, bai tsinana maku komai ba, yaci amanar ku. Saboda haka, kada ku bashi dama ya maimaita. Ku ba Dallatu dama zai iya, ya shirya tsaf domin samar da ingantaccen wakilci wanda kowa zai amfana.

Ku zaɓi Dallatun Zazzau, ku zaɓi Jam'iyar APC Sak.

Zaɓen Shugaban Ƙasa da na ƴan majalisar tarayya za'a fara kamfen; Talata, 19 ga Agusta, 2026.Tawagar ɗan takaran kujeran...
08/08/2026

Zaɓen Shugaban Ƙasa da na ƴan majalisar tarayya za'a fara kamfen; Talata, 19 ga Agusta, 2026.

Tawagar ɗan takaran kujeran Sanatan ZONE ONE Alh Dr Mukhtar Ramalan Yero (Dallatun Zazzau) mun shiryar tsaf domin shiga lungu da saƙo domin neman alfarmar al'umma su zaɓi Jam'iyar APC Sak.

Dallatu yanada ƙyawawan manufofi masu ƙunshe da abubuwan cigaban al'ummar wannan yanki.

Duk ɗan wannan yanki indai mai son cigaban yankin ne, zai bada tabbacin Sanatan dake kan kujeran Barrister Khalid Soba yayi failed, babu abin nunawa na cigaban al'umma da ya kawo a skekaru uku da watanni da yayi akan kujeran. Saboda haka bai chanchanta ya koma ba. A zaɓi Dallatun Zazzau ya kawo chanji nagari, wanda kowa zai amfana.

DALLATU Alkhairi ne, ku zaɓi Jam'iyar APC Sak ✍🏻

Address

Kaduna

Telephone

+18038436452

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dan Iyan Dallatun Zazzau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Dan Iyan Dallatun Zazzau:

Shortcuts

Share

Category