15/10/2023
ZAHIRIN RAYUWAR WADANDA BA SU JE JAMI'A BA
Sanarwa: Asalin rubutun nan ba ni na yi ba. Fassarawa kawai na yi don amfanin jama'armu. Kuma na dan yi canje-canje a ciki don ma'anar ta fito wa Bahaushe tarwai. A turakar Yayana Malam Aliyu Nuhu na ga rubutun. Shi ma kuma ya ce ya kwafo ne.
Ga abin da aka ce:
Ka dauki naira dubu 50, ka ba matashin da ya kasa kammala sakandare, za ka ga ya sayi risho da kayan tuya yana soya indomie yana sayar wa mutane, ko ka ga ya fara sayen gwanjo yana sayarwa, ko ka ga yana sayar da takalma 'yan Kwatano. Wani ikon Allah, a cikin shekaru uku zuwa biyar da fara bizines dinsa, za ka ga matashin nan ya yi aure abinsa. Ya sayi dan mashin dinsa Jinchen, har ma ya kai ga sayen fili don fara gini. Rayuwarsa ta dauki saiti.
Amma ka dauki naira miliyan daya, ka ba matashin da ya kammala jami'a, za ka ga ya sayi waya qirar IPhone 11 Pro Max ko Samsung Galaxy S20. Kuma ya sayi wandunan jeans damammu da 'designer shirts.' Sannan za ka ga yana daukar budurwarsa suna zuwa cin burger ko shawarma suna daukar selfies har kudin su qare. Bayan sun qare, za ka ga ya koma wurin mai indomie din can da bai gama sakandare ba yana cin bashin na dare ko bashin kudin fita da sunan jiran aikin ofis.
Abin tambayar a nan shi ne, shin ilimin boko yana qyanqyasar mutakabbiran marasa lissafi ne?
Kalla! Sam ilimin boko ba ya yin haka. Amma in har matashi bai kula ba, to rayuwar ilimin tana sa mutum ya riqa yi wa abin da qila shi ne dalilin arziqinsa gani-gani. Da haka sai ya tsallake damarsa saboda hangen dala. Wannan kuma na daga cikin dalilan da ke sa ake yawan samun marasa aikin yi cikin masu ilimi. Kafin ka ce me, sai wancan da bai ma kammala sakandare ba, ya yi bunqasar da zai zo ya dauki wanda ya kammala jami'a aiki, yana biyansa albashi a kowane wata.