10/03/2025
Ɗan takarar shugaban ƙasa a SDP ya yi maraba da El-Rufai zuwa jam'iyyar
Tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasa a Jam’iyyar Social Democratic Party, SDP, a zaɓen 2023, Adewole Adebayo, ya bayyana shigowar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai zuwa jam’iyyar a matsayin abin farin ciki, yana mai cewa lokaci yayi na siyasa mai kyau.
Adebayo, yayin da ya ke tsokaci kan ficewar El-Rufai daga jam’iyyar APC, a shafinsa na X, ya bayyana tsohon gwamnan a matsayin ‘mutum mai himma da hazaƙa.
“A madadin jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyar SDP da masu kishin kasa wadanda s**a yi imani da Nijeriya da kuma alkawarin da ta yi na cigaba ba makawa, ina maraba da dan uwana, El-Rufa’i sosai zuwa jam’iyyarmu.
“Tare da Malam, dan gwagwarmaya kuma haziki ya shiga sahunmu, an saka wani ma’aikaci mai himma ga jama’a a cikin rundunar mu don yakar talauci da rashin tsaro.
“Yanzu ne lokacin da ya kamata mu sanya kafadun mu a bayan sa don kokarin cika sashe na 2 na kundin tsarin mulki da kuma ceto ‘yan Najeriya daga mummunan shugabanci da rashin ci gaba,” inji shi.