02/08/2026
Yaron shago a yau zai iya zama attajirin gobe… amma ba saboda ya daɗe a shago ba. Saboda ya san abin da yake ginawa yayin da yake ciki.
Na ga mutane da yawa sun yi shekaru a shaguna amma ba su gina komai ba. Na kuma ga waɗanda s**a fara da zama yara a shago, daga baya s**a zama masu shaguna da gidaje da kamfanoni.
Abin da ya bambanta su ba sallamar shago ba ne, tunani ne.
Idan ka riƙi waɗannan shawarwari da zan ba ka a matsayinka na yaran shago, za ka ga gagarumin sauyi a rayuwarka gabaɗaya.
1. Ka koyi kasuwanci, ba aikin shago kaɗai ba.
Kada ka tsaya iya sayar da kaya. Ka fahimci yadda ake saye da yadda ake samun riba da yadda ake jan kwastomomi, da yadda ake tafiyar da kasuwanci.
2. Ka tattali da tara kuɗi tun yanzu.
Ba sai ka zama mai kuɗi ba kafin ka fara ajiya. Ɗan abin da ka fara ajiyewa yau na iya zama babban jari gobe.
3. Ka kasance mai gaskiya ko da babu mai kula da kai.
Amana ita ce jari mafi girma da yaron shago zai iya mallaka.
4. Ka ɗauki shagon kamar naka ne.
Wanda ya iya kula da na wani, shi ne ya cancanci Allah Ya ba shi nasa.
5. Ka yi tunanin inda kake son kasancewa bayan shekara goma.
Mutumin da ba shi da manufa, sau da yawa yana rayuwa ne bisa yadda rana ta fito da ƙarar da rayuwarsa wajen gina manufar wani.
6. Ka yi amfani da lokacin da babu ciniki wajen karatu da nazari, da koyon sababbin dabaru, sun fi ka zauna hira da gulma mara amfani.
7. Ka kula da sunanka.
A kasuwa, suna mai kyau yana iya kawo maka damar da kuɗi ba za su kawo ba.
8. Ka girmama mai gidanka.
Ko da kana da ra’ayi daban da nasa, ka tuna cewa kana iya koyon wani abu daga gare shi.
9. Ka guji gulma da yawan surutu.
Lokacin da wasu suke ɓata lokaci, kai ka yi anfani da naka.
10. Ka koyi haƙuri.
Ba kowace nasara ce ake gani cikin dare ɗaya ba.
11. Ka nemi ilmi koyaushe.
Kasuwanci yana son masu tunani fiye da masu ƙarfin jiki kawai.
12. Ka gina kyakkyawar alaƙa da mutane.
Mutunci da kyakkyawar mu’amala suna buɗe ƙofofi masu yawa.
13. Ka nisanci hassada.
Ka mai da han